Part 6

254 7 0
                                    

*💫❤LOVE CYCLE✨*

Written by

*@nnafie🖤*
(Smll but mighty😉)

*writer of*
Saif
Adaan
Wada mafita
Saboda duniya
Love cycle......

Bismillahir rahmanir raheem

💫❤Love cycle❤ (6)✨
Monday.......
Gama shiri tayi kamar kullum snn ta fito tayi breakfast tayi wa mummy sallama snn ta wuce sch... Duk da ynx suna shiri dashi seda taji fargaban da tasaba ji a duk lokacin da suke sukeda class dinsa... Dan murmushi tayi tana tuna moments dinsu na jiya.. Ta girgiza kai kamar ba su bane suke fada kullum... Koda ta shiga be zo ba dan haka ta samu seat ta zauna cike da kewar maryam...
Kamshin turaren sa ne ya cika mata hanci hakan ne yasa ta tabbatar da yazo kanta kasa ta kasa daga kai... Dr Amah ya shigo as handsome than ever dayawan yan class din suna crushing dinsa sbd komai nasa na daban ne..... Yawo ya farayi da idanun sa har ya sauke a kanta.... Kuma be dauke ba mutane da yawa sunsha cewa zeyi ta koma position din da ya bata.... Fannah duk da kanta na kasa seda ta tsargu..... Dan ji take kamar kallon ta yake gashi class din yy shiru... A hankali ta dago idanun ta ta zubasu cikin nasa...... Gaban tane yayi wani irin faduwa.. Tunanin ta cewa zeyi ta tashi... Ganin yaki dauke ido a kanta ne yasa.. Ta mike jiki a sanyaye...
Gira daya ya dage yace "where are you going".... Da burbucewa tayi tama kasa magana... Dauke idon sa yy a kanta yana kallon sauran yan class din yace mata "sit down".. Dama kamar abinda take jira knn ta zauna tana sauke ajiyar zuciya....
Cikin natsuwa da kwarewa ya cigaba da abinda ya kawosa yana gamawa ya fice suma duk suka fice.... Fannah nada wani class din in the next 2hrs dan haka direct inda suke haduwa da Aliyu can ta nufa bawai dan tana tunanin ze zoba se don ta huta...
Zaunawa tayi tana lumshe idanu cike da gajiya yunwa da kuma kewar maryam dan murmushi tayi da ta tuna cewa gobe zata dawo.... Kiran waitress din wajen tayi... Ordering din abinda zataci tayi.. Snn ta lumshe idanunta tana jira.. ...
Bude idanun ta tayi ganin waitress din tana jera abincin a gaban.... Fannah ta danyi murmushi kafin tace "sister you're mistaken this not what I ordered"... Waitress din tace "yes ma but that guy ask us to change and he paid the bills" ta fada tana nuna mata Aliyu dake wata resting chair... Dauke kai fannah tayi bayan sun hada ido da Aliyu ba tare da tace komai ba... Waitress din ma ta wuce.. Fannah ta hade fuskar ta duk da kuwa tayi farin cikin ganin sa .... Kamshin turaren sa da ya cika mata hanci ne ya tabbatar mata da ya karaso kusa da ita.. Amma taki dagowa.. Kanta kasa se kallon Abincin da aka kawo mata take na mutum biyu.. Nigerian dishes ne kamshin su duk ya cika mata hanci sbd tsabar yunwar da takeji se kace wacce batayi break ba... Tanaji ya zauna a kujerar dake opposite da kujerar ta amma bata dago ba...
Murmushi yy yana kallon ta kafin ya dauki spoon.. Maimakon yaci na gaban sa se yaci nagaban ta .. Da sauri ta dago tana kallon sa.. Ya dage gira yana tauna Abincin bakinsa seda ya hadiye snn yace. "Kallon fa?".. Dauke kai tayi ... Muryar sa ta kara ji yace "fushin fa"... Ba tare da ta kalle sa ba ta fara cin abincin.... Dan tagowa tayi suka hada ido... Marairacewa tayi yace "wai me nayi ne".. Hararar sa tayi tana dauke kai yace "alright bari na kara ci tunda bazakiyi magana ba"..... Da sauri ta janye tace "baxakaci ba wanda kaci ma ya isheka".... dariya yayi har ta dago tana kallon sa yace "to srry" tace "kuma bayan abinda kamun a class" ya ware manyan idanun sa "me kuma nayi"... Duk ba kaine ka rudani ba I thought you will say I should go back to my position da kabani da karfi da yaji".... Murmushi yy yace "na isa salan mu koma gidan jiya ki dena kulani bacin na riga na saba dake".... Tace "ai da maryam ta dawo gobe na dena kulaka"... Ya gyara zamansa yace "you must be joking babee".. Dan kallonsa tayi jin yace mata babee tace watch and see".. Dage kafada tayi...yace "tell me about you I mean ur family tunda ynx mu yan kasa daya ne" haka kawai ta tsinci kanta da basa lvrn ta da family dinta.... Haka ta basa lvr jiki a sanyaye lvrn da ko maryam bata taba ba.... Jin jina kai Aliyu yayi kafin yace "but at list you have to do something just see ur family back" kallon sa tayi tace "lyk how I don't even knw where to start"... Murmushin sa me kyau yayi yace "just think" shiru tayi tana kallon sa... Yace "kiyi tunani kamar nan da sati in kina bukatar taimako na zan taimaka maki" gyada masa kai tayi... Dan lvr sukayi daga nan suka tashi ta koma class..
Da Suka tashi shiya raka ta har mota daga nan sukayi sallama ta koma gida... Koda ta ta koma gida tana ta tunanin ta ina zata fara ranar har mummy seda ta tambaye ta lpy se tace ba komai ....
Da sukayi waya da maryam se cewa tayi wai bazata dawo gobe ba wai se Wednesday babu flight daga Abuja... Haushi kamar ya kashe fannah haka ma de ta kashe wayar maryam din nata kiran ta amma taki dauka dan har kaga Allah taji haushi jin maryam take har cikin ranta kamar me.....
Washe gari koda taje sch suna tare Da Aliyu idan kaga yanda suka sake da juna baka taba cewa da sune suke fada sosai ya biye mata gurbin maryam haka ma ranar Wednesday suna tare... Suna ta lvr yana tsokanar ta kamar yanda ya saba.. Hararansa tayi tace "yau de maryam zata dawo ko kulaka bazan karayi ba" ya dage kafada yace "nima na dena kulaki masu kawa nan gaba nasan se kinfi sona akan wnn kawar taki" zaro idanu tayi tace "tab to semi mugani" dauke kai yy yana wani murmushi itama batace komai ba dan takula shi miskilin mutum ne da kuma basar da abu ta kula da ita ne kawai yake sakewa .. Mikewa tayi tace "bari kaga zanje gidan maryam naga ko an gyara snn nadan dafa mata abinda zataci... Nasan ta taso... "Ya ware idanu yace inzo muje" make kafada tayi tace "bana gayyata".... Yana murmushi yace "zakiyi bayani.... Shiya rakata har mota yace "se gobe ko" ta noke kafada tace "baka kara ganina" murmushi yy batare da yace komai ba yana kallo har ta fice..... Wayar sa ce tayi ringing dubawa yy.. YUSRAH yaga yana yawo a screen din wayar tasa... Motar sa ya shiga ba tare da rufe ba yy picking wayar amma bece komai ba.... Tace "yaya"dan numfashi ya sauke kafin yace "yap" daga can tace "inafa America ance mun kana UK shine ka tafi bayan nace maka zanzo"... Dan lumshe idanun sa yy yace "yeah ai ba damuwa gasu mammah nan saleem da kuma sumayya suma duk yan uwanki ne ai".... "Ai ba dansu nazo ba dan haka I think next flight zan sauka a London din"... "Yusrah" ya kirata dan tsawa ce.....cikin rawar murya tace "srry yaya" yace "baki da hankali ne to idan kinzo nan wajen wa" "zan sauka gidan gidan aunty salmer "... Tabe baki yy yace "to karki sake ko wasa mu hadu you get me".. Cikin rawar murya tace "ka yi hakuri zan koma Nigeria"... Batare da ya ce komai ba ya katse wayar sa.. Yana tafe kai kafin yace " YUSRAH, JIDDA"... dan tsaki yy kafin ya tada motar yabar wajen
..
Maryam na sakkowa ta hango Fannah da take ta raba idanu tanason ganin ta ina maryam zata fito.. Maryam tace "oh god I love that soul ka nuna mun tsufan ta".... Ba tare da ta yarda Fannah ta ganta ba ta lallaba... Fannah ji tayi an rungume ta baya ana ihu... Koba'a fada mata ba tasan kawar ta ce .. Ture ta tayi tana hararanta tace "ni kyaleni na dena kulaki" dariya maryam tayi tace "srry swthrt wlh bani da niyar kara kwana ba laifi na bane"... Hararar ta Fannah tayi cike da kewar ta kafin ta rungume ta... Maryam ta kwalo idanu "ke karki karyani fa" dungure ta Fannah tayi tana dariya mota suka shiga suna ta shirme har suka karasa gidan su Fannah... Maryam ta rungume mummy dake parlor... Mummy tace "umm ynx de zamu huta da wnn cin kunun da ake mana kwana biyu sbd kin tafi.." Fannah na tura baki tace "kai mummy kar kija ta rainani ta daukana wani damu da ita" gwalo maryam tayi mata tace zama ki fadi gsky babee"... Fannah ta murguda baki...
Anan maryam taci abincin ci .. Suka zauna suna lvr.. Maryam ta ciro masu tsarabar su se murna suke dan duk wani abu na kasar tasu sonsa suke....
Ranar tare suka kwana da maryam sun dade suna lvr kafin sun kwanta... Bada wuri suke da lectures ba dan haka seda suka koma baccin safe... Kafin su tashi su shirya bayan sunyi break su ka wuce sch....
Bayan anyi lectures suka tafi inda suka saba zama koda wasa Fannah batawa maryam maganar Amah ba ... Chocolate suke sha suna ta shirmen su da suka saba... Suka saba kamar ance Fannah ta daga ido suka hada idanu dashi... Duk da dama tunanin sa take seda tayi mmkin ganin sa.... Wara idanu tayi ganin ya taso toward them.. Maryam da taga Fannah bata tare da ita ta juyo ga inda take kallo... Zaro idanu tayi tace "what Amah"... Dauke kai Fannah tayi batare da tace komai ba... Itama maryam sauke kanta tayi gaban ta na faduwa tana tunanin bade gurin su zezo ba ko .... Tunanin ta ya katse jin ya masu sallam tare da jan kujera ya zauna... Da sauri maryam ta gaisar da shi... Amsawa yy yana mata Murmushin bata taba gani a fuskar sa ba.. Snn yace "sbd kin dawo har ta manta dani... " cike da confusion da tsananin mamkin ina ya iya hausa tace "w.. Ww. Wa.. Kuma.." Ya nuna Fannah data wani tura baki... Maryam kallon Fannah tayi cike da mmki... Amah yace "to na nemo ki" marairaicewa Fannah tayi tace "ni wai me nayi" gyara zama maryam tayi tana kallon su da kyau cike da mmki wnn lamari... "Kallon wrist watch dinsa yy yace "zakiyi bayani bani da tym ynx am traveling" kamar tace ina zeje se kuma tayi shiru ganin irin kallon da maryam ke masu tace "self journey".. Murmushi yy kafin yace "bye" snn ya kalli maryam da ta saki baki yace "bye kawar mu" gyada kai kawai tayi batace komai ba tsabar mmkin daya narkar da ita....
Wucewa yy ya barsu.. Kamar jira maryam take yatafi tace "ke bn gane ba yaushe kuka fara shiri.. Wait dama wai bahaushe ne ina ya iya hausa"....
Duk ni kade wnn tambayar he's a Nigerian shiyasa muka fara shiri tunda kika tafi kullum se mun hadu he is nice ba kamar yanda na dauka da farko ba"..... Murmushi kawai maryam keyi tana girgiza kai kafin tace "geng geng geng wasan ya fara canzawa let's see how it wil end"... Jifar ta fannah tayi da choculate tace "munafika babu abinda zaki gani"... Duk yanda maryam taso taji wani abu Fannah ta barsar dole ta hakura ta barta....
Washe gari Fannah ta nunawa maryam inda suke zama aikam taje ta zauna wai daga ranar nan zasu rika hutawa... Fannah de bata ce komai ba... Cikin ranta tana tunanin ko ina Amah ya tafi... A haka de har suka gama zaman su be zo ba hakan kau ya damu fannah haka de ta daure har suka karasa gidan maryam daga nan ta wuce...
Duk fannah setaji ta damu da ina ya tafi sbd tunda maryam ta tafi kullum se sun hadu dashi kodayaushe suna tare.. To kode ya kyaleta ne sbd tace idan maryam ta dawo babu ruwansa da ita.... Ji tayi duk ba dadi... Tashi ta zaune tana dafe goshi "kai waini ina ruwana da shi ne".tura baki tayi kafin ta tashi ta shige toilet...... A hakade tayi baccin ranar da tunani tana kuma kokarin kawar dashi ....
Wajen karfe 10 ta tashi tayi wanka ta shirya kamar kullum snn ta fita for breakfast.. Kamar yanda tayi tunani kowa nanan sbd yau Saturday weekend ne kusa da Hisam ta zauna tana dan dungurinsa tace "Acici"... Mummy ta harare ta tace "daga fitowarki zaki koma inda kk fito".. Tura baki tayi tace "daddy good morning".... Yana murmushi ya amsa mata ta gaisar da mummy itama ta amsa mata yayinda hisam ya gaisar da ita ... Bayan sun gama Hisam yace "Aunty yaufa akwai kallo".... Gyada masa kai tayi tace "we're going with maryam too"... Hisam yace "what of that bro" harara sa tayi kawai.. Yayinda mummy ta bita da idanu.....
.....
Da yamma ta shirya cikin simple shigarta dake fito da asalin kyanta maryam tazo dan haka suka fice tare cike da nishadi hisam nabawa maryam lvrn last episode da suka kalla..... Fannah taxo zata gyara parking wata mota tayi blocking dinta.. Se ta danyi horn amma be matsa ba... Dama kaga yanda yy parking din kasan da gangan yy.... Dan tsaki Fannah tayi.. Tace "kinga maryam rabu da wnn kuzo mu wuce nasan dole securities zasu masa magana ya gyara"... Fitowa sukayi Gabadaya maryam rike da hannun Hisam suna zuwa saitin motar yayi daidai da bude dayar motar wanda ke ciki ya fito.....
Da sauri Hisam yaje ya rungume sa yana fadin "brother"... Kallonsa fannah ta rinka yi da mmki dan batayi tsammanin ganin sa ita duk tunanin ta yadena kulatan ne kamar yanda ya fada... Setaga yau ya kara mata wani kyau yy wani fresh ga cool kamshinsa duk ya cika wajen.. Duk da da kagansa kaga jarumin namiji kallo daya zaka masa kasa irin sangartattun yaran nan ne yan gata snn hutu da natsuwa sun bayyana a tare dashi.... Hannu yasa yayi kamar ze tsokane mata idanu... Da sauri ta kipta tana tura baki... Daga nan tayi gaba tana murmushi dan har ga Allah taji kunya da yakamata tana kallon sa.... Shima wuce ta yy rike da hannun Hisam ba tare da yace da ita komai ba.... maryam ta karaso kusa da ita.. Cikin rada tace "he's cute".... Fannah ta tabe baki tace "to ni bn gani ba".. "Shiyasa naga kin shagala da kallon sa ai" tsuke fuska fannah tayi "me zan kalla a can" ta fada tana hararar bayan Amah dake tsaye yana siya masu ticket... Maryam ta ware hannuwa tana dariya ciki ciki....mikawa kowa ticket din yayi.. Amma yaki bawa fannah kamar zatayi kuka tace nima... Maryam ta kama hannun hisam suka wuce... Ya nuna mata yace gashi nan... Zata karba ya noke... Kumbura fuska tayi tace nama fasa kallon.. Ta juya.... Yana murmushi yabi bayanta... Tana ganin ya biyo ta ta kara sauri har ta shige mota ... Bude front seat yy ya shiga... Tsuke fuska tayi "why are you following".. "Coz you need me by ur side" ta hararesa... "Dalili" kai tsaye yace "you miss me".. Waro idanu tayi tace "nidin"... Yana kishingida yace "malama just tell me do you missed me"... Kai tsaye tace "no".. Yadan lumshe idanu yace "ohk let me go but I missed you jiya kade da bn ganki ba.. But tunda baki so I don't have to nima".. Bude kofar yy ze fita... Da sauri tace "wait I was joking I..missed ...you.....too" ta fada kamar tana counting words... Yanda tayi kade ya nuna maganar subuce mata tayi... Juyowa yy ya zuba mata idanun sa... Tayi sauri dauke kai tana tura baki... Murmushin gefen baki yayi yace "really" ta girgiza kai "am not sure"... yana shigewa cikin kujerar yace "zakiyi bayani"... Tace "anfa fara film din" yace "bakin fasa kallo ba" "nifa wasa nake lets go pls".. Budewa yy suka fita seda ya siya masu kayan ciye ciye snn suka shiga.... Tuni fannah ta ware sunata tsonar juna.. Bakaramin burge maryam sukayi ba dan tunda suke fannah bata taba gani ta sake da wani namiji ba se shi....
Wnn karkon ma seda suka je wajen wasan ni dukkansu suka sake suna ta wasan su... Suka gama kowa ya kama gaban sa....
Tundaga wnn rana Amah da fannah suka sake shakuwa kullum se sun hadu idan kacire sunday tun yan course dinsu fannah basu fahimci sun shirya ba har suka fahimta.. Wasu ma suka fara dauka soyayya suke dan koda yaushe suna tare sunba mutane da yawa mmki sbd da yar tsama suke... Duk wani abu da ya shige masu duhu ita da maryam a wajen karatu yana koya masu kuma suna fahimta... Dayawan mata na kasashe daban daban da suka san amah suna kishi da fannah dan Amah mutum ne wanda bazaka kalla ka yar ba sbd ya hada duk wasu qualities da ake bukata a wajen namiji... Duk wann abun ita fannah bata dauka cewa soyayya suke kamar yanda kullum maryam da vaneesa ke tsokanar ta.. Sede tace masu shaakuwa ce kawai.. Tunda ita de tasan babu wata soyayya da suke hasalima ko numbern sa bashi da ita haka shima bashi da tata.... Har mummy da daddy sun san da Dr Amah a bakin su Hisam da ita kanta fannah... Snn bangaren ta yanda zata shawo lamarin family dinta yana nam a ranta duk da har yau be kara mata maganar ba...
Yaude ta yande wata shawara... Dan haka tana komawa gida ta gama duk abinda zatayi da daddare bayan ta kwanta ta dauki wayar ta.. Ta shiga IG duk da ita she's not irn social media person dinnan... RADDA tayi searching.. Aikam sega radda dayawa sun bayyana... Taga SADEEQ RADDA, AMOON RADDA, SULTAN RADDA, FARUQ RADDA, JIDDAH RADDA, YUSRAH RUDDA, SUMAYYA RADDA, HAFSAT RADDA, FAREEDA RADDA, SALEEM RADDA, FUAD RADDA, HABIB RADDA, dade sauran su... Fannah ta rasa ina zata saka ranta da farin ciki... Ynx nan duka family dinta ne knn duk suna nan.. Sunan duk suna tare, sun san juna amma basu santa da kaninta ba..😢Hawaye suka taru a idanun ta... Ta sauri ta share.. Tama rasa wanne zata shiga.. Kawai tayi clicking AMOON shi da ta taba jin sunan sa an kira kuma yana cikin qasar da take..
More comments more typing..
✨✨✨
Ur
Nafeesatuu....😍😍

LOVE CYCLE❤✨Where stories live. Discover now