*💫❤LOVE CYCLE✨*
Written by
*@nnafie🖤*
(Smll but mighty😉)*writer of*
Saif
Adaan
Wata mafita
Saboda duniya
Love cycle......Bismillahir rahmanir raheem
💫❤Love cycle❤ (20)✨
Kodaga yanayin yanda jiddah da yusrah suke ma chucu kade ya isa ya nuna maka zancen Amoon suke so suji tanayi.. Ita ko gaba daya batasu take ba se yima Fannah tambayoyi take cike da nishadi da murnar ganin ta.. Har seda sadeeq yace "madam wai ko har kin fara akin ne".. Chucu ta kyalkyake da dariya "kai yaya sadeeq" fareeda tace "ai ko kashi kake kaga chucu ka zauna kawai" duk dariya akai tayi.. Farouq ne ya shigo.. Ware idanu yayi yana kallon chucu kamar yanda itama tayi ganin sa yace "chucu" dan langwabar da kai tayi yace "chucun farouq ko ta Amoon ce" yusrah tayi saurin cewa ta farouq din de.. Duk dariya akayi chucu ta juya tana kallon yusrah "oh nima kishin kike dani?" Yusrah tayi dariya "eh harke"... Chucu ta koma kusa da farouq "yayana I missed you me America tayi maka ne ka dauke kafa" yaja hancin ta "abie ne beje ba shiyasa ba ki ganni.ba nayi missing chucun dadd".. Hafsa tace "katuwa da ita wai auta".. Chucu ta dubi Fannah tana dariya "kinga don't mind them kishi fa sukeyi"... Sosai Fannah taji chucu ta birgeta dan daga gani tana da son mutane duba da duk wanda yazo yake tsokanar takuma ta biye.. Yanayin ta se yake mata kama dana maryam.. Koda Fannah zataje gida tare suka tafi... Acan ta iske mammah dinta. Tare da mummy nan ta gaisar da mummy cike da ladabi.... A ranar maryam tazo koda suka hadu da chucu suka rinka lvri kamar sun san juna chucu tanada saukin kai snn ga hakuri but a yanayin ta seka dauka zatayi girman kai sede ko daya sanyi ne da ita a dan zaman da sukayi da Fannah duk ta fahimci hakan dan gidan su Fannahr ta koma kwana tana da saurin sabo shiyasa ta saba da mummy da hisam harma da daddy.
Fannah ta jefa ma chucu datayi tagumi tana kallon ta da wani murmushi pillow... Chucu ta chafe pillown tana dariya.. Fannah na hararan ta tace "kin wani zubamin idanu...".. "Pls cigaba wlh labarin wnn Amah din naki dadi yanayin yanda soyayyar ku ta fara dole ki soshi but ynx tsaya how about sultan".. Fannah ta ware hannu "ya zanyi babu wanda zeyi supporting dina".. Chucu tace "amma idan shi Amah din ya dawo kafin aurenki da yaya sultan ya zakuyi"... Dan murmushi Fannah tayi.. "Bazan iya ina ganin Amah na auri wani ba".. "Gsky kina sonsa sosai" cewar chucu.. I wish na gansa wnn son da kike masa bana wasa bane.. Yanda duk kyan yaya sultan da kuma komai nasa kikafi son Amah dinnan akansa nasan ya hadu.. Ya hadu ko?" Chucu ta tambaya tana wani ware idanu... Yanda tayi din seda Fannah ta lumshe idanu ta hango fuskar Amah... Chucu ta kyalkyale da dariya... "Dan Allah ki fadamun".. Fannah tace "shi Amoon dasu chucu suka makale masa duk yafisu kyau ne"... Da sauri chucu ta ware hannu "Aa wlh ya fisu tabb ke yayana fa bade yan mata ba kuma bn taba jin yace yanason wata ba.. Though he once told me akwai wacce yake so one day one tym zan santa.. Shiyasa kawai su Jiddah ke bani tausayi coz dama ace babu wacce yake so ze iya auren su but tunda yace akwai nasan babu wanda ze sauya masa ra'ayi.. Kafiya ne dashi shiyasa ko ynx da ake cewa za'a hada masa su Jiddah da yusrah jinsu kawai nake yaya akwai kafiya da taurin kai nasan za'a sha daga..."Fannah kallon ta kawai take.. Ita kanta har taji tsoran Amoon din nan take chucu ta ware hannu "amma kar ki fada wa kowa dan su yusrah sukaji zancen nen nasan akwai dan karamin tashin hankali da rashi lafiya wanda yaya kade ya isa yasa komai ya lafa bayan Allah ....
Fannah tace "toke wane saurayin naki".. Chucu ta ware idanu..."eh fadamun"... "Zan fada maki ba ynx ba"... Fannah ta harare ta duk wnn zubar dana gama kina nufin bazaki fadamun ba.. Fareeda ce ta shigo da sallama.. Chucu tace "yaya sadeeq na gida".. Fareeda ta girgiza kai wai suna da meeting ne tun safe a company..... "So nake mu fita kinga Fannah tanason yin siyayya kafin ta koma jibi zata wuce wlh harna fara missing dinta." Dariya Fannah tayi to kizo muje mana ai bazamu dade ba wnn karon 2months kawai zamuyi.. Dariya chucu tayi tab.. Dama harda su mummy da sena biku amma no"... Sultan ne yazo ya kaisu suka siyo abubuwan da sukeda bukata seda suka biya suka aje maryam dan tare sukaje snn suka dawo gida.. Chucu ta shige ta barsu.. Sultan kau ji yake kamar kar su rabu dan gani yake idan ta koma soyayya Amoon zata sake dawo mata sabuwa.. Ya dubeta yace "ko sati fa bazan iyayi bnganki ba".. Tayi dariya yace "serious duk tym din da nake free zaki ganni ne kawai".. Tace "don't stress ur self" yy murmushi "inde akanki ne babu abinda kemun wahala" murmushi tayi tana bude motar ta fita... Itakanta tasan zatayi missing din duka yan family din barin ma farouq gashi bayanan zata tafi.. Yana kano tasan zatayi missing dinsa bana wasa ba... Wayar ta ta dauka ta kirasa kamar zatayi kuka bayan ya dauka tace "ynx haka zan tafi bnganka ba..." Daga can farouq yadan lumshe idanu "my dear da Nigeria da London duk dayane..inde ina free zanzo kodan sbd ke nasan senafi missing dinki" ta langwabar da kai.. Promise me zaka rinka zuwa". "Sure dear"... Sallama tayi masa.. Chucu tace "kedawa".. "Yaya farouq ne wlh bakiji yanda na damuba tafiyar nan dayayi".. Zuciyar chuchu tayi wata irin bugawa.. Lokaci daya kuma taji relief data tuna cewa farouq shi mutum ne na mutane dan inde kana tare dashi dole kaji ya shiga ranka sbd ya damu da damuwar mutane...
Ana gobe Fannah zata tafi wuni sukayi a gidan baffa ita kanta tasan zatayi missing dinsu ita kanta setake jinta wani iri wai ynx itama kamar maryam haka zata rika zuwa kuma bada su mummy ba hisam ma har ansakasa wata sch din anan har gara ma daddy ze rinka zuwa duk da su mummyn suma bawai sun taso gabadaya bane...
Tare da maryam suka tafi ko a flight maryam se dariya take mata ganin yanda tayi jugum jugum tana tsokanarta wai itama taji yanda akeji hararanta Fannah tayi.. Maryan ta ware idanu tana dariya.. "Do you think is easy kabar gidan ku da family dinka ka tafi wani waje karatu.. Ynx zakiji yanda akeji ai.".. Fannah de bata tanka taba ... Koda suka isa maryam ce tayi komai ita de Fannah na kwance.. Se dare nema tadan ware sanadiyyar video call da sukayi da daddy da mummy se kuma farouq.. Bamasu ba dayawa sunyi vedio call dasu taji dadi sosai yanda kowa ke nuna yy kewar ta da yanda suke kokarin bata kulawa...
Ranar da sukaje makarantar memories dawaya sun dawo mata.. Ganin yanayin ta yasa maryam ta kama hannunta pls yakamata ki manta da komai ki fuskanci present.. Fannah tace "pls ko zamuje mu tambaya".. Maryam bata musa mata ba sbd ta kula da yanayin ta...
Duk wanda sukasan ze san inda Amah yake sun tambaya amma amsar daya ce Amah baya England dan idan ze shigo seda dalili wato ko wani surgery ya kawosa...maryam ta rike hannun fannah tana wasa dashi kafin tace "inaso ki cire amah a ranki tunda har ga sultan nan"... Fannah ta fashe da kuka... "Maryam bazan iya ba I can't wlh ko dede da second daya son Amah be taba raguwa a raina ba se ma karuwa".. Har suka isa gida Fannah bata dena kuka ba....
Fannah ta ringa kallon motar dake parke a gaban apartment din.. Idan bazata mata ba kamar motar farouq wacce ya hau ranar data fara ganin sa..bude motar farouq yy ya fito.. Da sauri ta karasa wajensa ta fada jikinsa ta fashe da kuka.. Bubbuga bayan ta yy yana lallashin ta... Maryam ce taje ta bude masu suka shiga.. Da kyar ya samu tayi shiru maryam ce tayi masa bayanin dalilin kukan nata.. Farouq yy tagumi yana kallota..
Bayan farouq ya samu ta kwantar da hankalin ta har ta ware take cewa "wai yaya daga kano ka taho nan ya gyada mata "next week bani da wani tym dubai zan wuce shiyasa nace yakamata nazo na dan duba ki ... Fannah tayi farin ciki sosai da zuwan farouq dan ko ba komai damuwar ta dayawa ta kau.. Kwana biyu yayi snn ya koma Nigeria..... Fannah ji tayi babu dadi.. And daga nan sultan ma yazo shima taji dadin zuwan sa.. Har ya tafi.. Sukacigaba da maida hankali suna karatu.. Daddy ma yazo... Sultan baya sati biyu be zo mata ba.. Kuma tanajin dadin kulawar sa farouq ma kullum suna waya.. Ta fahimci wani abu a duk lokacin da sultan yaga suna waya da farouq mood dinsa yana canzawa shiyasa ta fara kiyayewa bata yarda suyi waya a gabansa kuma ko sau daya bata taba fada masa farouq na zuwan mata ba.. Sede abinda bata sani ba sultan ya sani.. Seda suka shafe 3months snn suka fara shirin komawa gida.. Ranar da zasu koma farin ciki wajen Fannah ba'a magana tayi missing mummy bata taba ko kwana daya babu ita ba se wnn karon.. sultan ne yazo ya dauke ta.. Sukayi bnkwana da maryam da yaya khaleefa yazo dauka.. He's was lyk "ki gaisar min da Jiddah".. To shknn zataji... Koda suka daho sultan yace "shi khaleefan son jiddah yake ne" Fannah ta Gyada kai "wlh ko mugun son ta yake amma tayi bris dashi".. Yace "son Amoon ya rufe mata idoh.. But da zataji tani data hakura da Amoon ta kama khaleefa tunda yana sonta".. Fannah tace "hakane".. Ya dube ta yace "nima gara azo ayi magana asaka bikin mu ko".... Murmushi kawai batare da tace komai ba.. Itama tana ganin hakan kawai ya kamata coz kila idan taga gidan wani zataje ta cire Amoon a ranta... Yace "kin amince?" Gyada masa kai tayi.. . Sosai sultan yy farin ciki har suka isa.. da gudu da fada gida ta rungume mom dinta..yanda kasan ta shekara bata ganta ba.. Hakama hisam.. Babu jimawa sega su yusrah da hafsa da fareeda sun shigo fannah taji dadi sosai chucu da ta ganta kamar tayi hauka... Dan tayi murnar ganinta over duk da suna yawan waya... Ranar Fannah bata samu kanta ba.. Dama su Jiddah suna America se gobe zasu dawo shiyasa .. Washe gari tare sukaje gidan small mom dinsu raheena suka kwana ita da chucu.. Sultan ne ya dauko su ya sauke chucu a gida snn ya ya kawo Fannah har gida.. Tare suka shigo Fannah ta wuce sama shi kuma ya tsaya yanawa tambayar hisam sch... Ta window Fannah taga farouq ya shigo gidan.. Cike da murna ta fito daga daki domin yi masa oyoyo....
Sultan na fita sukaci karo da farouq.. Mika masa hannu farouq yy.. Suka gaisa..farouq yace "tana ciki ne Fannahr".. Sultan yace "sure.. Farouq zanje na samu abie inaso a saka mana rana da ita ai hakan yy".. Sultan yace "sure yayi Allah ya taimaka"... "Ameen idan da gske kk" cewar sultan... Murmushi farouq yy snn ya kalli sultan tundaga sama zuwakasa yace "sultan why are you behaving kamar karamin yaro sbd mace naga kamar ka manta alakar dake tsakanin mu".. Sultan yace "farouq munafunta ta kake.. Ina sane da duk abinda kk duk zuwan da kake England wajen Fannah ina sane da kai".. Farouq ya harde hannu.. "Inaji ita din yar uwata ce".. Sultan ya dage gira daya "yar uwa kade kode wacce kk so".. Farouq yace "sultan na kula bakason zaman lpy yes inason Fannah.. Amma nafi son kwanciyar hankalin ta.. Shiyasa kaga bn shiga tsakanin ta da wanda takeso ba na barta kaima bn shiga tsakanin ku ba nabar ku.. But dana so wlh tun daga lokacin da ta amince zata aure ka ni kuma zan shiga tsakani na raba.. Wlh sultan kai baka fini son fannah ba kawai ni zaman lpy nake bukata".. "Farouq baka son zaman lpy da kanasonta da baka rinka bibiyarta ba".. A kufule farouq yace "sultan banason zaman lpy kayi abinda zakayi kuma inason Fannah har yau har gobe do ur worst".. Dan sultan ya fara kaisa bango... "Ai zaka gani ne a soon in kana sonta daka dena bibiyaryata... Juyawa farouq yayi yafita dan sultan ya bata masa mood dinsa. Ada yanajin ya hakura da fannah ammah sbd Abinda sultan ke masa a shirye yake daya nuna masa shi wane.. Sultanma bin bayansa yayi ransa bace...
Fannah data gama jin komai.. Ta koma dakin ta ta fashe da kukan da take rikewa.. Ynx sbd ita yan uwa ke fada... Ynx sbd farin cikin ta farouq ya hakura da tasa soyayyar ya barwa sultan.. Ta runtse idanu "why is sultan behaving lyk dis".. Tabbass Koda ace tanason sultan yau seta rabu dashi.. Gara ma farouq tunda shine ke tausayin ta yake son zaman lpy.. Ta runtse idanu tana hango farouq... Ko sau daya be taba nuna damuwar sa akanta ba.. Lallai inde haka suke wnn fadan farouq yy hakuri.. Ynx kuma zega ribar hakuri dan ta fasa auren sultan farouq zata aura... " ta kwanta tana kuka sosai...
A ranar farouq ya samu Abie dinsa da maganar yanason auren Fannah... Abie ya rinka kallon sa snn yace. "My son are you ohk ko bakasan zancen su da sultan ba"... Nasani Abie but tun kafin ya so ta nake son ta... Abbie ya rinka kallon sa... Can yace "tashi ka tafi I will think about it".. Tashi farouq yayi ya fita.. Abie ya dubi mamie. Me kika fahimta da yaron nan".. Dan murmushi mamie tayi "na dade da sanin haka.. Sede na dauka ya hakura amma bnsan dalilinsa nayin haka ba tukunna....
Fannah ta fito tare da Hisam babu tambayar da Mummy bata mata ba ta fada mata dalilin kukanta amma taki.. Shiyasa ta korota.. Tana ganin farouq daya fito daga gida ganin su yayo inda suke shiyasa tayi hanyar gidan su farida.. Kiranta yy ta tsaya batare data juyo ba... Ya karasa kusa da ita ganin yanayinta yasa yace "meke damunki".. Juyowa tayi tace "babu abinda zakuce mun ynx ni har na isa na hadaku fada" seta fashe da kuka "jiya duk naji maganganin ku kaida yaya sultan.. Kuma kasani nafasa auren sultan kai zan aura".. Daga haka ta shige gidan su farida tana kuka.. Jimm farouq yayi zuciyar sa nayi masa babu dadi.. Se kuma ya kama hannun Hisam suka shige gidan baffa.. Dakin fareeda ta shiga.. Bata ciki sede karar ruwa a toilet.. Zaunawa tayi saman gadon ta tana share hawaye.. Idon Fannah ya sauka akan wani diary me kyau vaneesa ta taba bata kalar sa janyosa tayi tana dubawa.. Kafin ta bude a hankali tana dubawa tafi kusan kusan minti uku kafin fareeda ta fito.. Turus fareeda ta tsaya ganin ta da wnn diary din jiya dashi ta kwana ta manta yau bata dauke ba.. Gabanta ya dunga faduwa.. Fannah ta dago idanun ta cike da hawaye.. "Fareeda is this real?".. Da sauri fareeda ta girgiza kai tana kokarin kabar diary.. Fannah ta fisge "you mean duk wnn da kk fadamun kinaso dama ba wani bane sultan ne amma baki taba fadamin ba fareeda wane irin kallo kikemun ne"... "No Fannah don't quote me wrong". Fannah ta fashe da kuka sosai.. "Na shiga uku da wane zanji.. Wlh na fasa auren sultan.. ".. Fareeda ta riko hannun ta "pls Fannah ki tsaya ki saurareni ni na hakura da sultan tunda ke yake so ni na hakura ".. Kuka Fannah take sosai ta fizge hannun ta daga rikon da fareeda ta mata.. Ita tayama zata auri sultan wlh ta hakura dashi.. Daga haka ta fice tana kuka hankali tashe.. Gida ta wuce ... Dan gaba daya hankalin ta ya tashi.. Karo ta kusa ci da daddy ze fito... Hankali tashe yake tambayar ta lpy sbd yanda yaga tana kuka.. Ta fada jikinsa "daddy na fasa auren sultan bazan aure sa ba bazan iya ba daddy..." Da confusion ya jata suka zauna saman kujera ya kwantar da ita a shoulder dinsa seda yabari tayi me isar ta snn yace "now tell me meya faru".. Nan tayi masa bayani na komai da yake faruwa.. Shi kansa daddy kasa magana yayi sede yace taje ze duba lamarin.. Amma seda ya tabbatar tayi breakfast snn ya fita..
Ko a ranar duk yanda farouq ko fareeda suka so ganta ki yarda tayi.... Tsab abiee ya gama fadawa yan uwansa yanda sukayi da farouq, nan ma daddy ya fada masa yanda sukayi da Fannah.. Dadd yace "ikon Allah but ya kuke ganin za'ayi..." Mom tace "akira su muji ta bakin su".. Nan da nan kowa yy kiran dan sa... Farouq ne ya fara zuwa se sultan.. Sultan na shigowa seda gabansa ya fadi ganin harda farouq... Abbu ne yace "farouq maimata abinda kaje kafadawa mahaifinka".. Babu bata lokaci ya fada.. Sultan ya dinga kallonsa.. Dad yace "kana da labarin cewa Fannah tace ta fasa auren ka".. Wnn karon ba sultan kade ba har farouq seda ya dago... Abie yace "sure tace farouq zata aura.. Snn kuma fareeda na sonka baka taba sanar mana ba".. Sultan ya dago with shock.. Dama har ynx fareeda na sonsa.. Shi besan da wnn zancen ba tabbas yaso fareeda tun besa mene so ba Amma ynx Fannah yake so kuma bayajin ze iya barwa koda Amoon ne bare farouq"....More comments more typing......
Urs
✨✨✨
Nafeesatuu....😍😍
![](https://img.wattpad.com/cover/316445276-288-k861933.jpg)
YOU ARE READING
LOVE CYCLE❤✨
ActionA love story, strong love, me hade da abubuwan bn mmki I will not say much but just read it I knw you will love it