uncle naseer

332 32 1
                                    

Part 19&20

.... saurin kamota yay,ganin tana kokarin faduwa ...haka suka durfafi su Uncle muhsin da suka nufosu suma,fuskokinsu dauke da murmushi,itadai najma har lokacin gabanta Bai dena bugawa,ba tin hada idon da sukayi da ,alhaji umar,mahaifin naseer,...kallon sani ta rinkayi mai..amma ta rasa aina..duk da kasancewar tasan bata taba ganinsa ba saidai a hoto...koh lokacin daurin aurensu ma bashi ya daura ba su Uncle isah da uncle muhsin ne sukaje a macadinsa , while uncle muhsin ya zama wakilin ungo.....

Tinaninta ne yakatse sakamakon gaisuwar da hadimai gidan maza da mata suke mata...gaida su Uncle muhsin da uncle isah tafarayi..yayinda uncle naseer yarinka gabatar mata da sauran uncles nashi..... Uncle isah ne yace "naseer bayan tsawon lokaci baka wai waye mu ba,yau gaka kazo"..yafada yana mai wani shu umin murmushi...."uncle abubakar ne ya amshe da cewa. "haka yake kwata kwata bayason shiga cikin mu,kamar wasu dodanni,kuma wannan koyarwar uwarsa ce,.."

Uncle muhsin yace tayuyu kawai bayason mutane ne"

Uncle isah yakara amshewa da cewa.."kawai dai zargin zamu cutar dashi yake..kasan haka yake tun yana yaro bashi da yarda"

Murmushi yay musu gabadaya sannan yamatso saitin uncle isah yace..."my uncle na yarda da mutane mana,kawai dai dabbobin cikin zuciyarsu ne banyarda dasu ba.."

Yafada yana juyawa saitin da najma take...

Tabota uncle naseer,yay ya nuna mata alhaji umar dake tsaye gefe guda yana kallonsu..

Yace..."there"

Ahankali ta kai bakinta saitin kunnensa batare da wani ya ganiba tace..."is he your...
Saurin katseta yay ta hanyar janta har inda yake ta durkusa har kasa ta gaida shi....shima uncle naseer din ya gaidashi batare da y durkusa ba...

"How are you doing?"

Rasss! Gabanta ya buga sakamakon jin sautin miryarsa...

Amma sai ta dake tace "I'm fine"

"Allah yay miki albarka ,yafada yana maikai hannunsa kanta yasha,alamarsa albarka.... Yafada yana murmushi....
"Ameen ngd" ta mayar mai smiling back...

Hadiman gidan ne mata suka kama mata jakun kunanta ,,yayin da dayar wadda tun zuwansu taganta tsaye agefe , babbar cikinsu...ta durkusa tace ranki ya dade mai babban daki ta bada umarnin akawoki  bangarenta......

Batare da tace kala ba tabi bayan wannan harimar tai mata jagora zuwa bangaren hajiya rabi (hajjo). Mahaifiyar sarki ,kakar naseer....

Ba wata doguwar tafiya ,suka karaso bangaren hajjo..wanda yakasance gini me tsawo irin na sarauta ,amma fuskar shiga part dinta glass ne gabadaya........sojojin dake gardin wajen ne suka rissina suka gaidata sannnan suka bude musu suka shiga....

Wata farar bafillatar dattijuwa ce zaune a tankamemen parlon ...akan royal chairs..tana kallon tibi tana jan carbi......

Please do vote

UNCLE NASEER  ✅Where stories live. Discover now