uncle naseer

227 31 5
                                    

Part 41&42
💓❤️❤️💋

... sultan ne ke tafaman zarya,acikin tankamemen falonsa.. dinsa, yakai can yakai can shine abun da yake ta famanyi....yarasa ta inda ze bullowa al'amarin......

Gyaran murya da yaji ne yasa shi cikin sauri ya nemi waje adaya daga cikin kujerun da kin ya zauna....yana me bada izinin shigowa. ... ahankali hajjo ta nemi waje ta zauna tana me goge hawayen dake fitowa daga idanunta,da alqabbar ta.....

Sultan na kallon ta,bece mata kala,don shi kansa dauriyace kawai ta cikakkun mazan da ba a fiye ganin kukansu ba....
. ba,harse da taci kukanta ta koshi ....

Sannan sultan yay mata gyaran murya ..yana me cewa ...

"Fulani,munsan kalar radadin da kikeji acikin ranki,radadi ne wanda duk wata uwa da ta tsinci kanta aciki ,dole ne a tausaya mata"..

Dan jimm yay sannan ya cigaba da fadin...

"Fulani inason ki dauki Abdul Naseer, amatsayin kaddara"

Saurin dago kai tai tana me  kura mai ido...

Cigaba da magana yay, Yana me cewa

"Eh kaddara ,da lilin dayasa,nace ki dauke shi amatsayin kaddara kuwa shine,idan kika dauke shi amatsayin kaddara ,hakan yana nuna cewa kin miqa shi ga, Allah,kin kuma nuna cewa duk abun da yasameshi daga. Shi ne,babu wata halitta da zata cutu daga wasu dubban halittun,batare da amincewar ubangijin sammai da kassaiba,harse yace kunfa yakun sannan wannan abun ze kasance akan wannan halittar"

"Amma...

Sekuma tai shiru tana meyin tagumi...

"Amma me?"

"Nace yaya gidansu  indo (mufeeda). Zasu dauki abun,ace aranar daurin auren yarinya,ango ya yanke jiki ya fadi"

Dan murmusawa yay sannan yace...

"Fulani ai wannan andade da gamawa da wannan zance...,don a yau din nan mufeeda zata tare gidan Abdul Naseer...."

Dan jim ta kuma yi , sannan tace...

"Ranka ya dade inada wata shawara"

"Inajinki fulani"

"Nace,idan ran sultan bazai baciba , inason bayan komai ya lafa Abdul Naseer ya dauki mufeeda sukoma can UK din da zama,tinda kaga dama ba anan ya budi idoba,"

"Hhhhm, fulani inace ai mun dade da gama wannan maganar,nace miki Abdul Naseer babu inda ze koma,tinma  ba ayi gasa ansan wanene zeciba,ballantana yanzu da anyi gasa kowa ya shaida shine yaci,, ,kmar yadda na yanke nida zuciya ta dakuma neman shawarar aljani da kakanni suka barmin,na yanke cewar duk wanda ya cinye wannan gasar shi zan baiwa karagata....

Dan jimm yay sakamakon jin motsin mutum da yay ... Saurin leka window dake cikin falon nasa ,wanda daganan zesada ka da dakin namun dajin gidan ,babu kowa wayam yagani,babu motsi ballantana wani abu da zai nuna anzo wajen...

Juyawa yay yakalli hajjo da itama takaraso inda yake,don itama taji karar motsin.....

Ajjiyar zuciya ya sauke yana me rabata ze wuce saurin,shan gabanshi tai tana me yin kasa da kanta,tace....

"Yah sultan ,inaso kasani mulkn gidannan be canci mutum me,raunin zuciya kamar Abdul Naseer ba,be san komai ba face soyayya,baze iya  cutar da wani ba balle aje ga kashe raiba,"

Tafada muryarta na rawa...

Murmushi sultan yay sannan yace

"Kinji nace ze kashe wani ne...ko kinji nace ze cutar da wani ne,inason kisani fulani sanin zuciyar Abdul Naseer cike take da soyayya yasa nace, shine ze gajeni,domin inason ya kawar da duk wani makirci dake cikin masarautar nan ,batare da yaki koh koh zubar da jinin dan adam ba"

"Yah sultan hakan ba me yiwuwa bane ba,dole ne se ya zubar da jini kuma dole ne seyaci amana, saboda tin usul da haka kuka rinka gadar milkin....

Tana fada tai ficewarta batare da tajira yace  uhmm ba...

Da ido sultan yabi ta harta fice daga falon...tabbas yasan ran hajjo ya baci, tinda ta iya gamai wayannan maganganun batare da tsoro ko bacin raiba...sedai zemata uzuri ya kuma lallabata har ta sakko... Dan koh dakarun da aka aika sukashe su Abdul Naseer, shiya aika nasan dakarun tun kan afara gasar suka karar dasu........

Dole na   mika mulkin nan ,ga Abdul Naseer,nanda watanni goma da nai alqawari,dan tin sanda maganar wanda ze gajesa ta fita,suke ta ganin iftila i,inaga idan sukaji dagaske Abdul Naseer din yaegajesa ba wai wai va ... yakarashe fada acikin zuciyarsa.... ajjiyar zuciya yay yana mecewa,"Allah ya iyamana"

Hajjo kuwa bayan fitarta bata zarce ko ina ba,se bangaren da Abdul Naseer, Inda kuma aka kwantar da shi....

Jami an tsaro ne sosai aka zuba a bangaren, tare da umarnin sultan na duk wanda yazo kar abarshi ya shiga ,inbanda hajjon kantaa amma ko aike ne da sunanta aa....

Kaitsaye suka bude mata kofa ta shige ....
Koda hajjo taga halin da Abdul Naseer yake ciki se ta fashe da matsananci kuka tana me rungume shi,irin wannan tashin hankalin take jiyemai shiyasa ta nuna ma sultan batason abashi mulki,tinma fa ba a bashiba kenan inaga anbashi me dun gurum gume....."bazan ta ba bari sultan ya mika wannan mulki a gareka ba dana " takarashe fada tana me dora kanta akan kirjinsa.......

..........

Acan Bangaren hajiya gado kuwa lokacin da tasamu labarin ,yayan hajjo sun dawo batare da wani abu ya samesu ba, hankalin ta yay matukar tashi,tarasa meke yimata da dadi abun duniya ya hadu ya,tare mata,tana cikin wannan halin ne hadimarta zulaihert ta kawo mata labarin , yarima Abdul Naseer ne yaci gasar da me martaba yasa.....

Ai nan take ta hau fatali da kayan dake cikin falonta gabaki daya harseda yayanta ,mata suka fito suka rirriketa ,....nan suka jata suka kaita dakin ta,wato bedroom....suka kwantar da ita...ruwa abubakar da yakasance autanta ya debo ya,bata tasha,tana sha kuwa bacci ya debeta...saboda banju da yake cikin ruwan wanda abubakar ya zuba...nan sukai ajiyar zuciya,.......

Acikin wannan daren ne tawagar gidansu mufeeda ta karaso...dauke da  amarya mufeeda... Tindaga saka tafin kafarta acikin wannan gida taji gabanta yay wani irin yankewa ,taji jininra yanata tsitstsinkewa ,batare da wani daliliba.....

Kaitsaye bangaren Abdul Naseer aka kaita bisa umarnin sultan da mahaifinta.....

Ba su wani dade ba suka ,tafi suka barta acikin tankamemen dakin da aka kaita..... saboda mahaifinta da yace suna kaita su ,juyo. ....dalilin rashin lafiyar Abdul Naseer,da kuma abun da likitan Abdul Naseer din yafada ,cewar zuwa sha biyu 12:00 na dare ze far fado

Acikin daren wannan rana ne, dakarun da daya daga cikin miyagun wannan masarauta...da ya hayo shima domin a kashe Abdul Naseer suka karaso tindaga Niger.....

Hadi da hadin bakin me tsaron kofar masarautar  ya ,,bude musu  kofa suka shige cikin  masarautar....✍️

Dan girman Allah kuyi votting❤️

UNCLE NASEER  ✅Where stories live. Discover now