uncle naseer

220 49 5
                                    

Part 43&44
💓💓❤️💋

...... gabaki daya,al ummar dake gidan sarautar zazzau,sun tashi da matsananci mamaki da al ajabin,abin da suka wayi gari dashi....wato tsintar gawarwakin dakarun da aka hayo domin kashe Abdul Naseer,a kofar part dinsa, yayinda shikuma yake cikin koshin lfy,batare da wani abu ya samesa ba,harzuwa wannan lokacin Abdul Naseer din be farfado ba...
Tambayar da gabaki dayansu sukewa junansu,shine wa yay hakan....
Itadai hajiya gado harzuwa wannan lokacin,babu uhm datace,koda labarin yazo mata....

Acan Bangaren sultan ,kuwa,da hajjo ta takura masa da tambayar ya haka,sekawai yay murmushi,yace...

"Kina tinanin zanbar Abdul Naseer ne, kawai a hannun jami'an tsaron gidannan,nikuma inzo in kwanta....?"

Awannan ranan ne kuma bokan da sultan yakira  asirrince ,ya karaso inda kaitsaye Bangaren Abdul Naseer ,aka wuce da shi...

Sultan,se hajjo,gefe kuma mufeeda ce  azaune akasan carpet ,jikinta na nnade da laffaya...

Yayinda malamin tsubbun da sultan yakira,yake ta famanyin aikinsa akan Abdul Naseer ,
Ba adau wani lokaci me tsawo ba ,boka ya dakata daga abun da yake yi ,yana me kallon sultan yace ...

"Ranka ya dade, rayuwar  yarima tana cikin hadari ,bada ban Allah yasa an kirawo ni ba da tuni wani zancen alke ba wannan....

Dakatawa yay sakamakon tsawar da sultan ya daka mai...

Hakuri ya bashi sannan ya dora dacewa

"Ina mai bakin cikin sanar da megirma sultan cewa, yarima ya yanke jiki ne da lilin asirin da aka yimai,kuma wannan asirin ,ba sha yayba,binnesa akai acan cikin wani jeji a adamawa,nayi iya bakin kokari na don nagano inda aka binne amma abun yaci tura ,saboda wadanda sukayi abun arnen kule kule akasa sukayi,kuma sunyi ne da niyar kashe sa,da yake Allah ya kaddara da sauran kwanansa a gaba ,se hakarsu bata cimma ruwa,saboda daura aurensa da akayi, awannan rana,dalili kuwa su wadanda sukayi abun,anyi shine da sharadin,kar a kuskura a bari ya auri wannan yarinya mufeeda, saboda inhar aka bari ya aureta toh itace zata haifi danda da zezo ya. Kawar da duk wani makirci dasuka dade suna kullawa, sannan kuma ya hanasu karbar mulki daga hannun ka...,domin makiran ba daya bane ...."

Hajjo na gamajin abunda wannan makamina tsubbun ya gaya,seta fashe da kuka tana me mikewa ta fice daga dakin....

Da ido kawai sultan yabita,batare da ya dakatar da ita....

Ajjiyar zuciya sultan yay sannan yacewa wannan makamina tsubbun

"Yanxu ya al amarin farfadowarsa"

"Ze iya farfadowa a yau ma ,sedai ze farfado ne,da cutar fushi wanda ze rinka aikata abubuwa cikin fushi da zafin rai,da lilin kuwa shine ,daya daga cikin asiran da suka mai ya riga da yakamasa,don tin a farko nagaya maka su wadannan magauta ba mutum daya bane,shiyasa kowa da irin nasa shirin.."

Nan dai sultan ya sallame wannan malamin tsubbun,bayan fitarsa ne kuma sultan ya wa mufeeda umarnin da ta zauna a cikin dakin harzuwa farfadowar Abdul Naseer din sannan yafita shima......

Bayan fitar sultan ne,kuma mufeeda  ta mike ta karasa kan gadon da Abdul Naseer yake kwance...

Ta  kura mai ida nu,hawaye na gangarowa daga cikin idanunta ,suka sauka akan kirjinsa...caraf ya bude idanuns,yana budewa kuma ya mayar ya rufe.. hannunsa ta kamo ta damke acikin nata tana me dora kanta a kirjinsa...❤️💓
.........

A wannan rana ne kuma daya daga cikin yayan wannan masarauta...yamiki kafa takanas har garin adamawa .....

Acan Bangaren Abdul Naseer..kuwa  ...  Misalin karfe 9:00 na dare ya fara bude idaninsa bakinsa dauke da addu a...✍️

Ga shinan ba yawa,sekuma wani satin 😗

Saura kiris nayi deleting din ,littafin nan daga profile dina,saboda bacin ran kinyin voting da bakwayi,duk da kasancewar kara tsawon rubutun din da nayi... Masuyi kuma ina godiya ina gaf da fara amsar numbobin masu voting in tura musu ta WhatsApp aradun Allah  .....

Allah yasa mudace


UNCLE NASEER  ✅Where stories live. Discover now