page 2

509 17 0
                                    

*NI  DA KISHIYOYINA*

           *NA SADNAF*

*E.W.F*

*PAID BOOK*

*BISMILLAHI RAHMANIR RAHEEM*

    *Page 2*

LUBA

Mutane da dama suna ganin na aikata abin kunya nayi abin fade naci amana Wanda ni banga aibun abinda nayi ba tunda a musulunce ba haramun na aikata ba so so ne amma san Kai yafi,Ina san Jin dadi a rayuwata Ina san duk abinda nake so a rayuwata ya zama na samu,kina mace Ina mace ba abinda zaki gaya min Ina so naga na Zama mowa a wajen mijina ya zama ba matar data isa ta hada kafada dani Zan iya kashe ko nawa ne,Zan iya zuwa
Ko'ina  Ina dan na samu cikar burina.

Waiwaye


Aisha

Zuciyata cike take da farinciki dawowar da  uban yayana zaiyi.

Ya shafe shekara biyar  a waje   dan ya Karo karatun da yana dawowa zai zama cikakken likita Allah yasan nayi kewarsa Kamar na mutu Ashraf da Afrah ma sai murna suke Abbansu zai dawo,nasan ashraf da wayonsa a lokacin da ya tafi yasani Afrah ce dai take da shekara biyu lokacin daya tafi.

Salisu bashida komai a lokacin da mu kayi Aure dan zan iya cewa auren gata aka masa nima da yake a wajen yayana nake Yana kuma da dan rufin asiri Ina gama secondary school ya nemi salis daya fito da a lokacin ba wani aiki yake ba sai wani karamin chemist da yake dashi,da taimakon iyayen sa dai ya turo kudin aure gidanmu aka sa mana Rana wata shidda masu zuwa.

A lokacin cikin tsananin farinciki salis ya bugo katin engagement na raba wa kawayena,a lokacin banida aminiya sama da Luba da a lokacin makaranta daya muka yi jinin mu ya hadu da ita sosai ba Wanda baisan kawancen mu ba, har ana mamakin yanda akayi tamu tazo daya da ita dan ni Sam bana San hayaniya ita kuwa akwai zuciya da fada gata masifafiya masifarta yasa lokacin samari ma basu fiye zuwa wajenta ba.

A ranar da na bata  labarin salis ya kawo kudin aurena mamaki ta ringayi tana mai salis yake dashi da zan aureshi ita har yanzu bata ga kalar Wanda zata aura ba.

Dariya na sa mata ina nidai Ina sansa luba ni dama nafiso na auri Wanda bashida komai idan munyi aure mayi arzikin tare.

Anan ta hade rai Wai taso muyi aure rana daya bazata so na rigata aure ba cikin dariya nace ta bada himma nan da wata shidda ta samo mijin aure ta tab'e baki tana ita dai taga Kamar nayi gaggawa.

A kwana a tashi ba wuya sai gashi mun fara kirga sattikan Aurena,duk wani shiri da Luba muke yi dan itace gaba wajen fito da anko duk da ba wani shiri take da salis ba amma da ta ga dai shi zan aura ta fara sakar masa fuska a haka har aka sha shagalin bikina Luba tayi k'ok'ari sosai dan ba karamin gudunmawa tayi min ba haka ma a gidansu anyi min gudumawa na Kuma ji dadi matuka.

Duk da na rigata aure ban canza mata ba,
wai dan ganin yanzu ni inada aure hasali kawancen mu kara karfi yayi,dan ba abinda nake b'oye mata game da rayuwar Aurena itama ba abinda take b'oyemin ba ta ma fiye zuwa gidana ba amma idan dai tazo zata wuni a gidana ko da salis ya dawo ma haka zamu hadu mu uku muyi ta hira duk abokanan Salis da suke Santa duk tak'i su a fadarta tafisan ta samu mai rufin asiri sosai,a haka na samu cikin Ashraf har na haihu nan ma sai da ta hidimanta min na ringa addua Allah ya gwada min aurenta nima na rama abinda tamin.

Na tafi shekara biyu da Aure na,  aka kawo  kudin luba murna kamar nayita rawa har salis na tsokanata akan ko a bikinmu banyi murna haka ba,daga yanda naga luba na shiri tana kuma facaka da kudi nasan ta samu irin wanda take so ta aura wato mai kudi,tamkar dai lokacin bikina nima haka na dage muka ringa shirya bikinta,har asusu na ringayi dan inaso naga na mata fiye da abinda tamin.

NI DA KISHIYOYINAWhere stories live. Discover now