page 8

340 28 0
                                    

*NI DA KISHIYOYINA*

           *NA SADNAF*

*E.W.F*

*PAID BOOK*

    *Page 8*

Luba

Ta mik'e da sauri tana "Alhaji kaga idan Wasa kake min ka daina banaso kai yanzu ko sadakar mace aka Kara baka Kamar yanda aka baka waccan basumudiyar zaka yarda ka karba ne"?

Salis ya had'e rai yana "Luba inaga ban tab'a miki zancen Wasa ba ko karki manta ba ke kadai ce matata ba yanda kike takamar ke matata ce kina Kuma so da kishina haka sauran ke sona Aure dai an daura min jiya ranar litinin za'a kawo ta aure dai da na Kara inaga ba haramun bane tamkar lokacin da kike fada da na aureki akan Karin Aure ba haramun bane tom inaso wanan waazin da Kika min a yanzu sai kiyi wa kanki Yarinya na aura baza'a samu matsala da ita ba idan Allah ya yarda"

"Wlh kaci karya Salisu ka wulakantani har ni zaka cewa an daura ma Aure ka Kara cin amanata a Karo na biyu wancan jakar kace min tilasta ma ita akayi yanzu kuma baka ji kunya ba kace min an daura ma Aure ba ma neman auran kake ba sai da aka daura kazo kana fadamin bayan a yarjajeniyar da muka yi da Kai ba Karin Aure daga ni sai Aisha zaka zauna damu"

"Ba inda muka yi yarjajeniya dake akan bazan sake Aure ba luba na gaji da tashin hankali da kukeyi a gidanan ke da Hindatu Kun k'i ku sama min nutsuwa Karin Aure Yana cikin kaddara ta ban isa na kaucewa kaddara ta ba nidai na fita hakkinki dan ban munafirce ki ba tunda it Aisha a lokacin da na aureki bama tasani ba har aka shekara da haka nayi mi ki sai kice naci amanarki na munafirceki dan haka ranar litinin za'a kawota banasan tashin hankali"

"Idan ka isa Allah ya tsine min ka rasa lokacin da zaka Kara aure sai da na manyanta zaka auro yarinya karama ko kunya baka ji ba dan masifa ka ajiye mata har uku amma sai ka Kara auren ta  hudu,a Ina kaga kwarin rik'e mata hudun mu ukun ma da cutuwa nakeyi ko gamsar da mutum baka iya yi kana daya zaka baje ka hau bacci inaga ka karo ta hudu,? idan su basa gamsar da Kai baka  isa kace ni  bana gamsar da kai  ba dan rabin kudina a gyara suke tafiya, wlh Alhaji idan kana san zaman lafiya a gidanan ka janye auren nan idan ba haka ba wlh tallahi ruwa ma bazaka iya sha a gidanan ba Kuma ka jawowa Yar mutane balai dan wlh dukanta zan tayi har sai ta koma gidan iyayenta.

"Wlh baki isa ki hanani Aure ba luba ba'a aurowa aka auroki a lokacin da kikeso na aureki ta karfi da yaji wane irin wa'azi ne baki min akan Karin auren ba? wane irin magana ne baki min ba dan kawai na aureki? Ashe Aisha ita ba mutum bace sai ta yanki jiki ta Fadi tunda ke kawarta ce na aureki ba kuma ki tab'a Jin komai ba kina ganin ma ai ba wani abu bane sai dan yanzu na Kara aure zaki min hauka.

Wlh wlh Luba abinda na dauka a baya bazan dauka ba ayanzu kinji na rantse miki sai dai duk abinda zai faru ya faru"

Ya mik'e fuuu yayi waje

Luba ta bishi tana "Na rantse da Allah kuwa kayi auren nan sai na baka mamaki abinda nayi nima a baya kadan ne akan wanan da zanyi banda jarraba kana da manyan samari zaka Kara aure,kake hadani da jakar matarka ita tasan ciwon kanta ne nida ita ba daya bane wlh sai na baka mamaki wanan karon abinda kake gudu wlh sai ya faru ka Kara auren kagani"

Alhaji Salis kuwa ko kallonta bai Kara yi ba yayi kwanciyarsa a dogon kujera Luba a ranar kwana tayi tana balai ko runtsawa Salis baiyi ba har sai da Hindatu ta fito taji labarin abinda ke faruwa itama ta kadu da Jin labarin aure zaiyi sai gashi itama ta hau masifa dan ita zaa yiwa kishiyar nan amma Luba ta fita Jin zafi.

Aisha tana daga dakinta tana juyosu hayaniyar su, k'arfi da yaji sun hanata   bacci sai tsaki take daga dakinta Allah yasan da tana da halin barin gidanan da ta bari  dan wlh zaman dole take yi duk tsawon lokacin nan, tana mamakin Halin Luba da Hindatu ko gajiya basa yi da masifa.

NI DA KISHIYOYINAWhere stories live. Discover now