page 6

354 16 4
                                    

*NI  DA KISHIYOYINA*

           *NA SADNAF*

*E.W.F*

*PAID BOOK*


    *Page 6*

Alhaji Salis

"Aisha kin hanani samun nutsuwar zuciya na rokeki nayi miki kuka na sa mahaifiyata ta rokeki duk wayanda kike Jin kunyarsu na hadaki dasu Abba da Umma ma sun baki hakuri akan laifin da na miki Aisha kin k'i ki hakura tsawon shekarun nan Aisha karki manta fa bawa bai isa ya tsallaka kaddararsa ba rabo ne tsakanin nida Luba shiyasa Allah ya hukunta na aureta"

"Toh kaji na ce ma wani abune yanzu"?

"Haba Aisha kafin na auri Luba ai ba haka mu ke zaune da ke ba yanzu kiri kiri nake ganin kiyayya ta a idonki"

"Hmmm daga lokacin da ka auro Luba da ka san kawata ce yaci kasan ka tarwatsa duk wata soyaya dake tsakanin mu da yarda har gobe Zan fada da babban murya wlh tallahi zaman yarana nake da hakuri babu digon kaunarka a raina Koda duk mutanen duniya ne zasu hadu su ringa bani hakuri  batun Kuma baka da nutswar zuciya ai ba ni na hanaka nutsuwar zuciya ba tunda kana da luba,da kafi so da kauna ai Ina ganin baka da wani matsala abu daya nakeso.na fada ma shine ka ja mata kunne duk da nasan ba iyawa zakayi ba amma dai zan fada ma kace Kar ta kuskura ta Kara tab'a min Nana da na karbi amanarta wlh duk ranar da ta kuskura ta Kara tab'ata a ranar ba ita ba har kai sai na baka mamaki kaga duk abinda kuka min ban tab'a ce muku komai ba wlh ko Ashraf naga tana duka bazan kalli Inda take ba amma idan har ta tab'a min Nana wlh zan baku mamaki Banda kaddara data gifta mana da ba abinda Nana zatayi a gidanan ballantana har a kirata da agola"

Alhaji Salis kasa magana yayi ya zubawa Aisha Ido duk Yana jin kwarin gwiwar daya zo dashi ya sace.

"Aisha auren nida Luba da Hindatu wlh kaddara ce zan sake rantse miki ba wacce nake kauna a  cikinsu".

"Hakane kam tsabar kiyaya ma gashi har da yaransu uku uku nifa daka so su da Kar ka so su Salis ba abinda ya shafeni bane bansan dalilin daya sa kake gayamin ba"

"Aisha rashin samun hadin kanki da rashin bani dama yasa zan sake Aure"

Sai ta saki murmushi har hakoranta suka bayyana tana "Allah ya sanya alheri kace su Luba za'a sake samun sabuwar kanwa"

"Abinda Zaki ce kenan Aisha yanzu banida wani mutunci a idonki da zakiyi kishina"?

"Ina mutuncin yake Salis mutunci ai ya dade da zubewa sai zaman ibada kawai kishi kuma ba sai kana san mutum zaka ji kana kishinsa ba ai ni yau banki Allah ya gwada min ranar da  zaka shigo min da takardar saki ba"

Zuwa lokacin ran Alhaji Salis ya Kai kololuwa wajen b'aci

Ya mik'e yana " shikenan Aisha idan saki kikeso insha Allahu mutuwa ce zata rabamu ba abinda zai saka na tab'a sakin ki insha Allahu watarana zaki yafemin"

Daga haka ya fice daga d'akin Aisha taja tsaki.

Koda ya fito a bakin k'ofa yaci karo da Luba ba yau ya fara Kama ta tana labe ba ko a d'akin Hindatu yake haka take zuba laben ya zuba mata wani mugun harara Yana "Baki ji dadi ba wlh duk da kin manyanta kin kasa girma Allah ya kyauta"

"Ikon Allah ni na aikeka wajenta ta ma rashin mutunci da zaka zo ka hucce a kaina"

Bai kulata ba yayi waje ko zaman gidan bayaso yayi.

Sai da ya fara Shiga Bangaren yaran duk ya dubasu dan asabar ta Kama ba makaranta ya shafa kan Nana da murmushi Yana tambayarta mai zai taho mata dashi ta hau lissafa masa ya gyada mata kai tare da yin waje.

Yana Jin maganar luba a bayansa akan ga abincinsa can ko kallonta baiyi ba ya shige motarsa ya nufi gidansu.

Bashida inda zai je sama da can gwara ya wuni a wajen hajiyarsa  da dai ya zauna a gidan.

NI DA KISHIYOYINAWhere stories live. Discover now