page 9

381 24 7
                                    

*NI DA KISHIYOYINA*

           *NA SADNAF*

*E.W.F*

*PAID BOOK*

    *Page 9*

Aisha

Kuka na cigaba da yi Ina Jin Aunty mamy na cigaba da sallati yayana sai da ya dau tsawon mintuna kafin yace "Salisu dai mijinki shi ya Auri Luba kawarki har tsawon shekara daya baki sani ba"?

"Eee yaya ban tab'a sanin suna soyaya ba duk na d'auka aiki yake yi a Abuja bansan Luba ya aura a b'oye ba ya barni anan Yaya Ina fama da Yara shi Kuma ya Kai Luba Abuja Yaya idan Luba zata iya cin amanata ya dace Salis yaci amanata wlh bai tab'a nuna kaunarta a gabana ba kullum cikin kusheta yake tsana kawai yake nuna mata a fili ashe soyayya suke bansani ba sai ya kwashi wata kafin yazo wajena Yana wajen Luba,idan yazo haka zan ga ana ta kiransa yacemin ana nemansa a asibiti a daddafe yake sati daya bashida lokacina bashida na yaransa ashe Luba ya aura"

"Na dade Ina fada miki Aisha ban yarda da kawar nan taki ba a ranar da kuka tare a sabon gidanku idan baki manta ba har daki na kiraki na fada miki sau biyu Ina Kamata tana kallon mijinki kallo irin na soyyaya har ta zauna tana fada miki ita irin Salis take so ta samu ta aura a fakaice har tana baki dace da gidanki ba ita ta dace da gidan Kika sake mata ba inda bata Shiga a gidanki sau nawa na Miki fada anan,yanda Kika San Mara wayo haka Kika maida kanki a wajenta ke gaki bakya so tace bakida mutunci sabida kunyi kudi ai ga irinta nan duk yanda kike da ita ta zage taci amanarki Yan uwanta Suma basuji kunya ba suka hadu aka ci amanarki yanzu Yan uwansa zasu ce basu san ya Kara Aure bane"?

"Basu sani ba Aunty mamy dan a boye ya aureta wai da yarjajeniya baza'a su fadawa kowa ba nidai Aunty mamy ki fadawa Yaya wlh bazan koma gidansa ba ya karba min takarda ta tunda har ya fifita Luba a kaina wlh na bar mata shi"

Yayana  Allah ya kyauta kawai yace ya fice daga d'akin na cigaba da kuka Ina nadamar duk saken da nayi da Luba tarin Abubuwan da nayi mata sakayyar da zata min kenan har ta haihu ya hada mata taro ya Kai abokanansa da matansu gidan suka Zama kawayen Luba ni da nake matarsa bansan abokanan aikinsa sosai har muyi wani muamalla da matansu ba na tuno yanda Luba ta goge tana ta kyalli da alama ba karamin kudi Salis ke kashe mata ba ashe duk labaran nan da luba ke bani Salisu ne har yan uwanta suma dan sunji kudi suka hadu aka daura Auren cin Amana dan idan Salis ya tashi zakkan kayan abinci na azumi wlh mai shegen yawa nake sawa akai gidansu luba haka zasuyi tamin addua ba gori ba ba wanda ban yiwa dinki a gidansu ba har mahaifinsu ashe har suma zasu yarda su daura auren Salis da luba da arziki a gidan wasu gwara a nasu kenan"

Na Share kwalar da nake wahalar da kaina wajen sharewa dan ba daina zubowa zaiyi ba.

Dak'yar Aunty mamy ta tilasta min na Sha tea yayana ma na tsaye a kaina sai cemin yake sai na dorawa kaina hawan jini sabida namiji shi dai bazai min dole na zauna da Salis ba amma shi baiga abin daga hankali ba tunda ba haramun bane sai dai ace ana barin halak dan kunya,Kuma Salis bai kyauta da ya boye min ba da ya fadamin ai yasan bazan hana ba.

Karfe bakwai Ina daga d'aki su Ashraf zagaye dani a kwancen da nake Nana na kwance a jikina duk yarana ma ba mai makale min Kamar ita wlh Ina kaunar Nana yarinya tausayi take bani idan na tuno ba'a san waye mahaifinta ba ban tab'a sallah ban roki Allah ya tona asirin wayanda Suka yiwa muhasim fyade ba da yanzu tana gidan mijinta a mutunce tamkar yanda Khadija tayi aurenta tunda su biyu ne kawai Mata a wajen Aunty mamy.

Sallamar Salis naji a tsakar gidan haka yasa na runtse idona wlh muryarsa da naji ya Kara tasomin da wani tsananin bakin ciki ko kaunar ganinsa bana yi jiya da yayi niyya ai zai hau wani motar ya biyoni amma ya koma wajen matarsa sai yau yaga damar biyoni sabida banida wani matsayi a wajensa.

NI DA KISHIYOYINAWhere stories live. Discover now