*NI DA KISHIYOYINA*
*NA SADNAF*
*E.W.F*
*PAID BOOK*
*Page 5*
Alhaji Salis
A lokacin daya je ya samu mahaifin Aneesa akan turo manyansa izini ya bashi akan ya turo dan Aneesa tace ita tana San shi Kuma mahaifin Aneesa ya dan yi bincike akan Alhaji Salis bai ga Yana da wani matsala ba.
Sati ukun da yayi niyyar yi ya fasa ya d'auko hanyar gida dan ya fadawa Iyayensa ko da wasa bai tab'a kawowa kansa sake aure ba, hasali ma addu'ar sa kullum bai wuce Allah ya raba sa da Luba da Hindatu cikin sauki ba, ya zauna da Aisha uwar yayansa Wanda tunda ya aureta sai dai Santa ya karu a zuciyarsa sai gashi kaddara yasa ta maida shi hoto shi yasan akan dole take zaune dashi sai gashi kaddara ta sake hadasa da Aneesa dayaji Santa a zuciyarsa kwatankwacin irin san da yake yiwa Aisha har a yau da yake da manyan Yara Allah ya hore masa lafiya Yana bukatar nutsuwa a rayuwarsa sabida k'in da Aisha take Masa yasa baya samun nutsuwar da yake so a wajenta tunda shi kadai yake kidansa yayi rawarsa Hindatu da Luba kuwa baya kaunarsu ballantana yaji a zuciyarsa Yana samun nutsuwa dasu, hasali har fargabar kwanansu ya zagayo yake,ko a yanzu da yake san auren Aneesa kasan zuciyarsa cike take da fargaba da tsoro dan Luba ba k'aramin daga masa hankali tayi a auren Hindatu ba ko tunawa baya so yayi kalar cin mutunci da ta masa, tayi dambe kuwa da Hindatu tun kafin ma ya aureta yafi a kirga Inda yake dan samun sauki shine Hindatu itama ba kanwar lasa bace sau tari Yana so ya samu ko wata daya ne a gida ya samu lokaci da yaransa ya samu ya cigaba da rarrashin Aisha sai dai bai isa ba dan tashin hankali Luba da Hindatu ke saka shi tafiyar da bai shirya ba.
Ko daya iso garin katsina sai da ya fara zuwa gidansu mahaifinsa shekara biyar kenan da rasuwarsa mahaifiyar sa ce kawai ta rage masa.
Sai da yaci ya koshi ya fada mata Auren da ya keso ya Kara.
Sai da ta jima bata yi magana ba kafin ta sauke ajiyar zuciya tace "Yanzu Aure zaka sake yi Salisu? Yanzu baka girma da Aure ba? na dauka zaka cemin Afrah ma aka sawa rana, mai zakayi da Aure yanzu tsakani da Allah Salisu? matan ka gasu nan har uku banda tashin hankali da kake so ka Kara karowa kanka tunda ga lokacin da ka tsiri aure aure kayi bankwana da farinciki Aisha dai itace matarka ta rufin asiri daka tashi mata sakayya sai ka auro kawarta Kai ma tunda kayi auren ka sake wani baka Kara samun kwanciyar hankali ba baka tsaya ma a gidanka ba yanzu kana zancen dauko aure anya Karin auren nan naka Mai yuwa ne kuwa?
"Hajiya ya zanyi banida bambancin da Wanda bashida aure shekara da shekaru Ina bawa Aisha hakuri ita kawai nake Jin dadin zama da ita kema wai a haka arzikinki naci Aisha take zaune dani har yanzu.
Luba da Hindatu kaddara tasa na aure su hajiya auren nan da zanyi wlh na dolene kawai da ace Aisha zata yafe min laifin da na mata wlh da ba wani aure da Zan sake to ya zanyi kimin addua kawai dan ko na auren ba gida daya zan ajiye su ba yarinya ce ma wacce zan aura bata fi Sa'ar Aliyu ba"
"Kai yanzu sa'ar Yar cikinka zaka auro cikin manya manyan matan nan naka Salisu kanka daya kuwa ai wahala kawai Yar mutane zata zo ta sha a gidanka ko ka manta suwaye matan naka? Ina laifi ma kace babba ka d'auko zaka aura?ai daga lokacin da ka aikata kuskuren auro kawar matarka ka tusa mata bakin cikin da nasan har ta mutu bazata tab'a mantawa ba Kai ma fa ba zaka tab'a samun farin cikin da kake so ka samu a rayuwar aure ba wlh ba baki nake ma ba hakki ba Wasa bane ba ni nasan Aisha cewa kawai take ya wuce amma ba yafe maka tayi ba"
"Hajiya Kun kasa ganewa kaddara yasani auren kawar Aisha Kuma rabon Yara uku ko inaso ko bana so tunda Allah ya kaddara da rabo a tsakanin mu sai na aureta bansan mai yasa Aisha ta kasa ganewa ba wlh bata kaini bakin cikin zama da Luba ba duk tsawon shekarun nan hajiya wlh ban tab'a kaunarta ba zaman hakuri kawai nake Hindatu Kuma kema kinsan kaddarar da ta saka na aureta mahaifinta ya kakab'a min aurenta nidai kawai ki cigaba da tayani da Addu'a ayiwa su kawu magana suje su kai kudin auren da sadaki tunda mahaifin yarinyar yace wata biyu za'a saka"
YOU ARE READING
NI DA KISHIYOYINA
Actiona heart touching story based on true life story betrayal lov