Wace ce ita?

59 10 0
                                    

💠💠💠💠💠
©®AS-2022.






              *♡CIWO A JIKIN WANI¸.•💥*
                            '''(Kᴡᴀʀɪ)'''
                           



   *HAWWA__B__KUMO.*
     (Rᴇᴀʟ Sᴍᴀꜱʜᴇʀ).💕
*WATTPAD:@REAL-SMASHER.*
*AREWABOOKS:@REALSMASHER.*

     '''Iɴ ᴅᴇᴅɪᴄᴀᴛɪᴏɴ ᴛᴏ ᴍʏ ʟᴀᴛᴇ ᴅᴀᴅ Aʟʜ Mᴜʜᴀᴍᴍᴀᴅ Bᴀʙᴀ Usᴍᴀɴ (B–KUMO).'''
••••••••••••••
   '''Masu buƙatar a tallata hajarsu u should contact me directly via https://wa.me/+2348165726609.'''

                               03

#Wace ce ita?

             Da dare Sanda ya shigo gidan da sallama,hannunsa riƙe da ƴar baƙin leda,kasancewar yana sana'arsa na gyaran babura da motoci a wani garage,shima kuma Yaa Abbor ne ya neman masa maganin zaman banza,a lokacin idan ka ganshi ƙwandala akace ka siye shi baza ka siya ba,duk rana  idan suka tashi aiki aka biyashi ba ya shigowa gida sai ya siyo wani abu ya kawowa mahaifiyarsu,ƙofar ɗakin Maama yayi sallama,ta amsa tana ɗan murmusawa tace "shigo mana ka tsaya waje" ya ɗaga labulen ya shiga da wani sallamar a bakinsa,Maama ta amsa tana masa sannu,yayi murmushi ya ajiye mata ledar naman da ya shigo da shi,ta bishi da kallo cike da so tana ta sawa rayuwarsa albarka,yayi murmushi yace "Maama bari nayi wanka muyi fira" tace "tou Sanda,ga ruwan zafi nan a flask na ajiye maka" yace "na gode Maama" ya fita ɗakin ya ɗebi ruwa a famfo yazo ya karɓi ruwan zafin da Maama take cewa ta ajiye masa,ya sirka ruwan ya ɗauka ya tafi banɗaki yayi wanka,da ya fito ɗakinsu ya shiga ya shirya cikin gajeren wando da riga armless,yana gamawa ya fito yayi sallama ɗakin Maama,ta amsa masa tace "shigo ni kaɗai ce a ɗakin" ya shiga sai kuma ya ɗanyi tsaye yace "Maama abinci fa?" Tace "yana dai inda ka saba ɗauka" yace "okay!" Ya fita ya shiga kitchen ya ɗauko flask ɗinsa na abinci,zai fito suka kusan karo da Aunty dake shigowa,da sauri ya koma baya ya bata hanya da faɗin "sorry" wani kallo tai masa cikin ɗaga murya tace "kaifa Sanda baka da mutunci,yanzu idan uwarka ce za ka bangajeta ne?" Ya ɗaga kai ya kalleta jin yanda ta ambaci mahaifiyarsa,ya gyaɗa kai ya wuce zai fita without saying anything,a fusace ta biyoshi tana zaginsa kamar wanda ya rungumeta,sanin da yayi idan yayi magana sai Maama tai masa faɗa,kawai ya ɗaga labule zai shiga ɗakin,Aunty dake biye da shi ta wani kamo bayan rigarsa ta fizgosa,sosai ransa ya kuma ɓaci,ya juyo da niyyar yai mata rashin kunya,tunda abunda take so kenan,ta ɗaukesa da lafiyayyen mari,tsaiwa yayi yana kallonta speechless,Maama dake jin zage²n Aunty ta fito da hanzari tana tambayar "lafiya?" Cikin fushi Sanda yace "Maama kawai zan fito kitchen na kusa bigeta,na bata haƙuri shi ne ta biyo ni tana zagina" haƙuri Maama ta bawa Aunty ta kama hannun Sanda da zuciyarsa ke tafasa suka shige ɗaki,duk da haka Aunty bata tafi ba,sai da tayi haukarta mai isarta ta tafi,sun yi zaton maganar ya wuce daga nan,kou da Baaba ya dawo gidan Aunty ta haɗa ƙarya da gaskiya ta sanar masa har da yanda Sanda ya fita harkarta ya daina gaisheta,Baaba ya kira Sanda bai tsaya tambayar ba'asi ba ya rufesa da faɗa,abun ya ɓatawa Sanda rai yai zuciya ya tashi yai wucewarsa tunda Baaba ya ƙi sauraransa,kuma shi ne har da sawa ya bawa Aunty haƙuri a gabansa wai yai masu sulhu daga yau kar ya sake ji ko ganin bai gaisheta ba,munafukar har da wani kisisina tana murmushi tace "ya wuce ai Sanda ɗa ne a gurina.." Tun daga wannan faɗan da Baaba yayi masa,Sanda ya dena sakin fuska idan ba a gaban Maama yake ba,sai ko idan Yaa Abbor yana nan,tsakaninsa da Aunty kuwa wani irin sabon tsanarta ya dunga gwadawa a cikin gidan,duk abunda zai yi da zaran ta sa baki akai ko ta taɓa,gaba ɗaya ma ya daina amfani da shi kenan,dan wani shishige masan da ta fara tunda Baaba yayi masu sulhu,shi kuma iya yinsa yake yi na ganin basu haɗa hanya kou magana ta shiga tsakaninsu ba,a haka har Abbor ya shiga final year ɗinsa a jami'a,tun daga nan sai ba'a sake samun wani matsalar da za takaici ƙararsa ba. Cikin daren wata ranar Alhamis,Sanda ya fito ya shiga banɗaki fitsari,sai ya bar ƙofar ɗakinsu a buɗe,so ya saba dama ya kan fito da dare irin haka ya shiga banɗaki ko shan ruwa,har ya gama abunda zai da yake ranan Baaba yana ɗakin Maama ne,kansa tsaye kasancewar Abbor yana school ya rufe ɗakin ya koma ya kwanta,can bacci ya fara ɗaukansa yaji an fasa ihu,a firgice ya tashi ya zauna yana kalle²n ɗakin dake da duhu,fitowar Baaba da Maama suna tambayar ihun me suka ji yasa shima ya tashi ya buɗe ƙofar ya fita,Baaba ya kalleshi yace "baka ji wani ƙara ba?" Sanda yace "na ji yanzu shi ne ma yasa ni fitowa,dan ban jima da fitowa naje banɗaki ba" duk sukai Allah ya kiyaye,Baaba yace "amma lafiya Aunty'nku bata fito ba?" Sanda ya wani haɗe rai ya juya zai koma ɗaki,Baaba ya ƙarasa ƙofar ɗakin Aunty yayi knocking,shiru yaji batai magana ba,ya fara kiranta sai yaji ta amsa cikin shesheƙar kuka,sannan ta taso ta buɗe ƙofar,kallonta ya dunga yi cikin hasken farin wata yace "lafiya?" Cikin kuka tace "idan da lafiya me zai sa ni kuka a irin wannan lokacin?" Hankalin Maama duk yana kanta tana sauraranta,Baaba yace "ki sanar da ni kukan me kike da daren nan" Aunty tace "mu bari dai da safe kada ace na cika fitina" Baaba yace "wane irin safe kuma,ki sanar min yanzun nan" cikin kuka tace "gaskiya abunda ɗanka yake yi a cikin gidan nan bai kamata ba,da ina gani ina yin shiru amma yau sai naga abun yana neman wuce gona da iri" Baaba ya gaji da dogon zancen da ta ɗauka yace "wai mene ne yake yi ne? Ki sanar da ni Kai tsaye" tana goge hawaye tace "ai shi ne zan sanar maka" yace "ke nake sauraro" tace "yanzu saboda Allah duk duniyar nan,idan zai tsallake²nsa ai bai kamata ace yayi a cikin gida ba kou?" Kansu duk ya ɗaure sun kasa fahimtar me take son cewa,tace "duk ranar da ba ka ɗakina ya kan fito yazo yana ƙwanƙwasa min ƙafa,ban taɓa sanar maka bane dai,amma ace ya rasa wanda zai nemi ya keɓe da ita sai ni kuma da ranka,naga kou mutuwa kayi ai matsayin uwa nake a gurinsa tunda nake matar ubansa,idan har zai kwanta da ni me zai hana yayi da uwarsa" jikin Baaba ne ya fara tsuma banda kallonta babu abunda yake yace "wane ɗan nawa?" Tace "wane ɗa kuwa banda Sanda" salati Maama ta ɗauka saboda maganar sam hankali bazai ɗauka ba,Sanda kam da yaji maganar sosai ya shiga shock ya ma kasa ko wane irin motsi dan bai kai ga komawa ɗakin ba Maana ta riƙosa ta tsayar da shi,Baaba yace "a cikin gidana za'a yi wannan ƙazantar? Kuma ɗan cikina?" Maama tai saurin tarar numfarfashin Baaba tace "a'a Babansu kada kayi saurin yarda,ni dai ina da tabbacin Sanda bazai taɓa aikata haka ba,haba yama za'ayi ko tunanin haka yayi? Ai idan mafaɗin magana wawa ne majiyinta baya zama ba" cikin kuka da ihu Aunty tace "kenan dai kina nufin ƙarya nai masa?" Maama za ta sake magana Baaba yayi mata tsawa,cikin ɓacin rai ya fara faɗa ta inda ya shiga ba ta nan yake fita ba,Sanda har lokacin yana tsaye ne a gurin amma kwata² ya dena fuskantar abunda suke faɗa,har sai da Baaba ya kama wuyan rigarsa ya fara jansa ya nufi ƙofar fita daga gidan,Maama ta fashe da kuka tana kallon yanda Baaba ke jan Sanda tace "dan Allah Baaba kayi haƙuri,ni na haifi Sanda halayensa babu wanda ban sani ba,na san abunda zai iya aikatawa da wanda bazai ba,dan Allah kabi komai a sannu kayi bincike,kada ka yanke hukuncin da za kazo daga baya kana nadama.." Baaba bai saurareta ba sanda ya buɗe ƙofar duk gari yai shiru baka jin motsin kowa,waje ya cilla Sanda cikin tarin ɓacin rai yana ɗaga murya yace "kaje na yafe ka wa duniya tunda har rashin tarbiyyarka ya kai ka iya neman matar ubanka,tsinanne la'ananne,Allah ya wadaranka ya wadaran uwar data haifeka,in sha Allahu yanda ka nemi tozarta ni sai ƴaƴan cikinka sun maka fiye da haka,kaje na yafe ka daga yau,babu ni babu kai ko a hanya ka ganni ka nuna ka sanni Allah ya isa,ɗan iskan yaro watsatstse,kusa da ni inda hali ba na fatan ka sake zuwa,kaje Allah ya isa tsakanina da kai.. Idan na mutu ko kan gawata ban yarda ka zo ba,idan kazo kuma ban yafe ba.." Maama tana kuka cikin soron gida ganin Baaba zai rufe ƙofa ta ɗaga murya tace "Sanda kana ji na? Maza kaje gidanmu zanzo in sha Allah gobe" bata ƙarasa ba Baaba ya buɗe ƙofar daya rufe ya watso masa kaf kayansa masu kyau da marasa shi,duk wani abu da ya san mallakinsa ne bai barshi ba sai da ya tattaro shi,ya kalli Sanda dake durƙushe ƙofar gidan bisa guiwowinsa yace "idan kaje gurin wasu cikin dangina ko na mahaifiyarku ban yafe ba.. Ga tsiyarka nan daga yau ka ɗauka ba nine mahaifinka ba,nima zan ɗauka cewa ka mutu" Maama dake soron tana kuka tace "Sanda kada abunda mahaifinku yayi maka a yau yasa ka yi zuciya ka aikata wani abu ba dai² ba,ka ɗauka cewa iya abunda yake rubuce cikin ƙaddarar rayuwarka shi ne iya abunda zai same ka.. Masoyi ko maƙiyi babu wanda zai iya sauya komai,ka riƙe wannan kada manta.." Gaba ɗaya duniyar yaji tai masa zafi ya rasa me zai yi,har Baaba ya rufe gidansa bai iya motsawa daga gurin ba,bacci da komai ya ƙaurace masa,tunanin mafita kawai yake amma ya rasa,Maama da ta kirashi² taji shiru,batai zaton yana nan har lokacin ba,jikinta a sanyaye tana sharar ƙwalla masu zafi taja ƙafafunta ta koma cikin ɗakinta,har kusan asuba Sanda yana durƙushe gurin ya kasa tuna komai,kiran farko ya dawo da shi daga duniyar tunanin da ya shiga,jikinsa a mugun sanyaye ya tashi saboda yanda ƙafafuwansa suka riƙe ya tattara kayansa da Baaba ya watso masa ya bar ƙofar gidan,can masallaci ya wuce ya shiga bayan ya adana kayansa a waje ya canja na jikinsa zuwa manyan kaya ya zauna ya jinginar da kansa da bango,sai lokacin wasu irin hawaye suka zubo daga ƙeƙasassun idanunsa daga nan kuma suka sake ɗaukewa,ya ɗauke shi lokaci yana tunani kafin ya fita daga masallacin yayi alwala,yana zaune wajen yana tunanin maganar Baaba tsuntsuwa ta sauka kan wani bishiyar da aka sare,da kallo ya bita jin wani irin sautin kuka da take mara daɗi,ko da ya ɗaga kai ya kalleta mujiya ce tsaye kan iccen tana kallonsa kamar yanda yake,sai da aka kira sallah a karo na biyu sannan ya tashi ya koma cikin masallaci yana waiwayenta,a hankali mutane suka fara fitowa gidaje suna shigowa masallacin,bayan an idar da sallah ya miƙe yabi ayarin masu fita daga masallaci ya fita sanda ya ɗauki kayansa sannan ya ɗauki hanyar barin garin,tafiya kawai yake bai san ina yake nufa ba,bakinsa ya bushe saboda tsananin tashin hankali. Har gari ya waye rana ta fito bai daina tafiya ba,sai da ƙishirwa ta fara damunsa sannan ya tsaya yana kallon inda zai samu ruwa ya sha,hankalinsa sam bai jikinsa shi yasa kou a hanya mutane suke masa magana bai tanka su har ya fita daga Yerwa. A can gidansu ma dai yanda Sanda bai iya samun bacci ba haka Maama ta kwana tana kuka,ga wani irin tausayin Sanda da halin da zai shiga,ta san shi da zuciya akan abu,bare wannan da a gabanta ta ji furucin Baaba akansa,ta tabbatar tunda ya nemi ko haɗa hanya kada ya sake yi da shi,zuciyarsa baza ta bari ya sake haɗuwa da shi ba,ita duk ba ma wannan ne damuwarta ba fatanta Allah yasa kada yace zai bar garin,bata san ina zaice zai nufa ba,har tayi sallah hankalinta bai kwanta ba,da safe kuwa da yake Baaba yace in ta fita kou baya nan a bakin aurenta hankalinta duk ya tashi nan ta aika maƙota aka kira mata wani abokin Sandan tace yaje gida ya tambaya kou Sanda ya zo? Bai jima ba ya dawo da saƙon bai jeba,a taƙaice duk inda take zaton zai iya zuwa ta aika amma kou ganinsa babu wanda yace ya yi,tai kuka kamar ranta zai fita,taiwa Abbor aike makaranta da duk abunda ya faru,hankalin yayan nasa idan ya kai dubu duk sai da ya tashi,gashi lokacin babu waya sai hannun wane da wane,ga jarabawar data sakoshi a gaba babu halin yaje gida,dole haka yake danne damuwarsa yana addu'ar Allah yasa ba barin gari Sanda yayi ba. A ɓangaren Sanda kuwa kamar yanda zuciyarsa ta saƙa masa daga Damboa bai zame ko ina ba sai Biu LGA gidansu wani abokinsa,ya samu masauki wajen Bashir da yake tare sukai makaranta,da suna zaune can Yerwa sai suka tashi suka dawo nan cikin Biu,ranan da ya fara sauka gurinsa bai yarda ya sanar da shi abunda ya rabosa da gıda ba,kawai yace masa yazo ne cike takardan ɗaukan Soja da yaji ana sanarwa a radio,Bashir ya saukeshi a ɗakinsa yana tai masa addu'ar Allah yasa ya samu,ya amsa da ɗan murmushin yaƙe da ya aro ya lanƙaya a fuskarsa,ranan Litinin Bashir ya raka Sanda har barrack na Biu ya cike komai da takardunsa na secondary da sukai kyau,ya gwammace ya nemansa kansa madafa da yaita gararamba a gari bai san ina ya nufa ba,satinsa ɗaya da cikewa da yake kullum yana kan bibiyar yanda lamarin yake ya samu sun amshe shii,ranar da za'ayi secreaning ya shirya yaje,duk abunda ake buƙata tsayi da komai hatta lafiyarsa duk babu matsala,nan aka sanar masu ranan da zasu fara training,tunda ya sanar da Bashir ya fara tattara nasa ya nasa,ranan da za su shiga camp yayi sallama da Bashir da iyayen Bashir ɗin da yake sun san har Baaba,tunda Sanda ya shiga gidan horo na soja zuciyarsa a bushe yake komai,duk training ɗin da za ayi masu komai wahalar da zai sha baza ka ganta a fuskarsa ba,haka nan kwanaki sukai ta zuwa suna wucewa. Idan ya tuna yanda mahaifinsa yayi expelling ɗinsa daga gida abun yana taɓa masa rai,yayin da tsanar Aunty kullum yake ƙaruwa a ransa,duk dare da mafarkin abun yake farkawa,hoping that al'amarin zai ƙare iya nan,but da ya farka zai tarar da saɓanin haka,while soyayyar Maama da Yaa Abbor ke maƙale ransa,duk sanda zai tuna Maama da halin da take ciki yanzu nan zai rasa nutsuwarsa,soyayyarta mai girma tare da tausayinta suna cin zuciyarsa,a haka ya kwashe watanni shida yana karɓar horo,zuwa lokacin kam shi dai bazai ce ga abunda ya faru ba,kawai ya tsinci kansa cikin mugun yanayin ta'amalli da giya,yawan ganinsa da abokai keyi shiru cikin damuwa suka jashi ya fara ɗaga kwalba,cikin lokaci kaɗan ya manta da kowa da komai kansa kawai ya sani,ada ya kan fita cikin gari amma yanzu gaba ɗaya bai son fita idan ba da dare ba,ya koma killace kansa tamkar sabuwar amarya. A can gidansu kuwa damuwar inda ya shiga ya fi komai tayarwa da Maama da Abbor hankali,tunda ya gama karatunsa ya dawo gida suke ta neman inda yake amma basu samu wanda yace masu ya sani ba,a haka aka ɗauki tsayin lokaci,wata rana Bashir suka haɗu da Abbor yake tambayarsa ko ya ga Sanda cikin lokacin nan? Bashir da mamaki lokacin da Abbor ya bashi labarin Sanda ba ya gida basu ma san inda yake ba a halin yanzu,Bashir yace "ai yana Biu" Abbor yace "me yake a Biu?" Bashir yace "ya nemi aikin soja kuma alhamdulillah ya samu,yanzu haka ya fara aiki ma,muna yawan haɗuwa da shi yana zuwa gurina sosai" jikin Abbor har tsuma yake jin an samu labarin inda ɗan uwansa yake yace "ai kuwa zanje na sanar ma Maama inda yake,a yau zan bika muje gurinsa" nan ya bawa Bashir labarin abunda ya faru daya raba Sanda da gida,Bashir yai mamaki yace "amma ni Sanda bai taɓa faɗa min matsala ya samu da gida ba,ko da yaje Biu gidanmu ya sauka gurina,har sai da ya nemi aikin nan,sai da za su fara training sannan ya bar gurina" Abbor yace "ka san mutuminka da fushi,sannan zurfin cikinsa ma bazai bari yayi maganar da kowa ba,kuma tun daga lokacin bai ƙara waiwayo gida ba,hankalin Maama duk yana kansa,kullum sai tai kukan rashin sanin inda ya tafi" Bashir yace "aikuwa ka bata haƙuri sannan kayi mata albishir ɗanta yana nan lafiya ya zama soja" Abbor yace "in sha Allah zan sanar mata kuma yau ba gobe ba zan bika mu tafi Biu na ganshi.. Ya kamata ya dawo gida,kou bazai koma gidan ba dai aƙalla musan yana kusa damu hankalinmu zai fi kwanciya" Bashir yace "gaskiya kam" bayan Abbor ya shiga gida da murnansa ya samu Maama a ɗaki ya sanar mata inda Sanda yake,Maama tana kuka tace "Abbor kai gaggawa kaje ka nemo min shi,bana jin daɗin rashin ganinsa a kusa da ni,ko gidan wani ɗan uwan nawa ne gara na nemi alfarma ya zauna can da dai ace ina zaune nan ban san halin da yake ciki ba" Abbor yace "in sha Allah Maama a yau na yi alƙawarin bin Bashir tunda ya san inda yake zanje na dawo maki da Sanda" Maama dake kuka tace "Allah yasa ya yarda ya biyoka" Abbor yace "ameen.." After asr Abbor yayi sallama da Maama suka tafi Biu tare da Bashir,lokacin da suka sauka yamma yayi,Bashir yace suje gidansu ya kwana zuwa gobe sai suje Barrack,Abbor yace a'a gara yaje yau,baya son saɓa alƙawarin da ya ɗaukarwa Maama,dole bayan sun yi sallar maghreeb suka ɗauki hanya cikin taxi,fatan Abbor bai wuce yaga Sanda ba su koma gida tare,a Barrack lokacin da suka zo suka faɗi gurin wanda suka zo wani Soja yace "taɓɓɓ ɗin ai kuwa Sanda ya bar garin nan" Abbor ya kalli sojan yace "wane gari ya tafi dan Allah?" Yace "an tura shi Anambra state yau da safe" jikin Abbor yai sanyi yace "dan Allah ko zan iya samun address ɗin inda aka tura shi?" Sojan yace "babu matsala" da yake yaga kamar Abbor da Sanda sosai,shi yasa ya gane ƴan uwane su,Abbor da yai shiru cikin wani yanayi bayan sojan ya rubuta masa ya bashi,haka kawai ya ƙurawa takardar ido hawaye suna zuba idonsa yace "me yasa za ka tafi ba tare da kaje ka yi sallama da Maama ba?" Sosai yake kuka yana surutu kamar wanda Sanda yake gabansa,da ƙyar Bashir ya rarrashi Abbor sukaiwa sojan sallama,duk jikinsu yai sanyi da al'amarin haka suka koma gidansu Bashir babu mai yiwa ɗan uwansa magana,washe garin ranar da safe Abbor ya koma Yerwa,tunda Maama ta ganshi shi kaɗai take tambaya "ina Sandan yake?" Abbor da yayi shiru ya girgiza mata kai hawaye suna sauka fuskarsa yace "ban same shi ba,ance sun tafi Anambra jiya da safe" Maama tai shiru tana tunani can tace "yanzu ya za muyi?" Abbor yace "zan siyar da machine ɗina sai nayi kuɗin mota na bishi can" Maama ta girgiza masa kai tace "a'a baza ayi haka ba,akwai ɗankunne na tun wanda Baba ya bani na Mama zan baka ka siyar da shi sai kayi kuɗin motar ka tafi.. Yanzu yaushe za ka fara shirin tafiyar?" Yace "cikin satin nan in Allah ya yarda" Maama tace "Allah ya yarda" ya amsa,cikin kwanakin duk abunda ya kamata sun yi,lokacin da Abbor zai tafiyar bayan sun yi sallama da Maama ya kama hanya,tsaf yabi kwatancen da Sojan nan ya basu,sai dai abun mamakin ko da yaje an sanar masa Sanda bai zo ba,hasalima babu sunansa a cikin jerin sojojin da aka turo Anambra,kwanan Abbor biyu a garin ya koma Maiduguri,sanda ya sanar da Maama nan ma dai kuka kam ta yi shi har ta bawa uku lada,tun daga ranan duk inda za suji labarin anga Sanda basa gajiya da wuri suke yin shawara Abbor zai tafi nemansa,sai dai idan sunje baza su sameshi ba,kamar mai cin layar ɓata,sam sun rasa shi,a garuruwan Nigeria 36 ɗai² ne basu je ba kan neman Sanda a cikin shekara guda,kou da suka fuskanci neman nasa ma kamar ya zama wani jaraba,tunda ko sun je ma basa samunsa duka suka miƙa lamarin gurin Allah,a hankali lokaci ya dunga tafiya shekaru suka fara nisa,lokaci ɗaya Sanda ya ɓace aka neme shi aka rasa,har dai lokacin da labarinsa ya shuɗe ya zama tahiri a gurin mutane,wasu kam ko tunawa da shi ma suka daina,yayin da a gefen Maama da Abbor suka cire rai da tunanin wai yana raye cikin duniyar da suke...

                 *Many years later...*

'''ZANGO,KMC (Kano State)'''

        Wani irin unguwa ce da kana kallo za ka san cewa talakawa sun fi yawa cikinta fiye da masu hannu da shuni,musamman idan kai la'akari da tsarin yanda gine²n unguwar suka kasance a wani irin cunkushe asalin Ghetto area wanda ke ɗauke da mutane iri daban²,Zango unguwa ce dake kusa da kasuwannin Rimi market,Ƙofar Wambai,Kwari da kuma Marina (Kano dye fit) al'ummar cikin unguwar zango sam basu damu da karatun boko sosai ba,sai dai sana'a ko wane iri ne na hannu za ka samesu suna yinsa,matansu da mazansu gwanaye ne wajen neman na kai,sai dai duk da hakan bai hana samun gurɓatattu ba,kamar ƴan shaye² da sauransu.. Fitowar ƴar matashiyar yarinyar daga ɗan madaidaicin gidan around 9:30pm bai sa masu wucewa ta layin da wanda suke zaune cikin majalisu sun kula da ita ba,yarinya ce da baza ta wuce 16yrs ba,duk da kasancewar dare amma hakan bai hana a gane kyaunta,doguwa ce fara idanunta dake manya masu cike da wani irin sirri suna lumshewa da buɗewa kamar wanda ke shirin yin bacci,a hankali ta miƙi hanya tana tafiya ita kaɗanta babu tsoro ko fargar komai da zai iya faruwa duk da yanayin dabanci,ƙwace da satar mutane da ake fama sanadiyyar rashin kyakkyawan tsaro a ƙasa,tunda ta fito bata tsaya ko ina ba sai bakin titi,motoci da sauran vehicles suna ta wucewa ita dai tana tsaye ba tare da ta tsayar da abun hawa ba,can daga tsallake cikin wani majalisa irin na masu zaman banza gaban wani Plaza wani mutum da tun tsaiwarta gurin ya kula da ita yake kallonta,sanda ta shafe a ƙalla 30 minutes a gurin,ganin ba ta da niyyar tafiya ne,kamar bazai taso ba can bayan lokaci yayi tsam ya miƙe daga cikin abokan kartarsa ya nufi inda take,ya tsallako titi a hankali ya tsaya kusa da ita yai sallama,waigowa tayi ta kalleshi da manyan idanunta,yayi mata murmushi yana kallonta,underneath yake yabon kyaunta yana hasaso lokacin da za ta zama cikakkiyar budurwa,yana sauke wani numfashi yace "ƴan mata ina zaki da daren nan? Ba kya jin tsoron tafiya ke kaɗai?" Shiru tayi bata amsa ba ta juya ta ci gaba da kallon ababen hawan da suke ta wucewa,ya sake cewa "kou ba kya magana ne? Nace ina za kije da daren nan kusan ƙarfe 10? Ba kya tsoron dare?" Yanda yaga ta kalleshi idanunta suna lullumshewa yasa shi tsayawa yana kallonta,lokaci ɗaya ya riƙe hannunta yana sake ƙureta da wani kallo,yanda manyan lamppost ɗin titin suka haska ko ina,haka shima ya kureta da mayen kallo a hankali ya furta "ke yarinya ina za kije? Ina ne gidanku? Ina iyayenki suke?" Buɗe lumsassun manyan fararen idanuwanta tayi tana kallonsa,a hankali ta sake mayar da su ta lumshe tana layi kamar za ta faɗi saboda azababben baccin dake cin idanunta,ya kai hannu shoulders ɗinta ya girgiza ta yana sake tambayarta "yarinya daga ina kika fito? Ina ne gidanku?" Sake buɗe ido tayi tana yin baya kamar za ta faɗi,sai dai ta ƙi yin magana,ganin haka mutumin ya fara tunanin abun yi,dan ya gama fahimtar tsabar magagin bacci gareta,can daga cikin majalisar da ya taso,wani ya ƙwalo masa kira da faɗin "Alh Sardauna lafiya? Meke faruwa a nan gurin?"



           This book isn't for free,normal ₦300 posting 5 days excluding weekend,VIP ₦500 posting daily,SP VIP 1K all via 0060746882-Hauwa Muhammad Usman,access bank. Then u show ur evidence of payment via https://wa.me/+2348165726609. If u are willing to pay,my sister pay it now before the price will go up,after it is completed the price is ₦500.



#Follow
#Vote
#Comment
#Share fisabilillah!
#Asli Smasher.

CIWO A JIKIN WANI!Hikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin