Fargaba!

76 7 1
                                    

💠💠💠💠💠
©®AS-2022.






              *♡CIWO A JIKIN WANI¸.•💥*
                            '''(Kᴡᴀʀɪ)'''
                           



   *HAWWA__B__KUMO.*
     (Rᴇᴀʟ Sᴍᴀꜱʜᴇʀ).💕
*WATTPAD:@REAL-SMASHER.*
*AREWABOOKS:@REALSMASHER.*

     '''Iɴ ᴅᴇᴅɪᴄᴀᴛɪᴏɴ ᴛᴏ ᴍʏ ʟᴀᴛᴇ ᴅᴀᴅ Aʟʜ Mᴜʜᴀᴍᴍᴀᴅ Bᴀʙᴀ Usᴍᴀɴ (B–KUMO).'''

      '''Bᴇsᴛᴏᴡᴇᴅ ᴛᴏ Mʏ Zᴀʜʀᴀ Aʙᴅᴜʟʟ Tᴀғᴇᴇᴅᴀ (Nᴀ'ᴇᴇᴍᴀ).'''
••••••••••••••

                               09

#Fargaba!

            Wani irin kallo ya dunga binta da shi na tsantsar jahilcin dake tattare da maganarta,lokaci ɗaya ya tashi ya fice ya bar mata ɗakin,Hamdiyya ta bishi da wani shegen kallo lokaci ɗaya ta gyaɗa kai sannan ta ɗauki wayarta ta fara kiran number Mummy Shafa'atu,Mummy'n nata tana ɗauka ta fashe mata da wani irin kuka tace "Mummy wallahi yaƙi yarda da maganar nan,tun rannan nake binsa yana kaucewa,dan Allah Mummy kiyi wani abu da zaisa ya amince,ina tsoron rasa Mutallab.. Pleaseee" shiru uwar tayi da farko sanda ta sauke wani relieved ajiyar zuciya kafin tace "akan wannan ƴar matsalar kike zubar da hawayenki? Ki tsaya ki saurareni da kyau,ai matsalar nan tunda kece a ciki dole ne na shiga na fita,duk yanda zanyi nayi naga na share maki hawaye,Allah na tuba ko bai yarda ba,mu sai akace maku za mu zuba ido ne muna kallo? Ai dole ne mu san yanda za muyi da shi,kamar yanda idan shi ne a ciki,uwarsa baza ta so ace ki rabu da ɗanta ba,dan haka ki bar kuka ko da yardarsa ko babu mu zamu nemi wanda za tayi abun nan.. Ki barni da shi na san me zan masa" Hamdiyya ta wani gyaɗa kai tana share hawaye tace "tou Mummy.." Mummy Shafa'atu tace "maganar da kika sanar min,ki tuntuɓi Malam Ado kiji idan za mu iya zuwa a rana ɗaya mu dawo sai muyi sammako,in yaso sai ki nemi excuse a gurin aiki kamar za kije ganin Dr sai muje mu dawo" Hamdiyya tayi wani ihu tace "that's my Mummy.. Zan shiga office gobe in yaso sai na sanar jibi baza ni ba sai mu tafin kawai.. Ni bazan ma sanar masa ba sai an gama komai har yarinyar na ɗauko sannan zan faɗa masa,lokacin ai bai isa yace ba haka ba" uwar tace "that's my girl.. Shi kenan yanzu dai ki kwantar da kai,kada ki nuna masa komai har mu gama komai mu dawo gudun kada ya bamu matsala,dan na fahimci mijinki taurin kai ne da shi,duk abunda nake ƙona kuɗina akeyi akansa bai yin tasiri,kamar wuta nake ƙarawa petroleum" Hamdiyya tace "okay Mummy but a mota za muje ne?" Mummy Shafa'atu tace "tou so kike a ganmu a filin jirgi a kirashi kou uwarsa a basu labarin?" Ta wani turo baki kamar tana gaban Mummy'n nata,daga haka sukai sallama kowa da tunanin da yake a tsakaninsu. After some minutes Hamdiyya ta sake ɗaukar wayarta,number Malam Ado driver ta kira,ya ɗauka sukai magana kamar yanda Mummy Shafa'atu tace mata,ta sanar da shi ranar Tuesday za suyi tafiyar ya zama cikin shiri saboda a ranar take so suje su dawo ba ta son a samu matsala,Malam Ado ya tabbatar mata za ayi komai kamar yanda ta buƙata,here tace ya kira abokin nasa ya fara masa highlighing maganar da zai kaisu ba sai sun je sannan a fara jan dogon sentence ba,suna yin sallama Mutallab yana shigowa,da kallon mamaki ya bita ganin yanda take murmushi,fuskarta ya nuna lallai tana cikin farin ciki,sosai ya ƙureta da kallo yana son gano wani abu,kafin ya zauna gefenta kaɗan yace "ya dai? Me ya faranta maki rai haka?" Ta washe baki tace "kai dai ka bari wani abu ne wallahi" yace "bai da suna abun?" Tace "no ka bari zan sanar da kai a right time" ya taɓe baki yace "okay!" Wayarshi ya ɗan danna kafin ya tashi yana kai wayar kunnensa sai kuma ya fita daga ɗakin yana sakin murmushin gefen baki. Cikin kwana biyun nan Hamdiyya ta kammala shirinta tsaf na tafiya ba tare da ta sanar da Mutallab ba,while a gefensa shima aiki ya sha masa kai bai cika zama garin ba ma wani lokaci sai dare yake dawowa gida,sanda zai shigo gidan kuma ta yi bacci,dan ita irin matan nan ne da babu ruwansu da miji sai lokacin da suka so. As they set out ranar Tuesday tun asubah Hamdiyya ta tashi ta gama shiri,around 6:30am Mummy Shafa'atu ta kirata taji kou ta tashi dan ta san halin ƴarta da shegen son jiki ba lallai tayi abunda ya kamata ba,Hamdiyya ta ɗauki wayarta dake vibrating saman bedside drawer,tayi answering call ɗin tana ƴar dariya tace "Mummy i'm awaken fa tun asubah" Mummy Shafa'atu tace "ina fatan kin gama shiri zuwa yanzu?" Hamdiyya tace "Mummy na shirya mana,7 nake jira yayi na fito" Mummy Shafa'atu tace "good.. Sai kin zo" tana ajiye wayar Mutallab da tun sanda wayar ya fara vibrating ya farka yace "ina za kije early morning? Da wa kike waya a irin lokacin nan?" Sosai maganarsa ya tsorata ta because batai zaton ya tashi ba,a rikice ta fara in'ina,ya ƙureta da kallo kafin ya tashi ya zauna yayi folding hannayensa a ƙirji yace "tambayarki nake Diya,ki sanar min gaskiyar abunda kike ɓoyemin kwanaki biyu da suka wuce" sunkuyar da kai tayi ta turo baki,lokaci ɗaya ta juya tace "babu komai" yace "okay! Tunda babu ki jira na shirya sai mu fita tare" saurin juyowa tayi ta kalleshi tace "wai baka yarda da ni bane?" Yace "not at all.. Idan babu abunda kike ɓoyewa ki bari na sauke ki office da kaina" daga haka yai shigewarsa bathroom,within 30 minutes ya gama shiryawa cikin Dasiki brown color,kansa da beret brown,sanda ya fito yayi knocking bedroom ɗinta kafin ya buɗe ƙofar,waya take da Mummy Shafa'atu cikin ɓacin rai tana sanar mata yanda Mutallab ya matsa sai ya sauketa office da kansa,and kamar yana zargin tana ɓoye masa wani abu ne shi yasa ya takura,uwar ta fara masifa tace ta san yanda za tayi ta gujewa fitar nasu tare mana ita kamar ba mace ba,Hamdiyya tace "wallahi Mummy yaƙi kawai zan bishi mu fito tare kafin ya sauke ni sai na turo Malam Ado yazo ya taho dake,sai ku ɗauke ni mu wuce" Mummy Shafa'atu tace "tou shi kenan.. Hakan ma dabara ne" suna yin sallama yana shigowa ɗakin,ya kalleta yana lullumshe idanuwansa,sam bai yarda da Hamdiyya ba cikin kwanakin nan,yace "muje kou kada mu makara" ta ɗauki hand bag ɗinta,dama she's ready tana sanye da riga da skirt na suite sai scalf da ta ɗaura kanta da baby hijab da tasa,suna saukowa sai da suka fara breakfast sannan suka fito yana gaba tana binsa a baya,Malam Ado ya kira ya bashi key yace "muje kou" a wani irin tsorace Hamdiyya ta dunga kallon Mutallab,ganin yana neman wargaza masu plan,cikin wani irin yanayi ta buɗe motar ta shiga haɗe da rufewa a fusace,Mutallab ya bita da kallo yayi wani murmushi sannan ya buɗe front seat ya shiga ya rufe. Gaba ɗaya Hamdiyya ta cika tai fam,wani irin takaicin Mutallab yau duk ya cika ta,duk AC dake aiki cikin motar taji iskar bai mata daɗi,a hankali ta kwantar da kanta jikin seat tana kallon hanya,ji take kamar za tai kuka saboda haushi,hanyar gidansu da Hamdiyya taga sun nufa yasa ta saurin tashi ta gyara zama tana ware idanunta,few minutes drive suka shigo cikin Wuse area,a bakin get ɗinsu Malam Ado yayi parking,Mutallab dake gaba ya kalleta ta mirror ganin yanda tai lokaci ɗaya,yace "ki kira Mom ta fito kada rana yayi mana" wani irin zaro idanuwa tayi surprisingly tace "ok.. Ok" ta ɗaga wayarta dake jikinta ta shiga kiran Mummy Shafa'atu jikinta na rawa,fuskarta tana bayyana tsananin farin cikin da take ciki,Mummy Shafa'atu ta ɗauki wayar tace "kin fita ne?" Hamdiyya tace "Mummy come out gamu bakin get" Mummy Shafa'atu tace "kin samu fita ne ke kaɗai ɗin?" Hamdiyya tace "Mummy hurry up please" daga haka ta katse wayarta tana sakin murmushi,not too long wata hamshaƙiyar mata ta fito get ɗin da suke tsaye bakinsa,irin manyan hajiyoyin nan na Abuja ne ta fito cikin wani ubansun super blue mai adon fari da baki,ta yafa vail a shoulders ɗinta fari da takalmi da jakarta suma farare masu tsadar gaske,sai ka rantse budurwa ce ko kuma irin zawarawan nan masu neman miji,tunda ta fito Hamdiyya ke kallonta tana murmushi,sanda ta ƙaraso ta buɗe back seat ta shiga,Hamdiyya ta kamo hannun uwar dake ɗauke da wasu manyan bangles biyu sai rings na gold ta ƙanƙame,da muryar excitement tace "good morning Mummy" Mummy Shafa'atu tayi mata murmushi ta amsa,Mutallab dake front seat ya ɗan waigo yana risinar da kai yace "good morning Mom" a mamakance ta amsa tana kallon Hamdiyya tai mata alama da ido da Mutallab,Hamdiyya ta lumshe mata idanu alamun kada ta damu,Mummy Shafa'atu taita kallon Hamdiyya dake wani irin blushing,ta kasa haƙura ta zungureta sai kuma ta ɗauki wayarta tai mata alamar ta duba wayar nata,duk abunda suke Mutallab is aware,amma baza ka taɓa cewa su yake kallo ba,Mummy Shafa'atu ta aika mata text ta waya tana tambayarta Mutallab da suka zo tare,here ta sanarwa uwar tare da shi za su je,amma abunda bata sani ba shi ne yanda aka yi ya sauko,Mummy Shafa'atu tai wani murmushi ta tura mata "ai na faɗa maki zan yi komai ta kama,saboda kada ya bamu matsala" Hamdiyya na murmusawa tace "that's My Mummy,i really love and proud of u" Mummy Shafa'atu ta tura mata "i love u more" daga nan kowa ta ajiye wayar suna kallon hanya da Malam Ado ya ɗauka ta barin garin Abuja. Throughout the journey from Abuja to Kano State sosai Hamdiyya ta gaji dan bata saba tafiya mai nisa a mota ba,sai dai da yake abune da tasa kanta har wani irin gaggawa take taji Malam Ado driver yace sun iso,Mummy Shafa'atu ma a gajiyen take sosai dan ko magana babu mai yi cikinsu,Hamdiyya kuwa kawai tana hango irin nasarar da za suyi ne idan aka dace suka samu yarinyar da za tai masu aikin,wannan sai yasa ta iya ɓoye gajiyarta ba kamar Mummy Shafa'atu ba,and shi kuma Malam Ado da yake ya saba dogon tafiyar and hanya ne da babu traffic,4 good hours and some minutes drive ya kawo su cikin Kano,sanda suka iso Zaria road ne suka ɗan ɗauki lokaci kafin su shigo cikin gari saboda traffic,manyan motoci da suke shigowa da kaya daga other states suka ɗan tare su,sanda suka samu hanya sannan suka wuce,ta ƙofar Mata da yake ta wuraren Sani Abatcha stadium suka biyo,nan da nan Malam Ado yayi parking ƙofar gidan,sannan ya kashe motar yana faɗin "alhmdllh.. Mun iso yallaɓai" Mutallab dake danna wayarsa yace "ok! Ka kira mutumin ka sanar masa.." Daga nan yai shiru bai sake cewa komai ba,Malam Ado ya amsa ya buɗe motar ya sauka,Mummy Shafa'atu ta bawa ƴarta hannu suka gaisa suna dariyar farin ciki,cikin soron gidan ya shiga ya kwaɗa sallama,Adija tana kitchen ta leƙo ta amsa,Malam Ado ya shigo tsakar gidan da akaiwa gyara sosai kamar ba gidan ba har paint sai da aka sake an ƙawatasa,idan ba ka yiwa farin sani bama za kace ba shi bane yana ɗan murmushi,zaro idanuwa Adija tayi tace "laaa! Baba Ado sannu da zuwa" Malam Ado ya kalleta yace "Baffan naku yana nan ne?" Adija ta girgiza kai,tace "a'a! Amma bai jima da fita ba,yace idan kun zo a kirashi" Malam Ado yace "tou tare muke da baƙi bari nai masu magana su shigo ciki kafin ya dawo" Adija tace "tou" sai lokacin ta gaishesa ya amsa yana sauri ya fita. Adija ta koma ɗakinsu da yasha sabbin furniture da ƙaton plasma TV ɗinsu,tsakiyar ɗakin an shimfiɗa sabon carpet da ya shiga da kayan ɗakin,sam baza kace wancan ɗakin nasu ne wannan ba,ta kalli su Ashey da suke kwance kowa da abunda take cikin sababbin wayoyinsu da Alh Sardauna ya siya masu,tace "ku tashi baƙin za su shigo" da sauri duk suka tashi Aalima ta shimfiɗa masu ƙaton sabon pray mat a gefe saman lafiyayyan marble da aka yiwa ɗakunan gidan,ta fito da ruwa da lemo masu sanyi daga fridge ɗinsu ta ajiye,dai² lokacin Malam Ado yayi sallama tare da su Hamdiyya da Mummy Shafa'atu,Adija dake tsakar gidan tana masu murmushi tai masu sannu da zuwa,suka amsa suna bin gidan da kallo,duk da ba wai gidan masu kuɗi bane kamar na Abuja,amma babu laifi gidan dan a share yake tsaf kuma babu wani abu da suka gani da yake ajiye ba'a muhallinsa ba,Adija tace "bismillah ku shigo" tai masu jagora zuwa ɗakinsu,suka bita a baya har cikin ɗakin,Aalima da Ashey da suke cikin ɗakin suka amsa sallamar da sukai suna masu sannu da zuwa,Mummy Shafa'atu ta amsa tana kallonsu,a ranta take faɗin babu laifi dukansu kyawawane babu wanda take da wani aibu,tayi ɗan murmushi tana tunanin abunda ya kawo su,idan aka dace ɗaya daga cikinsu ta kasance surrogate mother of her grandchild tana ganin baza'a samu matsala ba dan ta ga duk suna da hankali,food warmers sababbi cikin siyayyar da sukayo bayan an sallamo Fannah daga hospital Adija ta ɗauko ta zuba abinci dama Baffa ya sanar mata za'a yi baƙi ayi abinci da su,ta kira Aalima taje ta ɗauko masu ta kawo,abinci na musamman Baffa yasa aka shirya masu,da kuɗinsa yayi chefane ranar saboda kwaɗayin abubuwan da Malam Ado ya fara sanar masa ta waya though komai akwai cikin babban freezer ɗinsu,kullum ne sai Alh Sardauna yai masu aike,Mummy Shafa'atu sai sannu take masu tana kallon ɗakin dake cike da ƙamshi da sanyin AC. 1:30pm Fannah ta sauka napep a ƙofar gida,tana sanye da blue ɗin skirt da farin hijab da riga uniform ɗinta na Army day sababbi,fuskar nan yai fayau saboda ɗan zazzaɓin da tayi kwana biyu,ta bawa mai napep kuɗinsa ta juya tana goye da backpack baƙi da takalmi sneakers,tunda ta nufo ƙofar gidansu gabanta yake wani irin faɗuwa,ta kai hannu ta dafa zuciyarta bakinta na motsawa a hankali ta furta "laa ilaha illa anta subhanaka inniiy kuntu minaz'zalumiiyn.. A'uzhubikalimatillahit'tamaat min sharri maa khalaƙ.." Haka nan kwanakin take fama da faɗuwar gaba,tun kafin ma tai zazzaɓin nan,sam batai zaton da mutane a soron gidan ba,sai da ta shigo kanta tsaye,burki taci a tsakiya lokaci ɗaya ta ɗan zaro idanuwa sai kuma tayi sallama da ƴar siririyar Baby voice ɗinta,Malam Ado da Mutallab da suke soron suna jiran Baffa da yace gashi nan daga Bukavu Barrack suka amsa,fuskarta ta ɗan saki ta durƙusa tace "Baba Ado sannu da zuwa.. Ya hanya?" Yayi mata murmushi yace "a'a Fannah! Daga makaranta kike?" Ta gyaɗa masa kai ta gaisheshi,ya amsa yana kallon yanda ta sunkuyar da kanta,yace "tou ya karatu?" Tace "alhmdllh.." Bata kalli inda Mutallab yake ba tun sau ɗaya da ta kalleshi taji gabanta yayi wani irin faɗuwar da bai taɓa irinsa ba muryarta tana rawa tace "ina yini?" Ɗago kansa yayi jin Baby voice ɗinta dake ɗauke da wani irin nutsuwa ya bita da kallo lokacin har ta yunƙura ta tashi,side of her face kawai ya iya gani yace "lafiya lau.. How are u and studies?" Batai zaton zai amsa ba,tace "alhmdllh!" Daga haka ta wuce ta bar tsoron da ya cika da ƙamshinsa,sallama tayi cikin gidan lokacin Adija na ajiye ma su Mummy Shafa'atu buta da za suyi alwala saboda an fara kiran sallah,Adija ta amsa tace "kin dawo?" Fannah tace "Mmm!" Adija tace "sannu da dawowa.." Fannah ta amsa har za ta wuce ɗaki,Adija tace "zo ki miƙawa su Baba Ado ruwan alwala" Fannah tace "tou bari na kai jakata ɗaki" Adija tace "kawo na kai maki,ki kai masu sai ki dawo ki huta" Fannah tace "tou!" Ta sauke jakar dake bayanta ta ajiye sannan ta ɗauki buta biyun da Adija ta ajiye mata ta juya ta fita,sallama tayi masu kafin ta ajiye butar hannunta tace "Baba Ado ga ruwan alwala" yace "tou madallah.. Bari kam muyi sallah kafin ya ƙaraso" ita dai ta juya tai shigewarta ciki,ganin lokacin sallah ya yi yasa ta cire takalmi da farin socks ɗin ƙafarta ta ɗauki buta tai alwala,sannan ta shigo ɗakin da sallama,Aalima ta ɗago ta kalleta tana mata murmushi tace "student sannu da dawowa" Fannah ta kalleta da manyan idanuwanta tace "thank u" Ashey tace "sannu Auta.. Ya school?" Tace "alhmdllh.." Tsugunawa tayi tana kallon Mummy Shafa'atu,ganin babbar mace ce tace "ina yini?" Mummy Shafa'atu tayi mata murmushi tace "lafiya lau ƴanmata,ya karatu?" Fannah tace "alhmdllh" Mummy Shafa'atu tace "maa sha Allah.. Allah ya bada sa'a da ilimi mai amfani" Fannah ta amsa ta gaisar da Hamdiyya dake ta kallonta tana mata murmushi,ta amsa tace "ya sunanki?" Fannah ta kalleta tana ƙifta manyan idanuwanta tace "Fannah!" Hamdiyya tace "Wow! Nice name.. Kamar mai shi" Fannah ta ɗan yi murmushin yaƙe tace "thank u Maa" daga haka ta wuce wajen sabon press ɗinsu ta buɗe gurin kayanta,pray mat ta fito da shi sabo ta shimfiɗa,sanda tayi sallah sannan ta fita ta watsa ruwa,ta shigo ɗakin ta sake buɗe gefen kayanta,doguwar riga ta ciro arabian designer cikin siyayyar da Alh Sardauna yayi mata ta zuge zip ɗin rigar ta wajen wuya,sanda tasa sannan taja rigar tai ƙasa dashi ta zare towel ɗin da tai wanka,Mummy Shafa'atu dai sai kallonta take saboda kyaun Fannah da ta gani har tsoro yaso bata,Fannah na gama shiryawa ta kwashe uniform ɗinta tayi folding ɗinsu kamar ba'a sa ba ta zubasu laundry ɗinsu na kayan wanki,after ta gama ta juyo tana kallon Aalima tace "Yaa Aalima kun ci abinci?" Aalima dake chart tace "a'a ke muka tsaya jira ki dawo" kafin Fannah tayi magana Ashey dake kitchen tare da Adija suna maganar zubawa su Malam Ado abinci a kai masu ta ƙwalo mata kira,Fannah ta amsa sannan ta tashi ta fita,bakin kitchen ɗin ta tsaya dan bazai ɗaukesu dukansu ba saboda ƙanƙantarsa,Adija tace "su nawa ne a waje?" Fannah tace "su biyu ne" Adija ta kalli Ashey tace "zuba sai ki bata ta kai masu" Ashey tace "tou" ta shiga zuba abincin cikin wani sabon flask ɗin mai kyau,sanda ta gama ta ɗago ta kalli Fannah dake tsaye tace "tou a haka za ki fita ne?" Fannah ta girgiza mata kai sannan ta koma ɗaki ta ɗauko ƙaramin hijab,Ashey ta ɗauki nasu abincin da za su ci ta shigar masu da shi ɗaki,a hankali Fannah ta sunkuya ta ɗauki ƙaton silver tray ɗin da aka ɗaura abincin da za ta kaiwa su Mutallab ta fita,kafin ta shigo soron tai sallama,idanunta a ƙasa ta jira suka amsa sannan ta ƙarasa ta ajiye masu abincin ta juya cikin gida,lemo da ruwa masu sanyi ta ɗauko ta kawo masu sannan ta koma,tana shigowa ɗakin ta samu su Aalima suna jiranta ta zauna cikin da'irar da sukai tana sauke hijabin jikinta tasa hannu tai bismillah suka fara cin abincin. Ba'a ɗauki lokaci mai tsayi ba da shigowarta Baffa ya dawo,yayi sallama soron gidan da su Malam Ado suke zaune suna cin abinci shi da Mutallab da kamar ba ya gurin,da wani irin farin ciki ya kalli abokinsa yace "shegen sama.. Kana nan amma kamar baka garin nan" Malam Ado yayi dariya yace "tou gamu dai ka ganmu ai,ka san shigowa Kano yanzu akwai wahala" Baffa ya bashi hannu suka tafa,sannan suka gaisa suna taiwa juna shaƙiyanci,Malam Ado ya nuna masa Mutallab dake zaune yana jinsu yace "ga uban gidana baku gaisa ba" Baffa yayi dariya yace "Allah sarki.." Sai kuma ya kalli Mutallab suka gaisa a mutunce kafin ya tashi yace "bari na shiga na fito kafin ku gama" Malam Ado yace "tou babu laifi" Baffa ya barsu su gama cin abincin kafin suyi magana,dan Malam Ado ya fara masa maganar ta waya basu gama ba yace masa ma ya bari za su zo kawai suyi maganar face to face,bayan Baffa ya shiga gidan ya jima a ciki kafin ya dawo ya samu sun gama shi suke jira,ya zauna suka sake gaisawa yayi masu ya hanya,sanda Mutallab yake amsawa kansa a ƙasa sannan yace Malam Ado ya yiwa Baffa bayani bari ya ɗan basu guri,ya tashi yasa takalminsa ya fita ya tsaya jikin motar da suka zo da shi yana kallon unguwar,yana fita Malam Ado ya gyara zama ya fara yiwa Baffa bayani kamar yanda Mutallab yace,da irin aikin da suke son cikin ƴaƴansa tayi masu,ya sanar da shi komai sai dai bai fito ya faɗi actual aikin ba kai tsaye ya masa ƴan dabarun magana cikin hikima da azanci,bayan Baffa ya gama jin jawabin da suka zo masa da shi ya dunga kallon abokin nasa ya kasa cewa komai,Malam Ado yayi wani murmushi yace "ka bar kallona haka kasa yaran su zo,idan an dace zan maka cikakken jawabi da yaren da za ka fi fuskata" Baffa yace "wane yare kenan,kasan yare ɗaya nake ji duk duniya?" Malam Ado ya murza yatsunsa yace "yaren takarda.. Wanda za su wankeka daga dattin talauci,su kashe maka matsalolin shekaru rututu,sannan su fito da kai duniya ta sanka" dariya Baffa yayi yace "shegen bisa.. Inji kura" sannan ya tashi jikinsa har rawa yake jin maganar kuɗi yasa takalmi ya shiga cikin gida,Adija ya ƙwalawa kira ta fito lokacin basu jima sosai da gama cin abinci ba,yace ta biyosa soro suje ta amsa ta shiga ɗaki ta ɗauko hijab ɗinta,Mummy Shafa'atu ta kalli Hamdiyya cikin yin ƙasa da murya tace "tashi kije ayi komai a gaban idonki,kada a rufemu muna nan cikin gida.." Adija za su fita Hamdiyya ta fito ta biyosu,tare suka shigo soron Hamdiyya ta dunga kallon Mutallab da ya shigo sanda ya zauna ta tafi kusa da shi itama ta zauna,hankalinsa kaf yana kan waya Baffa ya gabatar masu da Adija,Mutallab ya taɓe baki bai ɗago ba,bayan ta koma Baffa ya kira Ashey da Aalima,amma duk da Mutallab ya kallesu sai yace basu yi masa yanda yake so ba,sanda Baffa ya gaji ya kalli Mutallab yace "yaro wai shin me kake dubawa ne? Kai dai ba wanda za tayi maka aiki kake nema ba?" Gyara zama Mutallab yayi yana shanye idanunsa halp open yace "haka ne amma ni ina da qualities da dole sai mai su nake so" Malam Ado da ya zuba idanu kawai ya kallesa yace "wasu irin qualities ne ranka ya daɗe? Ai tun farko da ka faɗo su,idan muna da wanda tayi dai² da ra'ayinka sai mu bayar" Mutallab yana gyara zama yace "firstly ina son mai nutsuwa da kyawawan ɗabi'u,wanda take da tsayuwa akan addini,i mean ta san every hukuncin Allah akanta,sannan sallah bai wuceta akan lokaci,and then wanda tafi duka waɗannan kyau.. Idan kuna da irin wannan ita nake nema" kallonsa kawai duk suka tsaya yi,Hamdiyya ta taɓashi tace "Honey a irin wannan unguwar za'a samu mai wannan halayen kuma? Wannan ai ko a FCT baza'a samu ba bare nan.." Bai kalleta ba yace "if suna da ni irinta kawai nake so,if babu sai muje mu nema a wani wuri" Hamdiyya ta fara masa dariya kamar taɓaɓɓiya tace "tou kai da ba aure za kayi ba ina ruwanka da duba duk waɗannan?" Ba tare da ya kalleta ba,yace "duk da haka ina son Surrogate mother of my kid ta zama mai ibada,saboda ya taso da kyawawan ɗabi'un da za'ayi alfahari da shi.." Malam Ado ne ya yiwa Baffa raɗa a kunne,da sauri Baffa ya kalleshi zai magana shi kuma ya ƙifta masa ido,duk abunda suke Mutallab na kallonsu yai shiru ne kawai bai ce komai ba,kafin Baffa yace komai Malam Ado yai zaraf yace "ai irin wannan ɗin ma muna da ita fiye ma da yanda ka faɗa,sai dai tunda ta fi sauran qualities za kayi ƙari akan abunda muka fara magana da Madam" Mutallab ya gyaɗa kai yace "ka faɗi nawa kake so price ɗin ya kasance" Baffa yana so ya tsayar da abokin nasa,da sauri shi kuma ya kama hannunsa yace "muna zuwa bari muyi shawara.." Da sauri suka fita soron gidan,can gefe suka tsaya suna kallon juna,Baffa yana tunanin maganar zuciyarsa tana rawa yace "wannan aikin naku anya babu haɗari cikinsa kuwa? Nifa auren Fannah nake shirin yi nan da ƴan watanni,na faɗa maka na karɓi kuɗin aurenta kwana biyu da suka wuce,yanzu haka da kake gani na babu kuɗin nan babu dalilinsu duk sun tafi.." Malam Ado yace "ka ga Malam Umar wannan duk ba abun damuwa bane,abune da dukanmu idan ya tabbata za muyi farin ciki,in badan ina sonka da alkhairi ba da sai na kaisu wani gurin daban,amma duk ba wannan ba tunda aiki ne za tayi da dawo,idan ta gama sai kai mata auren kaga ka ci ribar haihuwarta,ka jefo tsuntsaye biyu da dutse ɗaya a lokaci guda.. Idan ka amince da wannan tsarin wallahi riba zai kawo maka ƙazama ma kuwa,fiye da cacar da muka jima muna yi wanda kullum sai asara kawai muke tafkawa cikinta amma babu riba,tsayin shekaru muke asarar da abunda muka mallaka kuma har yanzu bamu fasa ba,amma wannan aikin da kake gani,su da suka zo gareka tamkar manoma ne da suke neman hayar gona za suyi shuka,da zaran ka amince masu sun watsa ɗan iri a gonar ƴarka,kai kuma za ka bada aron gonar ce na ƴan watanni,bayan nan da anyi girbi amfani ya fito shi kenan sai a sallameka,amma kayi tunanin maganata da kyau,idan kaso a yanzu za ka iya cewa su baka kafin alƙalami,in komai ya kammala a maka cikon kuɗin aiki.. Shi kenan ba sake ganinsu za kayi ba sun tafi kenan" Baffa yayi shiru yana tunani yace "kuma zai kai kamar nawa kuɗin da za su biya?" Malam Ado yace "duk da kuɗin da kaso su biyaka da shi,idan dala kake so za su biya ka da shi sai ka canjo,za su zama miliyoyin kuɗi,ka biya bashin dake kanka sannan kuma ka fita daga talauci,kai da shi kunyi fam³.." Baffa dai sai nazarin maganganun yake a ransa,Malam Ado ganin Baffa yai shiru yana girgiza kai yace "malam Umar da ace nine kai nake da ƴaƴa mata a yau,irin wannan damar yazo min,tofa ba zan ma tsaya tunani ba zan amince,saboda Allah ya kawon hutu nima,sai su fara biyana ribar ɗawainiyar da nayi da su tun suna yara,kuma ni idan nine a matsayin da kake tuni zan amince da wannan kasuwancin saboda ya fi zaman da suke ana ganinsu kullum zaune gida babu mashinshini,sannan ka ga kou ta nan ma ka yi maganin masu zaginka,da dai ace wani ya lalata maka yara,ya tafi ya barka da cizon yatsa,gara ace inda za ka samu riba da su ka aika su,kou ya kake gani?" Baffa ya gyaɗa kai cike da gamsuwa yace "kuma fa maganar ka gaskiya ce,tou yanzu ya kake ganin za muyi da su,nawa za su ƙara?" Malam Ado yace "su ƙara mana $10k ya zama $100k kenan" Baffa yace "tou muje mu sanar masu kada muyi sanya.." Shigowarsu cikin soron yasa Hamdiyya ɗaga kai ta kallesu,sanda suka zauna Malam Ado yana murmusawa yace "mun amince za mu baku irin wannan yarinyar amma za ku ƙara mana dala dubu goma" Hamdiyya ta kallesu da sauri tace "babu matsala za mu biya hakan" Baffa yayi murmushi yace "tou amma yanzu za ku fara bada kafin alƙalami,sauran ko a hankali ne sai ku biya" Hamdiyya tace "babu damuwa,ina yarinyar take ya ganta,kafin muzo tafiya da ita?" Baffa ya tashi jikinsa yana rawa ya ji maganar kuɗi yace "bari a kirata,ai yau ma sai ta shirya ku tafi" ya shiga cikin gidan da sauri yana ƙwala kiran "uwata! Ke Fannah!" Fitowa tayi daga ɗaki da sauri ta durƙusa ƙasa tace "ga ni Baffa" ya kalli ƴartasa yana murmushin farin ciki yace "zo muje" ta kalleshi tace "Baffa zan ɗauko hijabi" a wani irin fusace yace "biyo ni muje nace" babu musu tabi bayansa,Baffa ya kalli Hamdiyya yace "na san wannan dole za tayi maku" Mutallab da kansa ke ƙasa yana danna waya yana jinsu bai ɗago ba yace "Diya ki duba idan ta yi" Hamdiyya kallon Fannah kawai take da kanta ke ƙasa tana fidgeting fingers,tayi wani murmushi tace "Honey ai ni na ganta,kai dai kalleta idan ta yi yanda kake so" bai ɗago ba yace "alright!" Kama hannunsa Hamdiyya tayi tace "ka kalleta nace.. Ɗago kaga she's so cute and i like her tun zuwanmu" wani irin ɗago idanunsa yayi yana kallon Fannah tun daga kan feets ɗinta masu ɗauke da dogayen yatsu farare sol,sanda yayi sama da idanunsa a hankali ya kai wuraren ƙirjinta da take wasa da hannayenta a cikin scalf ɗin kanta data kunce tunda Baffa yayi mata tsawa duk ta kasa sakewa,sanda yabi lips ɗinta da suke wasu irin pinkish sai taunesu take alamunta ya nuna a tsorace take,gabansa yana faɗuwa ya kalli complete kyakkyawar fuskarta,though idanunta suna ƙasa half close,gashin da suke gaban goshinta mai ɗauke da black mark ɗinta na sallah da ya fito a farar fatarta da zara²n eyelashes ɗinta gami da girarenta da suke wasu irin light ba masu cika sosai ba kamar anyi curving ɗinsu sun ƙawata halittar ta na zamowa ƴa mace cikakkiyar musulma,duk kyaun Hamdiyya da yake gani sanda yake kallon Fannah though she's too young,amma hakan bai hana ya gane huge bambacin dake tsakanin su biyun ba,ɗauke idanunsa yayi saurin yi daga kanta yana lumshesu...

      #Mutallab ka zo da rainin hankali fa,me kake nufi da kalmominka ne,ehhh? 🙄 Malam kaida kace ba ka da tsarin mata biyu wannan duk tsarin da kake na mene ne?

           This book isn't for free,normal ₦300 posting 5 days excluding weekend,VIP ₦500 posting daily,SP VIP 1K all via 0060746882-Hauwa Muhammad Usman,access bank. Then u show ur evidence of payment via https://wa.me/+2348165726609. If u are willing to pay,my sister pay it now before the price will go up,after it is completed the price is ₦500.



#Follow
#Vote
#Comment
#Share fisabilillah!
#Asli Smasher.

CIWO A JIKIN WANI!Where stories live. Discover now