Mafari!

99 9 2
                                    

💠💠💠💠💠
©®AS-2022.






              *♡CIWO A JIKIN WANI¸.•💥*
                            '''(Kᴡᴀʀɪ)'''
                           



   *HAWWA__B__KUMO.*
     (Rᴇᴀʟ Sᴍᴀꜱʜᴇʀ).💕
*WATTPAD:@REAL-SMASHER.*
*AREWABOOKS:@REALSMASHER.*

     '''Iɴ ᴅᴇᴅɪᴄᴀᴛɪᴏɴ ᴛᴏ ᴍʏ ʟᴀᴛᴇ ᴅᴀᴅ Aʟʜ Mᴜʜᴀᴍᴍᴀᴅ Bᴀʙᴀ Usᴍᴀɴ (B–KUMO).'''

      '''Bᴇsᴛᴏᴡᴇᴅ ᴛᴏ Mʏ Zᴀʜʀᴀ Aʙᴅᴜʟʟ Tᴀғᴇᴇᴅᴀ (Nᴀ'ᴇᴇᴍᴀ).'''
••••••••••••••

*LAST FREE PAGE*

                               10

#Mafari!

            Zuciyarsa tana wani irin rawa,a hankali ya sauke wani ajiyar zuciya,fuskarsa ɗaure yace "mene ne sunanta?" Baffa ya kalli Fannah yace "faɗa masa sunanki ba da Hausa ba" cikin sanyin muryarta tace "my name is Fatimah Umar Farouk" yace "which class are u? Both islamiyya and modern education?" Da Baby voice ɗinta dake rawa tace "S.S 2 munyi qualifying,islamiyya mun yi sauka" yace "wasu littattafai kika sauke?" Tace "muna Risalah a fiqhu,Hadith muna Riyadhus'salihiiyn,sai Azkarun'nawawiiy,and Kitabut'tawuhiid" yace "duk wanda nace ki karanta za ki iya?" Ta gyaɗa kai a sanyaye tace "in sha Allah" duk yana danna wayarsa yake mata tambayoyin nan,Baffa ya kalli Mutallab yace "wannan da kake gani Hafizah ce,duk cikin ƴaƴana babu me iliminta,ta je musabaƙa babu adadi,sannan a islamiyyar da tayi har aji suka bata,saboda haka wannan duk tambayar da za kayi mata na tabbatar za ta amsa maka fiye da zatonka,ba na jinta in dai a nan ne" Mutallab was busy wayarsa a hannunsa ya ƙi ɗagowa amma duka yana jin me ake cewa,Hamdiyya jin yayi shiru tace "yarinyar nan fa ta yi Honey,ni tun zuwanmu ta shiga raina wallahi,kawai mu karɓeta tunda buƙatarmu zai biya a ƙarshe dai" bai kalleta ba itama ɗin yace "okay" gaban Fannah yana faɗuwa ta ɗago idanunta cike da hawaye ta kalli Baffa,magana take son yi amma ta kasa sai karkarwa jikinta yake,Baffa yayi murmushi bayan sun haɗa ido da Malam Ado abokinsa yace "alhamdulillahi!" Mutallab dai tun ok ɗin da yace bai kuma magana ba,Baffa yace "tou ya ake ciki? Ta yi makun za ku ɗauketa a hakan?" Hamdiyya ta kalli Mutallab ta kasa gane kansa tace "A.A kayi magana pleaseee" yanda tayi maganar yasa shi kallonta ta wutsiyar ido,yace "ta yi.. But" da sauri Hamdiyya tace "no honey tunda ta yi me muke jira,muyi yanda suka ce ɗin mu ɗauketa kawai mu tafi" Mutallab dai haka nan zuciyarsa ke rawa akan maganar yana jin kamar kada ya biyewa Hamdiyya,sanda ta damesa da wani irin shagwaɓa da magiya yace "it's ok Diya" Baffa yayi wani special hamdala shi da Malam Ado suka gaisa,Malam Ado yace "Congratulations mutumina" Baffa ya washe baki,sanda ya kalli Fannah dake share ƙwalla yace "shiga ciki ki haɗa kayanki maza da sauri" kuka ta fashe da shi tace "Baffa ina zanje?" Yace "wani ɗan aiki za kije kiyi masu da kin gama za ki dawo gida" cikin ƙoƙarin danne kukanta ta girgiza kai tace "ni dai ba na son zuwa ko ina" Baffa yace "haba yarinya ai aikin gama ya gama tunda na amince" daga haka ya tashi ya shiga cikin gidan,da kansa ya shiga har ɗakinsu yace ma Adija "ina kayan Fannah suke?" Adija jikinta a sanyaye tace "suna cikin press" Baffa ya wuce ya fara buɗewa yace "a ina suke?" Adija ta  faɗa masa,da kansa ya shiga haɗa ƴan kayanta a wani ƙaramin ghana must go da yaje ɗakinsa ya ɗauko,su Adija sai kallonsa suke sun kasa gane me Baffa yake shirin aikatawa,Aalima sai gunaguni take tunda suka ga Baffa ya shigo jikinsa yana rawa,sanda ya ɗauko kayan ya fito yace ma Mummy Shafa'atu "Hjy kizo za ku tafi" Mummy Shafa'atu ta tashi da sauri tace "tou madallah bari na fito mu kama hanya kada yamma ya riskemu hanya babu kyau yanzu.." Tunda Baffa ya fito da kayanta Fannah take kallonsa,da wani irin fuskar tausayi ta zube gwuiwoyinta ƙasa ta fara masa magiya da roƙonsa "dan Allah Baffa kayi haƙuri,ni ba na son zuwa ko ina,ka barni na gama makaranta ta please,Baffa kou ban gama ba na yarda kai min auren da kace,amma dan Allah Baffa kada kasa ni binsu" kuka sosai take mai cin rai,Mutallab da haka kawai yake jin kukanta yana taɓa masa zuciya ya tashi bai kalli Hamdiyya ba yace "idan kun gama ina jiranku a mota" ta gyaɗa masa kai sannan ta juya tana kallon Fannah tace "tashi mu tafi ƙanwata" wani irin gigitaccen ƙara Fannah ta fasa tana toshe kunnenta tace "ni bazan biku ba kuyi tafiyarku ku rabu dani,ni me na haɗa da ku za'a ce in biku,na sani ko kuna siyar da mutane ne" Mutallab dake ɗaura takalmi ƙafarsa ya kalli Malam Ado yace "muyi magana a waje idan babu damuwa" malam Ado jiki na rawa suka tashi suka bi Mutallab da har ya fita waje,Mutallab ya kallesu yace "maganar nan ina ganin kamar bazai yiwu ba,idan da matsala me zai hana baza'a haƙura ba?" Baffa yace "a'a babu wani matsala.. Kai dai ka biya kafin alƙalami ku ɗauketa ku tafi,kou bata so tunda ni da nake ubanta ina so ai dole tabi ku" duk yanda Mutallab yaso ya masu bayani ya fahimtar da su ƙin sauraransa sukai saboda hangen kuɗin da za'a biya,Mutallab ya sauke numfashi yace "shi kenan duk yanda kuka ce dai tunda ƴarku ce kun fini iko da ita" ya buɗe mota ta wajen dashboard ya cire rappers na dollars ƴan 1 hounded ya bawa Baffa,jikin Baffa har rawa yake ya karɓa yasa aljihu yace "tou sauran kuma sai aiki ya biya kou?" Mutallab yace "in sha Allah.. Idan kun gama da ita ina jiransu kada dare ya riskemu a hanya" Baffa yace "bari su fito ku tafi" ya juya yana kaɗa babbar riga ya nufi soron gidan nasa cikin wani irin farin cikin da tunda yake bai taɓa samun kansa a ciki ba. Baffa yana shigowa soron ya kalli Hamdiyya dake ta rarrashin Fannah yace "baiwar Allah tashi ki bamu wuri,bari nayi magana da ita" jikin Hamdiyya a mace tace "Baba kana ganin za ta yarda kuwa?" Ya gyaɗa mata kai cike da tabbatarwa yace "za ta amince" Hamdiyya ta tashi ta ɗauki tsadadden hand bag ɗinta na company Gucci tace "mun gode sosai Baba" tai masa sallama,tana fita Baffa ya kalli Fannah yace "uwata tashi muje.." Girgiza masa kai ta fara,cikin faɗa yace "ke mahaukaciya.. Idan kika bisu makaranta sai wanda kika zaɓa za su saki,kuma aikin da kika ji na ce idan kikai masu abunda suka saki maƙudan kuɗaɗe za su baki,sannan shi wannan mijin matar da take ta lallaɓaki shi zai aure ki,saboda kin fi matarsa kyau nesa ba kusa ba.." Kalmar data kuɓuce bakin Baffa yasa shi saurin yin shiru,kallonsa Fannah keyi da idanunta da sukai jaa saboda kuka tace "ni Baffa ba na son zuwa ko ina" wani kafirin tsawa yai mata yace "tashi nace don ubanki kafin kici na jaki" da sauri jikinta na rawa ta miƙe saboda tsoronsa da take ji,ya nuna mata ƙofa yace "maza ki bisu kuma idan naji wani abu saɓanin abunda na sanar maki kin san sauran.. Yanda ƴan uwanki suke ɗin nan haka kema kike so ki zame min ƙarfen ƙafa,bazan mori wahalar da nayi da ku ba? Maza wuce nace ki bisu" girgiza masa kai ta shiga yi tace "dan Allah Baffa kayi haƙuri" yace "wuce muje" babu musu ta fita soron gidan tana kuka tana waigen baya,Baffa ya ɗauki kayanta ya sakota a gaba har bakin motar inda Malam Ado suke tare da Hamdiyya dake masa magana,while Mutallab yana cikin motar ya lumshe idanunsa yai shiru yana tunani,Hamdiyya tana ganin fitowarsu ta saki fuska unlike lokacin da suke magana da Malam Ado,sanda suka ƙaraso da sauri ta kama hannun Fannah tana sakin murmushi tace "did she agreed?" Baffa yana dariya irin tasu ta ƴan duniya yace "ahau! Kuma dai ba ni na haifeta ba? Ku tafi kawai Allah ya tsare ya sauke ku lafiya" Malam Ado yayi wani dariya yace "komai naku na siyarwa ne" Baffa yayi murmushi yace "hatta rigar jikinmu kuwa ka gani ka taya muna iya kwaɓewa mu siyar maka" yana nufin komai ka gani zai iya sallama maka indai abun ya yima ya karɓi yan canjinsa yayi gaba,fizge hannunta Fannah tayi daga riƙon da Hamdiyyar tayi mata tana kuka tana kallon Baffa,Hamdiyya ta buɗe back seat tace "shiga za mu tafi" Fannah ta girgiza kai tana noƙe kafaɗa tana sake kallon Baffa,da Baffa yayi mata wani kallo bata san sanda tayi saurin shiga ba,ta zauna kusa da Mummy Shafa'atu tana matsar ƙwalla,sannan Hamdiyya ta shigo suka sa Fannah tsakiya,murna kamar zaisa Hamdiyya ta tashi sama,Baffa zaisa kayan Fannah a motar Hamdiyya ta kalli Ghana must go ɗin tace "Baba wannan fa?" Yace kayanta ne na sawa kada ku manta" Hamdiyya ta girgiza kai tace "a'a ka bayar da su kawai za'a siya mata wasu a can" Baffa yace "atoh! Shi kenan Allah ya saukeku lafiya ya tsare hanya" Hamdiyya ta amsa tana jin wani irin farin ciki yana zagaya jinin jikinta,Baffa ya rufe masu ƙofar ya matsa kusa da Malam Ado sukai ƙus² suka tafa sannan sukai sallama,Malam Ado ya shiga driver side yana ƙyaƙyata dariya ya tada motar,Baffa ya matsa gefe yana ɗaga masu hannu yace "tou Allah ya sauke ku lafiya,Ado sai ka shigo" Malam Ado yace "za muyi waya dai idan mun isa" Baffa yace "babu laifi" hawaye suna saukowa idon Fannah tace "ban yi sallama da su Yaa Aalima ba" Hamdiyya ta kalleta tace "ohh! Bari a kirasu sai kuyi sallama a gurguje kinga yanzu muna sauri ne kada dare yai mana,hanyar Abuja babu kyau kwanakin nan" ta sauke glasses ɗin gefenta ta kalli Baffa tace "Baba tana son yin sallama da su Aalima wai" Baffa ya kalli Fannah kamar zai zarota daga motar ya daketa yace "tou bari su fito suyi sallamar daga nan" ya koma cikin gida da sauri yana kaɗa babbar rigarsa,tun sanda su Baffa suka fita dukansu suka fito tsakar gida suka yi cirko²,Aalima kam kuka take ma tun bata kai ga jin abunda yake faruwa ba,ganin yanda Baffa ya ɗauki kayan Fannah ya tabbatar masu da lallai wani wajen za'a tafi da ita,Baffa yana shigowa yace "kuzo maza kuyi sallama da su" kamar masu jira suka biyoshi da sauri,ta kusa da gefen Hamdiyya duk suka tsaya Fannah ta ɗago tana kallon Aalima da su Adija tace "Yaa Adija dan Allah kice da Baffa ya barni a gurinku,ni ba na son binsu,na yarda yai min auren da yace,amma dan Allah kada ya rabani da ku,pleaseee" Adija ta juya ta kalli Baffa hawaye suna cika mata idanu tace "Baffa ina za'a tafi da ita?" Yace "aiki za ta je idan ta gama za ta dawo" Adija tace "yaushe? Wane irin aiki ne Baffa? Me yasa sai Fannah? Madadin ka turani ko Ashey ko Aalima.." Tsawa Baffa yayi mata yace "kuyi sallama za su tafi,ba abunda na kirawoku kuyi ba kenan ku tsare ni da tambayoyi" Aalima tana kallon Fannah tace "little i'm gonna missed u" Fannah ta sake fashewa da kuka tace "Yaa Aalima dan Allah ku roƙi Baffa ya barni tare da ku" Baffa ya kallesu ganin za su dama masa lissafi yace "tou maza ku wuce ku koma gida sai na shigo" yanda yake kaɗa su kamar awakai duka suka juya Ashey kam ta kasa ma magana jikinta sai rawa yake,suna waigen Fannah dake kuka itama tana kallonsu har suka shiga soron gidansu,Baffa ya matsa yana yiwa su Hamdiyya addu'ar sauka lafiya,yana tsaye gurin sai da Malam Ado ya juya kan motar suka nufi hanyar fita daga line sannan ya juya ya nufi gida yana murmusawa,Fannah tana ganin sun fita line gidansu ta kifa kanta tsakanin cinyoyinta ta sake fashewa da wani irin kuka mai ban tausayi,kaf cikin motar Hamdiyya kawai ta iya daurewa ta fara lallashinta,Mummy Shafa'atu kam taɓe baki tayi tace "za ki gaji ki bari,dan na ga alama tunda mahaifinki ya karɓi kwangilar nan,ba zai taɓa dawo da kuɗin aikin ba" Mutallab dai yana gaba bai ko ce uffan ba,sanda suka ɗauki hanya suna ta sharar gudu kan coalter,a hankali sanda kanta ya fara ciwo ta gaji tai shiru dan kanta tana sauke ajiyar zuciya,tunda suka fara wuce ƙauyukan dake wajen Kano,kafin ma suyi nisa sosai wani irin bacci ya fara ɗaukanta,Malam Ado kam ko tari baiba shima gudu kawai yake akan titi yana murmusawa,tafiyar awanni sukai wanda har lokacin Fannah bata san me ake ba tana bacci,sanda suka shigo FTC Abuja guraren maghreeb ne,sanda suka fara biyawa Wuse suka sauke Mummy Shafa'atu a gida,ta sauka bakin get tana faɗin "wash! Maa sha Allah,har mun iso gida" tana kallon Hamdiyya tace "tou Allah ya huta gajiya sai mun yi waya?" Hamdiyya tace "sure Mummy" taiwa su Mutallab sallama ta wuce gidanta,daga nan su kuma suka juya kan mota suka nufi LAKE VIEW (Jabi). Kuka sosai Aalima keyi da su Ashey tunda suka shiga gidan,ba'a jima ba wayar dake aje saman bed ƙiran 14 pro Max ya ɗauki beeping,kira sai shigowa yake da ya katse sai wani ya sake shigowa,can kuma ya fara haske alamun message,ganin wayar Fannah ne data tashi ta bari ta fita kiran Baffa ke beeping,yasa Aalima ta ƙarasa gurin ta kai hannu ta ɗauka lokacin ana sake kira,wani irin kuka ne ya zo mata ganin me kiran,gaba ɗaya jikinta yai sanyi ta kasa ɗauka,kusan missed calls 20 aka yi,kafin Adija ta share hawaye ta kalli Aalima tace "wai waye ne yake ta kira?" Aalima tana fashewa da kuka sosai tace "shi ne yake kiranta.." Adija tace "shi wa?" Aalima tace "Alh Sardauna.." Share idonta Adija tayi sosai sannan tace "ba ni wayar" ta karɓa tayi answering call ɗin dake daf da tsinkewa,wani ajiyar zuciya Alh Sardauna yayi yace "Autar mata kina wahalar da wannan bawan Allan fa,ina kika shiga tun ɗazu nake ta kira no response.. Mmm?" Adija ta runtse idanuwanta maganarta a sanyaye tace "ba ita bace Adija ce" wani iri gyara zama Alh Sardauna yayi dake cikin office ɗinsa yace "where's she? Ina fatan lafiya lau take babu abunda yake faruwa?" Adija ta sauke bayyanannen ajiyar zuciya tace "it's a long story amma idan da yanda za ayi ina zan zo na sameka saboda ba na son kazo gida yau akwai matsala" jikinsa a sanyaye zuciyarsa na wani irin tsinkewa yace "ok! Bari na turo maki text na address ɗin inda za ki same ni" Adija tace "tou.. Na gode sosai" daga haka tai saurin katse wayar jiyo shigowar Baffa gidan yana waƙe² kamar yanda ya saba. A hankali Fannah ta dunga buɗe idanunta tana kallon hanya da manyan gine²n Abuja,titunan garin kawai sun bambanta da na Kano,wara manyan idanuwanta ta dunga yi har lokacin bata bar sauke ajiyar zuciya ba,sanda suka shigo estate ɗinsu Hamdiyya tayi wani murmushi tana kallon Fannah da ta ƙi sakewa,dai² bakin get Malam Ado yayi horn military officers da suke gadin gidan suka buɗe masu suna masu barka da zuwa,ya ƙarasa ƙasan manyan tent dake ɗauke da manyan motoci yayi parking,kafin kowa ya fita Mutallab ya buɗe motar ya sauka sannan Hamdiyya da aka buɗewa mota,ta kalli Fannah tace "sauko muje" wani irin dame fuska Fannah tayi za tayi kuka kuka ta ƙi saukowa motar,Hamdiyya ta koma cikin motar tana kallonta,lallashi na sosai ta dunga mata,kafin ta samu ta sauko tana share hawaye,suka fito suka wuce zuwa main entrance,garin har ya fara duhu dan tuni aka idar da sallah a masallaci. Tunda suka shigo cikin gidan take raɓe² ta ƙi sakin jikinta,Mutallab kam tunda ya shiga bai zauna downstairs ba,yai wucewarsa upstairs gabansa na wani irin faɗuwa,sam ya rasa cikakkiyar nutsuwar zuciya akan al'amarin nan,sanda ya shiga bedroom ɗinsa kayan jikinsa ya rage ya shiga ya watsa ruwa,yana fitowa jallabiya ya saka mai short hard ya kabbarta sallah,after ya idar ya zauna yai shiru yana tunani. Baffa ne ya ƙwalo ma Adija da su Ashey kira,suka fito tsakar gidan sukai masa cirko²,ya kallesu yana dariya sosai dake nuna yana cikin farin ciki yace "yaro² ne! Yanzu saboda abunda ya faru kukai min tsaye a kai baza ku tsuguna ba?" Adija ta ɗauke kai tace "Baffa ai ko me ya faru kai ka siya da kuɗin ka" ya kalleta da kyau yace "tou uwata! Me na yi?" Hawaye suna sauka idonta tace "Baffa duk ba wannan maganar ba,ni yanzu kawai ina son sanin inda aka tafi da Fannah! Sannan wane irin aiki za ta yiwa mutanen da ka haɗata da su? Na kasa gane mene ne manufar abunda kake mana,tun muna ƴan ƙanana har zuwa yau kullum da irin ƙalubanen da muke fuskanta,Baffa wace irin rayuwa kake so muyi ne? Me yasa sai Fannah? Bayan ka yi alƙawarin aurenta da wani sannan ka ɗauketa ka bawa wasu,me haka yake nufi dan Allah? Ka san illar saɓa alƙawari kuwa? Me yasa haka Baffa? Mutanen nan fa baka sansu ba suma basu sanka ba,kawai daga haɗuwa yau ka ɗauketa ka damƙa masu ita,sun tafi da ita idan siyar da ita suke da niyyar yi fa? Yanda duniya babu gaskiya ko da basu siyar da ita ba suka lalata mata rayuwa,me za kace da Allah lokacin da ka tsinci kanka gaba gareshi? Da wane ido za ka kalli Fannah saboda Allah? Shi kenan dan bamu san kowa a dangin mahaifiyarmu ba sai abu yaita faruwa da mu muna shanyewa,muma fa halittarmu akai,me yasa za ka ɗauke mu tamkar wata baƙar ƙaddara? Dan mun zo a ƴaƴa mata ko dan me? Shi yasa kake kallonmu a matsayin wahala? Shi kenan Baffa duk yanda kaso kayi da mu,na tabbata yau ko lalacewa muka yi bamu da hakki,laifin duk yana wuyanka tunda kai ne mahaifinmu,baka kula da mu yanda ya dace ba,da ka tarbiyyantar da mu kamar yanda addini yace baza mu sauka daga hanyar gaskiya ba,amma kayi tunanin maganata.." Ashey da Aalima duk kuka suke kamar me,Ashey tana shanye kukanta ta sunkuyar da kanta ƙasa tace "Baffa ni dai dan Allah tambayarka kawai zan yi,ka sanar da mu inda dangin mahaifiyarmu suke,za mu nemesu tunda mun zame maka masifa,gara mu tafi inda za'a iya riƙemu akula da mu,mu mata ne bai kamata ace rayuwarmu ya kasance a haka ba,dan komai yana iya samunmu.." Dariya Baffa yayi kafin ya kalli Aalima yace "kema kina da tambayar ne ko baki da ita?" Aalima ta gyaɗa kai da sauri hawaye suna zuba idonta tace "dan Allah Baffa kafin rayuwar Fannah ya lalace ka yi magana da mutanen da suka tafi da ita su dawo mana da ita,gara kai mata aure kamar yanda ka faɗa da dai abunda zai faru da ita" Baffa ya kaɗa babbar rigarsa yana kallonsu duka yace "idan kun gama tou duk ku shiga ku fara haɗa kayanku dan za mu bar unguwar nan cikin satin nan in Allah ya kaimu" wani irin kallonsa suka dunga yi,Adija tace "zuwa ina Baffa?" Baffa yace "duk inda Allah ya nufa" Adija tace "Fannah kuma fa Baffa?" Baffa yace "ke ki saurareni da kyau,idan na sake magana kika mayarmin zan daka ki yanzun nan,ni sa'anki ne da zabki tutsiye ni da tambayoyi kamar kin haifeni?" Adija tayi wani murmushi mai ciwo cikin ɗaga murya tace "Baffa kayi haƙuri amma gaskiya bazan bika ba untill na san inda aka kai Fannah" Ashey da Aalima ma suna haɗa baki suka ce "muma babu inda za mu har sai mun san inda ƴar uwarmu take" Baffa ya kallesu cikin takaici yace "tou kuwa baku isa ba dan ni na haifeku ba ku kuka haifeni ba,idan kun ga dama ku shirya mu bar unguwar nan,idan kuma kun zaɓi zaman nan ne tou duk abunda zai faru babu ruwana,dan idan kun zauna ma babu abunda zai canja.. Auren da kuke son yi babu wanda zai bari ɗansa ya aureku indai a irin wannan unguwar ce" kallon juna suka yi suna haɗa baki suka ce "Baffa saboda me?" Yace "za ku bini mu tafi ne ko kuwa?" Adija tace "me yasa baza mu auru ba Baffa? Dan Allah kai mana bayani" Baffa ya juya ya nufi cikin ɗakinsa da sauri yace "ku haɗa inaku² mu bar unguwar nan faƙat" duk yanda suka so yayi masu bayani ƙi Baffa yayi ya shige ɗakinsa yana waƙa abunsa,ya ƙi sauraronsu ƙarshen ma ficewa yayi ya bar masu gidan su ci kansu,dole suka fara yin yanda yace,amma sam babu mai nutsuwar zuciya,tunanin maganganunsa kawai suke suna jujjuyasu a rai. Vibrating ɗin da wayar Fannah yayi yasa Adija saurin ɗauka ta shiga duba address ɗin da ya turo mata,da sauri ta kalli Aalima tace "tashi ki rakani muje muyi sauri mu dawo" Aalima tace "ina za muje Yaa Adija?" Adija tace "ke dai yi sauri kafin Baffa ya dawo" Aalima ta tashi ta fita ta wanke fuskarta,kafin ta shigo Adija ta ɗauki hijab ɗin Fannah har ƙasa da niƙaf,ta ɗaura fuskarta Aalima ma ta ɗauko hijab da niƙaf tasa sannan suka fito gidan Ashey tana tambayarsu ina za suje Adija tace "zan miki bayani idan mun dawo ki kula da kanki" Ashey tace "tou" suna fita titi Adija ta tsare masu napep tace "Ni'ima guest palace" mai napep yace "tou bismillah" suka shiga yaja sai kiɗa ke tashi cikin napep ɗin,har suka iso bakin hotel ɗin babu mai magana,Aalima jikinta a sanyaye bayan sun sauka Adija ta bawa mai napep kuɗinsa ta kalli Adija tace "Yaa Adija hotel fa muka zo" Adija tayi mata wani kallo tace "sai me tou dan mun zo hotel? Dalla biyoni muje ni" ta wuce ta shiga get ɗin,duk da yamma ne amma harabar hotel ɗin cike yake sosai da manyan motoci,Aalima dai bin Adija kawai take tana buɗa idanunta gabanta na faɗuwa,lokaci ɗaya suka tsaya jikin wani mota Adija ta shiga kiran number Alh Sardauna,ya ɗauka yace "kin zo ne?" Adija tace "ehh muna gurin da ake parking" yace "alright! Ki jirani a nan bari na fito na taho dake" Adija tace "tou amma mu biyu ne za ka ganmu da hijab da niƙab" yace "alright! Mu biyu ne amma,za ka ganmu tsaye da hijab" ta sanar masa yanda zai saurin gane su sannan ta katse wayar,Aalima dai bata nutsu ba har sannan sai kallon mutane take a gurin da suke kallonsu,sunga baƙon abu mata a hotel kuma wai da hijab da niƙab,bai jima ba sosai ya fito cikin wani irin ɗanyen shadda,babban mutum ne sosai dan duk cikinsu babu wanda bai haifa ba,Adija ta amsa sallamar da yayi masu sannan ta gaisheshi,yana murmusawa ya kallesu yace "wannan irin shigar fa haka" Adija tace "ai ka ga bamu saba zuwa irin gurin nan ba,yauma kasada muka ɗauka amma mu da bamu fi ƙarfin zagin mutanen unguwa ba aka ganmu a nan kuma ai bamu san me zai faru ba" yace "haka ne.. Muje tou kada kuyi ta tsayuwa a nan" Adija tace "alright!" Tiryan² suka bishi har room ɗin dake can wani surƙuƙi a VIP,suna shiga Adija ta ɗaga niƙaf ɗin fuskarta ta zauna saman sofa,Aalima ma ta zauna kusa da ita tana sauke nata niƙaf ɗin,Alh Sardauna ya zauna bakin gadon ɗakin yace "me za'a kawo maku?" Adija ta girgiza kai tace "a'a mun gode sauri muke ai,dama magana kawai nazo muyi na sanar maka abunda ke faruwa" yace "okay! Duk da haka bari a kawo maku drinks" ita dai bata ce komai ba har ya kira reception ya bada order abunda za'a kawo masu,yana ajiye wayar ya kalli Adija yace "ina sauraren ki" nan Adija ta gyara zama ta shiga feɗe masa biri har wutsiya,Alh Sardauna kallonta kawai yake mamaki ya cikasa,shi Harkas zai wa haka? Kamarsa zai cuta? Yayi wani murmushi yana kallonsu yace "okay! Babu damuwa na gode sosai Adija da kika sanar da ni,yanzu ita Fannah baku san inda aka tafi da ita ba kenan?" Adija tace "wallahi hankalina ya ƙi kwanciya saboda rashin sanin takaimaman abunda Baffa yake shiryawa" Alh Sardauna yace "babu komai.. Yanzu ku koma gida,zanyi magana da Baffan naku in sha Allah" Adija tace "ka rufa mana asiri dan Allah kada ka faɗa masa mu muka sanar maka" Alh Adam yayi mata murmushi yace "kada ki damu bazai taɓa sani ba in sha Allah.. Na yi maku alƙawari" Adija ta sauke ajiyar zuciya tace "mun gode sosai.." Sanda ta kalli Aalima tace "tashi mu tafi mun bar Ashey ita kaɗai a gida" Aalima ta tashi tana kokawar ɗaura niƙaf ɗinta tace "sai an jima" ya amsa su yana tashi tsaye yace "muje na sauke ku a gida" tare suka fito a hanya ya gamu da receptionist ɗin da zai kawo order da yayi masu ya kalleshi yace "ka mayar a yi packaging ɗin shi da sauri tafiya za su yi" ya amsa ya juya su kuma suka nufi hanyar fita,a hanya wani Babban Alh sai kallonsu yake Aalima ta kalleshi yanda yake tafiya da ƙyar saboda ƙiba tayi siririn tsaki tana ƙananan mita ta cikin niƙaf ɗinta,suna fitowa suka tsaya inda suka fara tsaiwa da suka zo,sanda receptionist ɗin ya dawo da leda a hannunsa,Alh Sardauna ya karɓa ya miƙawa Aalima,tasa hannu biyu ta karɓa sannan ya buɗe motarsa yace "ku shiga muje" babu musu suka shiga,Adija a front Aalima kuma tana baya,har suka iso Zango babu mai magana sai da suka sauka bakin titi,ya zaro sababbin ƴan 1k masu ɗan yawa dan bai ƙirga ba ya miƙawa Adija yana dariyar tsokana yace "Adija ga wannan babu yawa,na san Aalima baza ta karɓa ba" Aalima tayi dariya ta sauka motar tace "sai an jima" yayi dariya shima yace "na gode sosai,a gaida Ashey" Adija ta karɓa tace "mun gode" sannan ta sauka motar ta rufe masa,suna tafiya yaja motar da wani mahaukaci gudu zuwa majalisarsu zuciyarsa na tafasa...


        '''#Me zai faru a haɗuwar Baffa da Alh Adam Sardauna ne? Yaya rayuwar Fannah zai kasance a FCT? Shin Mutallab zai amince ayi Surrogacy ɗin nan ko kuma dai zai canja shawara? Wane ne daga cikin mutum uku zai nasarar aure Fannah? Kuna ganin Yusuf zai dawo? Yaya rayuwar su Aalima zai kasance ɓacewar Fannah? Ina labarin Maama Fandi da Abbor? Wace duniya Sanda ya shiga zuwa lokacin nan? Me Baffa yake ɓoyewa su Adija ne? Ina danginsu na uwa da uba? Mene ne alaƙar ɓangarorin nan uku?  Duka za ku samu amsoshin tambayoyinku nan gaba idan Allah ya amince,mu haɗe da ku a paid group habiiybaatiiy.  ‍🔥رومانسيه of a special kind awaits u in this novel of CIWO A JIKIN WANI.. Don't missed it out ki biya naki kada ayi babu ke dan yanzu za'a fara wasan...'''


         #Alhamdulillah! I'm done with free part,kamar yadda nasan sauran novels ɗina suna fita,wannan ma will go round as usual and i can't prevent that,but if u should come across it it's not for free,ki biya kafin ki karanta please,ba zan yi maku Allah ya isa akai ba,normal ₦300 posting 5 days excluding weekend,VIP ₦500 posting daily,SP VIP 1K all via 0060746882-Hauwa Muhammad Usman,access bank. Then u show ur evidence of payment via https://wa.me/+2348165726609. If u are willing to pay,my sister pay it now before the price will go up,after it is completed the price is ₦500.





#Follow
#Vote
#Comment
#Share fisabilillah!
#Asli Smasher.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Oct 05, 2022 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

CIWO A JIKIN WANI!Where stories live. Discover now