Munafukin_zama

66 7 4
                                    

💠💠💠💠💠
©®AS-2022.






              *♡CIWO A JIKIN WANI¸.•💥*
                            '''(Kᴡᴀʀɪ)'''
                           



   *HAWWA__B__KUMO.*
     (Rᴇᴀʟ Sᴍᴀꜱʜᴇʀ).💕
*WATTPAD:@REAL-SMASHER.*
*AREWABOOKS:@REALSMASHER.*

     '''Iɴ ᴅᴇᴅɪᴄᴀᴛɪᴏɴ ᴛᴏ ᴍʏ ʟᴀᴛᴇ ᴅᴀᴅ Aʟʜ Mᴜʜᴀᴍᴍᴀᴅ Bᴀʙᴀ Usᴍᴀɴ (B–KUMO)'''
••••••••••••••
   '''Masu buƙatar a tallata hajarsu u should contact me ta number na,kou kuyi magana kai tsaye ta https://wa.me/+2348165726609.'''

                               02

#Munafukin_zama

            Bacci take amma sam babu nutsuwa ko sukuni tattare da ita,sosai gabanta ke sake yankewa yana faɗuwa a cikin bacci cike da wasu irin matarkai marasa kan gado,sanda ƴan rakiyar amarya suka shigo gidan wasu danginta suna ta shewa da waƙe irin na mutanen da,wasu kuma suna ɗaga murya suna cewa "tou gafararku dai masu gida.. Amarya Allah ya nufa,alƙawari tsakanin Zannah da Ruqayya,maƙi gani Allah ya kawar da shi kou da uwarsa ce" maganganu dai na rashin mutunci da ɗiban albarka haka sukaita fama,har suka shigo cikin gidan inda su Yagana suke tsaitsaye suna masu barka da zuwa,few suka amsa suma tsofaffin da suka shigo da ita ne,sauran kam sai kallon banza da ganin basu isa ba har suka kai amarya ɗakinta babu maganar a kaita gurin uwar gida a gaisa duk da tana cikin gidan,Yagana ta riƙe baki tana kallon ikon Allah,wata matar Ƙanin Babansu Fandi irin bakatsinan nan ce ta taɓe baki tace "Yagana anya za'a yi zaman lafiya kuwa a gidan nan?" Yagana tace "muna fatan haka Mama Kubra" Mama Kubra tace "gaskiya banga alama ba,tabbas Zannah ya ɗebo ruwan dafa kansa,Allah dai ya tsare Fandi,ita da ba hayaniya ta iya ba ko a gida.." Yagana dai murmushi kawai tayi bata sake cewa komai ba suka koma ɗakin da kujerun Fandi suke suka zauna suna ɗan hirar abunda ya faru. Lokacin da ƴan kawo amarya suka kaita ɗakinta,tsofaffin da suka tarar masu jere suka ce ba haka ake ba,su suka sa akai Ruqayya gurin su Yagana,sukai sallama parlon da Yagana suke,sanda suka shiga wata ƙanwar Baban Ruqayya tace "kuyi haƙuri dan Allah ba'a fara kawota kun gaisa ba" Mama Kubra tace "a'a babu komai hakan ma" aka gaisa suke tambayar "ina uwar gidan Zannah?" Yagana da ta gama ɗaukar cikinsu tace "eyyahh! Bata jin daɗi ne yanzun nan ta samu bacci taita jiran isowarku,tou da baku zo ba ciwo yana neman kayar da ita nace ta samu ta kwanta ai muma idan aka ganmu kamar an ganta ne,kuma abu ma dai da zasu zauna gida ɗaya" tsohuwar tace "kayyade! Allah ya bata lafiya" Yagana ta nuna masu Sanda da Abbor da suke cikin ɗakin tace "ga ƴaƴanta nan dai" ta ƙasan mayafi Ruqayya ta kirasu,tace "wane ne Sanda a cikinku?" Abbor ya nuna ƙaninsa,ta kalleshi tace "kai ne Abbor kou?" Yace "Ehh nine" yanda ta ɗaura Sanda akan cinyarta sai duk wanda suke ɗakin jikinsu yayi sanyi,bayan su Yagana sun karɓi amanar Ruqayya da ƙanwar Babanta ta basu tare da cewa "dan Allah ku kula da ita idan kunga tayi wani abu ba dai² ba ku gyara mata,bata da kowa garin nan banda Zannah sai kou Fandi dake abokiyar zamanta" su Yagana suka ce "babu komai ai an zama ɗaya in sha Allah" daga nan suka mayar da Ruqayya ɗakinta bayan sun ƙara yi mata nasiha sannan sukai mata sallama dan a lokacin za su juya,duka basu wuce mintuna ba suka yi sallama da su Yagana suka tafi,gidan ya rage su Yagana kawai,suna ta ɗan ƙus² ɗin yanda wasu cikin ƴan uwan amaryar sukaita kallonsu ɗai² badan da tsofaffin bama da babu wanda za suyi gaisawar mutunci da shi,dangin Ruqayya suna tafiya kuwa suma suka fara shirin tafiya dan maghreeb ta kawo jiki,bayan sun gyara gidan sun sa turare irin nasu na mutanen Kanuri mai matuƙar kyau,Yagana ta shiga ta tashi Fandi dake bacci tace "tou mu za mu tafi kina ta bacci,har ƴan kawo amarya sun zo sun tafi" da sauri ta sauko saman sabon gadonta da Zannah ya sake mata duk cikin kyautatawar yanda ta sauko da wuri,ta biyo Yagana sukai sallama da ƴan uwanta tana tai masu godiyar yanda suka gyara gidan,kamar kada su tafi a haka dai suka wuce,gida ya rage daga ita sai ƴaƴanta da tasa a ɗaki sukai sallah tare,tana ta sauraren surutunsu da ba fahimtar me suke cewa take ba,kamar jira Zannah yake ana yin ishaa ya shigo gidan sanda ya fara shigowa ɗakinta ta ɗaga kai ta kalleshi ya shigo bakinsa ya ƙi rufuwa kana kallonsa ka ga ango,ya ajiye mata ledar kajin da ya shigo da shi,ko zama baiba yace "bari na leƙa gurin ƙanwarki na dawo" tace "a fito lafiya" tunda ya fita ɗakin Fandi bata ƙara ganinsa ba sai washe gari da safe kusan ƙarfe taran safe tana kitchen ta gama haɗa breakfast tana cikin adonta kamar kullum duk da dai ta rame amma sosai tai kyau,ƙananun 2 step kitson kanta sun sauka bayanta,da sallama ya shigo kitchen ɗin ta amsa ta daure ta saki fuskarta ta gaisheshi,ya amsa yana kallonta cike da ɗan jin nauyin yanda bai koma ba da dare yace "kiyi haƙuri jiya ban dawo ba kuma" tace "babu komai.. Ga breakfast ɗinku" yace "mun gode.. Amma da ruwan zafi kika bani nayi wanka,banyi sallar asuba ba har yanzu" kallonsa ta ɗaga kai ta dunga yi da mamaki,tsayin zamanta da Zannah bai taɓa barin sallah ta wuce shi akan lokaci ba sai yau,bata dai ce masa komai ba ta ɗora masa ruwan,ta ɗauki abincin yaranta ta fita,a gaba tasa su suka ci tare,bayan sun gama ta fita da komai,sanda tayi wanke² ta fara shirin ɗora lunch,lokacin sai ga Ruqayya ta fito da fara'a a fuskarta ta gaisheta,babu laifi itama fara ce sai dai bata kai Fandi kyau ba,bayan sun gaisa take tambayar su Sanda,Fandi tai murmushi tace "ga su can suna wasa a ɗaki" Ruqayya tayi murmushi tace "me zan tayaki?" Fandi ta girgiza kai tana murmusawa tace "a'a wallahi kije ki huta,ai amarya bata aiki" duk yanda taso hana Ruqayya tayata aikin nan bata fasa ba,sai da ta kama mata suna yi suna ɗan hira sama²,duka kuma kusan tambayarta Ruqayya keyi,bayan sun gama ma bin Fandi tayi parlonta tana ta hira da su Sanda tana masu tambaya akan makaranta,abu ɗaya data fahimta yaran dukansu akwai ƙwaƙwalwa dan duk tambayar da za tayi masu sai sun bata amsa, wannan dalilin yasa Zannah yake mugun son su musamman Sanda da komai Zannah zai magana akai indai ya shafi rayuwarsa da iyalinsa zai wahala bai maganar sa ba,a haka Zannah da ya fita gurin aiki ya dawo ya samesu kasancewarsa ma'aikacin gwamnati,shi kansa ya ji daɗin yanda ya tarar da su zaune though ba hira suke ba,amma yanda yaga Ruqayya tana jan ƴaƴansa a jiki abun yai masa daɗi,nan ya zauna shima suka ci gaba da hiran tare. Kullum tunda aka kawo Ruqayya Fandi ke yin girkin safe,rana da dare kuma tare suke yi da Ruqayya dake shige mata,dai² sau ɗaya Zannah baice mata komai game da matarsa ba har lokacin itama batai masa maganar ba,ko even ya haɗa su matsayin matansa yayi masu nasiha,kullum zai shigo ya gansu tare ya zauna suyi hira,ranan da Ruqayya ta cika kwana bakwai da tarewa daren na 8,wamda a ranan ne zai bar ɗakinta kamar yanda shari'a ta tsara,shiru² Fandi tana jiran shigowar Zannah dan duk sauran kwanakin tare take kwana da yaranta amma yau da yake ta san kwananta ne bisa shari'a sai ta kwantar da su ɗakinsu,har tai bacci baza tace ta ji motsinsa ba,da safe ma ko da ta tashi still taga wayam,abun ya taɓa mata zuciya,ta danne duk yanda take jin kuka ta shiga kitchen ta shirya abincin safe,bayan ta gama ta yiwa yaranta wanka ta shiryasu kamar kullum ta zaunar da su ta kawo masu abinci,suna cikin ci Zannah ya shigo parlon,Fandi bata ɗago ba ta gaisheshi yara ma haka ya amsa,sanda ya zauna yana kallon fuskarta yace "kiyi haƙuri jiya ban shigo ba har kikai bacci,ƙanwarki ce bata jin daɗi shi yasa na tsaya gurinta" ta gyaɗa kai tace "Allah ya bata lafiya" ya amsa,har ya tashi zai fita ko me ya tuna ya waigo yace "na sha'afa har yau bamu zauna da ku ba.." Ita dai bata ce komai ba tana bawa Sanda shayin da ta gama fifita masa,Zannah dake kallonta yace "idan kun gama ki shiga ki dubata,kuje tare da yara su gaisa da Aunty'nsu" idan Fandi tai magana tou kujeran da suke parlon sun motsa,ya gaji da maganarsa yai gaba,bayan sun gama suka shiga sukai wa Ruqayya sannu da jiki,the way take wani irin narkewa Fandi ta fahimci lafiyarta lau tsabar iya kisisina ne,suna gama abunda ya kawo su ta kaɗa yaranta suka fita,Zannah kuwa tunda ya fita bata kuma ganinsa ba sai da dare ya shigo,shima kuma tunda ya kwanta bai ƙara motsi ba sai da asubah da ta tasheshi yaje sallah,kafin ya shigo tana ji ya shiga ɗakin amaryarsa har bacci ya ɗauketa bata ji shigowarsa ɗakin ba. A hankali kwanaki suka fara turawa,a ɓangaren zamanta da shi kawai dai za tace gashi nan ne,haka kou yara ma tun zuwan Ruqayya gidan idan ya dawo za suje da gudu suyi masa oyoyo,wani lokacin har su bishi ɗakin amaryar tasa,sai dai Fandi ta jiyo ana cewa "kuje gurin Maamanku" ko "ku tafi kuyi wasa" tun al'amarinsa na damunta sama² har ya fara neman fin ƙarfinta,ranan da ta gaji da sauraren zai raba masu girki da ayyukan gida tai masa magana tunda kullum ita keyin komai shi ne fa ta samu dai ya zauna da su ranan ya raba masu kwana biyu-biyu har ya ɗan masu ƴar nasihar zaman lafiya da juna.. Alhamdulillah! Kuma suna zaman lafiyar,dan tunda aka kawo Ruqayya duk inda ya kamata Fandi ta kaita cikin dangin Zannah ta yi,wani lokaci kou gidansu za taje tare suke zuwa,yanda take nunawa ƴan uwan Fandi so tana masu hidima wani abun kou ita Fandin bata masu,cikin lokacin Ruqayya ta fara laulayi,duk da ba wani mai zafi bane,amma a hakan Fandi ke kula da komai da ita tunda suna zaman lafiya,har zuwa lokacin da cikinta ya tsufa,ranan da Allah ya sauketa ta haifi ɗa namiji,kada kuso ganin murna gurin Zannah,sai nan² yake duk da ba wannan ne karon farko da aka fara masa haihuwa ba,yanayin hidimar da yake yi zaisa mutum yaji wani iri,Fandi ta yi ƙoƙarin ɗauke kai saboda kada tunanin wani abu ya shiga ranta,tunda suna zaman lafiya da Ruqayya,ranan suna yaro yaci sunan baban Ruqayya Nuhu,faɗan irin kayan da Zannah yaiwa iyalinsa kusan ɓata baki ne,haka manyan ragunan da ya yanka,washe garin suna Ƙanwar Baban Ruqayya da take gidan tunda Ruqayya ta haihu da Ruqayya sukai sallama da Fandi saboda za taje wanka gida,dama an bari ne har ayi suna,kamar kada su rabu saboda sabo,yara kam har da kukansu sai sun bi Aunty,da ƙyar aka rarrashe su,Ruqayya suka tafi suna ɗaga masu hannu. Tunda Ruqayya ta tafi Sokoto kulawar Zannah ke kansu Fandi ita da yara,wani sabon shafin soyayya ya buɗe masu,a haka kwanaki sukai ta tafiya. Kamar yau Ruqayya ta tafi sanda ta share wata uku a Sokoto,kullum sai Fandi ta tambayeshi yaushe za ta dawo,zaice mata dai suna hanya,shiru² har sai da sukai wata biyar ciff,zuwa lokacin wasu kam ma har sun fara zargin ko sakinta Zannah yayi yake ɓoye masu,rana a tsaka Zannah yake sanar da Fandi dawowarta,Fandi tayi masu addu'ar sauka lafiya,washe garin ranar kuwa sai ga Ruqayya ta doka sallama,Fandi ta amsa ta fito ɗaki tana mata sannu da zuwa da kuma hanya,tunda Ruqayya ta kalleta sau ɗaya ta wani ɗauke kai,a can ƙarshen wuya ta amsa da "Yawwa! Ya kike?" Jikin Fandi a sanyaya ta amsa,ta tambayeta lafiyar Nuhu da suke kira da Khalifa,bata amsa ba ta wuce ta buɗe ɗakinta ta shige,tunda Ruqayya ta dawo al'amura suka sauya,gaba ɗaya ta daina shiga harkar Fandi,girki da komai Fandi keyi a gidan sarauniyar sai dai taci ta kwanta,and kou za su haɗu a tsakar gidan Fandi bata isheta kallo ba bare gaisuwa ko tambayarta yaranta,sanda take yiwa Zannah maganar raba girki,tunda Ruqayya ta dawo yace ta bari zai mata magana yana sane,daga nan sanda suka ɗauki hanyar wata guda a haka,har lokacin bai magana ba sai dai tashin zance,data sake masa a karo na biyu ya fara faɗa "ni bansan me yake damunki ba wallahi,kwanakin nan wani ganin ido kike ji da shi,mene ne dan kin yi girki da aikin gida? Tunda dai yaranki dake kuke ɓatawa" tunda yai wannan maganar Fandi bata kuma ce masa komai ba akan maganar ta ci gaba da kula da gidan da ƴaƴanta kamar yanda ta saba,girki ne dai tai alƙawarin baza ta kuma yi da shi kou matarsa ba indai ba wai yana ɗakinta ba,duk da har yanzu babu wani bambanci tsakanin ranar kwananta da na Ruqayya inda yaga dama nan zai kwana,duk abunda yaga dama shi yake yi a tsakaninsu,ita kuma tai alƙawarin baza ta sake masa magana akan komai da zai yi ba. A hankali yanayin zaman nasu gaba ɗaya ya canja,kulawar da yake masu a da da yanzu komai ya fara bambanta,ko ɗan wasan da yake yi da yara ma duk ya dena,za suyi masa sannu da zuwa duk sanda ya shigo gida zai amsa fuska babu wadataccen annuri da zaran ya shige ɗakin matarsa can za ta jiyo dariyarsu yana ɗaga ɗansa yana masa wasa,duk wanda zai shigo gidan zai yi tunanin suna zaman lafiya ne saboda duk wani hanyar da zaisa a fahimci wani abu tsakaninsu Ruqayya bata bada fuskar da za'a fahimci komai,haka kou ta ɓangaren Fandi duk wanda zai tambayeta kou akwai wani abu ta kan ce babu,a zahiri duk ƴan uwanta suna ganin yanda tayi rama me munin gaske,duk mai hankali ya kalleta kuma zai fahimci tana cikin damuwa,amma ko an tambaya ba ta cewa komai,hatta Baba idan taje gida yana yawan tambayarta idan da wani abu ta sanar masa,sai dai ta girgiza kai tayi masa murmushi,tace "babu komai Baba" zai tambayeta yara tace "suna nan lafiya" haka kou yanayin zamansu da kishiyarta ma za tace masa lafiya lau. Haka rayuwa taita tafiya,a kwana a tashi babu wuya gurin Allah,yara suna girma suna fuskantar yanda rayuwa take sauyawa,duk lokacin da Ruqayya za taje ganin gida kuwa dama ba ta dawowa da wuri,sannan duk dawowar da za tayi sai an samu wani sabon abu ya sake ɓullowa,da daɗi da rashinsa haka nan Fandi ke rayuwa cikin gidan,tunda Zannah bai ce ya sawwaƙe mata ba bare ta tattara ta tafi gidansu,cikin lokacin yaranta duk sun fara zama samari dan Abbor har ya shiga matakin jami'a,while Sanda ya kammala secondary School,a ɓangaren zamansu a gidan da rayuwarsu kusan za su iya cewa mahaifiyarsu ce komai nasu,baza su ma iya tuna wani abu da mahaifinsu yayi masu ba ko ya yiwa mahaifiyarsu,sai dai yanzu da suka fara mallakar hankulansu su suke taimaka mata,tun daga aikin gida har zuwa abunda za su ci,kou da Abbor ya samu gurbin karatu a Jami'ar Maiduguri boarding ya tafi sai idan ya samu hutun ƙarshen semester kou weekends,sai gidan ya rage Sanda da mahaifiyarsu sai kuma kishiyarta da ƴaƴanta da ta kafa sabon mulki,komai ita ke cewa ayi a gidan yanzu,da zaran ta furta kuma babu musu ne Zannah zai yi,Sanda duk yana ganin abubuwan da ake na rashin adalci,sau da yawa yakan yiwa Mahaifiyarsu magana yace "Maama wai me yasa Baaba yake yiwa Aunty kaza ke baya maki?" Sai tace "nima yana min mana,kai ne dai baka sanin lokacin da yake yi ɗin" to daga haka zai bar maganar,dan idan ya takura lallai sai ya san abunda yayi mata rufeshi take da faɗa,ya kan bata haƙuri daga nan bazai kuma magana ba,dan Allah ya yi shi mutum mai sauƙin kai sai dai idan ka taɓo shi akwai faɗa sannan idan gaskiya tazo ko da iyayensa ne ya kan faɗa masu,kou da al'amura suka ci gaba da tafiya a haka ya samu Baaban yai masa maganar yanda yake yiwa mahaifiyarsu abubuwan da basa kamata,uban ya shigo gida ya rufe Maama Fandi da faɗa har yana kiranta da munafuka,ai ya san duk ita ke zaunar da yaran tana kitsa masu ƙarairayi,yanzu in banda lalacewa har nawa Sanda yake da zai sameshi yana faɗa masa magana,abun yaiwa Fandi ciwon da tai kuka har ta godewa Allah,da dare Sanda ya shigo gidan tai masa faɗa sosai tace idan bazai iya cire idonsa akan abubuwan da suke faruwa a gidan ba tou ita dai za ta daina kula shi,haƙuri ya bata sosai yai mata alƙawarin bazai sake magana ba tunda ba ta so,ya tashi ya tafi ya kwanta yana ta tunanin wa zai samu ya sanarwa ya yiwa Baaba faɗan abunda yake bai kamata ba,a lokacin kakansu mahaifin Fandi ya jima da rasuwa,sai Ƙannensa da kuma ƴan uwan Baabansu Zannah,tunda shi dama maraya ya taso babu uwa bare uba,kou da ya kai ƙarar baban ma dai abunda ya faru ne ya sake maimaita kansa,haushin yanda Sanda ke zuwa yana haɗa shi da ƴan uwa yasa shi sakin Fandi,lokacin tai kukan rashin iyayenta a raye dan ko zaman gidansu ma yanzu wani irin zama ake tunda Baba ya rasu kowa ya kama kan iyalinsa ya ware gidan duk an kacalcalasa wasu sun fitar da kansu daga gidan gandun sun kange iya sashen su,abinci da ƙyar ake sammata,har ta gwammace zaman gidan mijinta da nan,dole tasa ta yiwa Abbor aike makaranta dan lokacin bai jima da komawa ba hutun 1st semester level 3,cikin weekend yazo ya tarar da ita da halin da take ciki,dole ya kira Sanda suka je suka bawa Baabansu haƙuri,shi ne fa suka samu ya mayar da ita da yake saki 1 yayi mata bayan mugayen sharuɗan da ya gindaya,suka ce sun ji sun amince,a ranan Maama Fandi ta dawo gidan,tun daga ranan Sanda yake iya ƙoƙarin ganin ya ɗauke idanunsa akan al'amuran gidan sai dai tsakaninsa da matar Babansu harara dan kou gaisheta ma ya daina yi,ita kuma wannan abun ya fi komai ɓata mata rai,haka kou tsakaninsa da Ƴaƴanta duk wanda yai masa abu duk ƙanƙantarsa yanzu zai kama yaro ya make,sai dai suje mata suna kuka,idan ta tambayi mene ne suce Yaya Sanda ne ya dake su,abun yana bata haushi ta rasa yanda za tayi da Sanda,duk ta inda ta ɓullo shi kuma sai ya san yanda yayi ya cusguna mata taji baƙin ciki,Sanda ya zame mata ciwon ido a gidan. Ana cikin haka ne ya samu Baaba yace yana son ya nemar masa admission ya gaji da zama gara kou makarantar da Yaa Abbor yake ne shima a nemar masa,Baaba yace ya bari yayi shawara,ƙarshe dai sai tashin zance,abun ya bawa Sanda haushi dan ya san duk lokacin da Baaba yace zai shawara ba shawarar kowa zai nema ba sai na Aunty,a lokacin Aunty'n nasu kuma bata jima ba tayi tafiya garinsu,amma wannan lokacin bata yi irin jimawar da take ba ta dawo,bai haƙura ba ya sake samun Baaba da maganar makaranta,Baaba yace bai da halin saka su duka a makaranta yanzu,sai dai ya bari idan Abbor ya gama,yace tou ya nemar masa aiki da Secondary certificate ɗinsa,idan yaso daga baya sai ya nemi tafiya ƙarin karatu,shima again yace ya jira sai ya yi shawara...

     This book isn't for free,normal ₦300 posting 5 days excluding weekend,VIP ₦500 posting daily,SP 1K all via 0060746882-Hauwa Muhammad Usman,access bank. Then u show ur evidence of payment via https://wa.me/+2348165726609. If u are willing to pay,my sister pay it now before the price will go up,after it is completed the price is ₦500.

#Follow
#Vote
#Comment
#Share fisabilillah!
#Asli Smasher.

CIWO A JIKIN WANI!Donde viven las historias. Descúbrelo ahora