Kishi!

68 6 0
                                    

💠💠💠💠💠
©®AS-2022.






              *♡CIWO A JIKIN WANI¸.•💥*
                            '''(Kᴡᴀʀɪ)'''
                           



   *HAWWA__B__KUMO.*
     (Rᴇᴀʟ Sᴍᴀꜱʜᴇʀ).💕
*WATTPAD:@REAL-SMASHER.*
*AREWABOOKS:@REALSMASHER.*

     '''Iɴ ᴅᴇᴅɪᴄᴀᴛɪᴏɴ ᴛᴏ ᴍʏ ʟᴀᴛᴇ ᴅᴀᴅ Aʟʜ Mᴜʜᴀᴍᴍᴀᴅ Bᴀʙᴀ Usᴍᴀɴ (B–KUMO).'''

      '''Bᴇsᴛᴏᴡᴇᴅ ᴛᴏ Mʏ Zᴀʜʀᴀ Aʙᴅᴜʟʟ Tᴀғᴇᴇᴅᴀ (Nᴀ'ᴇᴇᴍᴀ).'''
••••••••••••••

                               08

#Kishi!

   '''Thanks for ur Support u and ur beautiful heart,together make u a special one. A honest guide from the start,and all the things u have done. May be i would have even managed it otherwise,but u helped the journey to an easier way. For u threw light on my lanes,with every advice,and what u did for me,is something i can never pay. So,i thank u u and ur beautiful heart,for ur true support from the start. Thank u dearest,i really appreciate ur help and support! This little poem is for u My Zahra Abdull Tafeeda (Na'eema) ILYSM💓.'''

💝

            Sai kusan 12am saura Baffa ya shigo gidan da waƙa a baƙinsa irin nasu Marigayi Mamman Shata,Adija da har lokacin basu yi bacci ba ta tashi ta fito tsakar gidan a lokacin yana buɗe ɗakinsa,motsinta yasa yai saurin ɓoye ledar da ya shigo da shi ya juyo yana kallonta,tace "sannu da zuwa Baffa" ya amsa yace "baku yi bacci ba har yanzu?" Ta gyaɗa kai jikinta a sanyaye tace "dama jiran shigowarka muka tsaya yi" yace "tou lafiya dai?" Tace "gaskiya Baffa dukanmu a tsorace muke" yace "a tsorace kamar yaya?" Tace "dama.." Sai kuma tayi shiru lokaci ɗaya,yace "ke nake sauraro me yake faruwa?" Tiryan² ta fara masa bayanin haɗuwarsu Aalima da Alh Adam Sardauna da yace ya sanshi da irin kyautar da yayi masu cikin kwana biyun da ya zo,Baffa sai sauraronta yake yana murmusawa,sanda take faɗa masa irin kayan da yayi musu aikensu yau Baffa yayi wani shewa yayi dariya yana ma kansa kirari kamar mafarauci yace "tou shi ya faɗa maku wane ne shi?" Ta girgiza kai tace "a'a" yace "ina ita Aalimar suke?" Adija tace "suna ɗaki Fannah kam kanta ke ciwo ma" yace "tou shi kenan tashi kije da safe zanga kayan da ya aiko,amma babu wani abu da zai faru sai alkhairi" Adija tace "tou Allah yasa.. Sai da safe" ta tashi ta shige ɗakinsu,kallonta Ashey dake zaune tayi tace "me yace?" Adija tace "da alamun ya san mutumin ne,baki ji dariyar da yayi ba da na faɗa masa" Ashey ta sauke wata relieved ajiyar zuciya tace "alhamdulillah! Tunda ya sanshi ina ga da sauƙi" Adija dai ta koma gurin kwanciyarta tana sauke ajiyar zuciya itama tace "Allah yasa.." Da safe Baffa ya shigo duba kayan yana ta murmushi,Aalima dai na can tsakar gida tana aikinta,Baffa ya kalli Adija yace "ina uwata?" Adija tace "ta tafi school" Baffa yayi murmushi sannan ya fita daga gidan. Da rana bayan Fannah ta dawo school dake can Bukavu Barrack take zuwa Army day,tunda tai sallama Baffa dake dakon shigowarta ya ƙwalo mata kira,ta amsa sanda ta fara ajiye jakarta a ɗaki sannan ta shigo ɗakinsa,ta durƙusa ta gaishe shi,ya amsa ya nuna mata guri yace "zauna sosai uwata" yanda yake wani nan² da ita jikinta ya fara sanyi,banda gabanta dake wata irin faɗuwa,ta gyara zama ta zauna dai²,Baffa yana kallonta yace "uwata na yi maki mijin aure,amma na faɗa masa kina karatu yanzu,in sha Allahu idan kin kammala makaranta zan aura masa ke,nai masa alƙawarin nan,idan Allah ya kaimu nan da sati biyu zan karɓi kuɗin aurenki na ajiye,na sanar maki ne tun yanzu gudun fita hakki.." Tunda Baffa ya fara magana gabanta ke faɗuwa kanta ya fara wani irin sarawa,har ya gama magana tunani take,yanda za tayi aure ta bar su Yaa Adija kawai cikin mugun yanayin rayuwa da tun tashinsu suka tsinci kansu ciki,sanda ya gama magana baza ta iya cewa ta ji kalma biyu ƙwarara ba,sai da yace taje ta huta tunda daga makaranta ta dawo,ta tashi kamar dama jira take ya sallameta ta fita,tunda ta shigo ɗakin bata iya magana da kowa ba ta kwanta kou uniform bata cire ba,kuka take son yi amma duk rauninta yau hawaye sun yiwa idanuwanta hijira,damuwa ya cunkushe mata zuciya sosai,nan da nan wani irin zazzaɓin fargaba ya rufeta daga ciwon kai,Baffa da ya gama shirin fita har yai hanyar soro ya tuna akwai maganar da bai sanar mata ba ya juyo ya kalli Adija yace "ina uwata?" Adija tace "tana ɗaki ba ta jin daɗi" a ɗan rikice yace "tun yaushe? Me yake damunta" Tace "tunda ta dawo,zazzaɓi ya rufeta" wucewa Baffa yayi da sauri ya ɗaga labulen ɗakin nasu ya kalleta yace "uwata jikin ne?" Ta gyaɗa masa kai a hankali,yace "sannu.. Allah ya ƙara sauƙi" underneath her breath ta amsa,fita Baffa yayi daga gidan gaba ɗaya,Adija suka bishi da kallo ganin bai ce da su komai ba kuma sai wani rawar jiki yake yau,Ashey tace "lamarin Baffa yana ɗaure min kai wallahi" Adija ta taɓe baki taƙi cewa komai. Ba'a jima ba Baffa ya dawo gidan jikinsa na rawa ya shiga ƙwalawa Adija kira dan Aalima ba ta nan ta fita babu jimawa,Adija ta fito ta durƙusa gaban Baffa,ya miƙo mata tarin magunguna da ya siyo fuskarsa da fara'a yace "ki bawa uwata tasha,idan bata samu sauƙi ba kuma ki kira ki sanar min zan fita yanzu" gyaɗa kai Adija tayi mamakin Baffa yau fal ranta,paracetamol na naira 10 za ta iya cewa bata san yaushe ne ya taɓa siya masu ba,ko da kuwa ace ciwo zai kashesu,bare akai ga sauran matsalolinsu na yau da kullum,komai su suke nema su yiwa kansu,duk wani hakki na uba bai saukewa na su a matsayin Ƴaƴansa,kou sana'a da suka ce ya basu jari suyi cewa yayi shi ba'a gidansa ba baya son abunda za aita zuwa sassafe ana sallamar a bada kaza,da ace ma sana'ar ya karɓe su ne duk da sauƙi,komai suka taɓa ko suka siyo da niyyar siyarwa da an fara zuwa ana siya kamar abun arziki sai kuma a daina,ƙarshe sai dai su gaji idan na amfani ne a gida suyi amfani da shi,idan kuma saɓanin haka ne sai dai su nemi wanda yake siyarwa su haɗa shi da Allah da Annabi ya siya ya basu kuɗin saboda wahalar da suke ciki,tun daga lokacin shi ne yace su nemi wani abun banda wannan,dan basu da sa'a sam a rayuwarsu,kamar wanda akaiwa asiri baƙin jininsu yai yawan da har ta kai ga saurayi babu me ƙwaƙƙwara a cikinsu,dole tasa suka haƙura suke zaune babu sana'ar yi,amma abun yana mugun damunsu,shi yasa ko fita basa yi,basu da wasu tsayayyun ƙawaye,ijunansu suka haƙawa su binne,babu mai jin kansu shi yasa kuwa kansu yake a haɗe,komai ɗaya ya samu na sune gaba ɗayansu,ɗan abunda Fannah ke samowa a islamiyya kuɗin term da ake ma malamai ihsani,da kuma Director da yake mata kyauta akai²,tunda ya fahimci yanda suke rayuwa,wani abun kuma yana jinsa a unguwa game da yanda suke zaune,wannan dalilin yasa da yawan Malamai da ɗalibai suke ganin sonta yake,sai dai har yanzun shi kuma ta gefensa bai fito ya faɗa mata da bakinsa ba,kuma ba wai bai sani ko bai fahimci abunda mutane suke faɗa game da alaƙarsu bane. Wani irin juya maganin Adija ta dunga yi a hannunta,Baffa ya kalleta har ya juya zai tafi yana waƙar "Na tsaya ga Annabi Muhammadu! Na tsaya ga Annabi Muhammadu! Kalmar harshe nasan wannan! Daga zucci ake ƙaunar Allah! Daga zucci ake ƙaunar Manzo! Allah sa muga Annabi Muhammadu! Na tsaya ga Annabi Muhammadu! (Sallallahu alaihi wasallam)" (Alhaji Dr Mamman Shata. Allah ya jikansa.. Ameeen). Sai kuma ya juyo yana kallonta kamar da faɗa yace "tashi kiyi sauri mana,me kike jira baki tafi kin bata maganin ba?" Tashi Adija tayi kamar wanda ta farka daga mummunan mafarki ta shiga ɗakin,Fannah na kwance har lokacin lulluɓe da wani bargo,Ashey ta kalli Adija data shigo dan ta jiyo muryar Baffa kamar yana faɗa tace "me ya faru?" Adija ta nuna mata maganin hannunta tace "Baffa ne ya siyowa Auta magani" Ashey ta zaro idanuwa surprisingly tace "Baffa!?" Adija ta gyaɗa mata kai ta kalli inda Fannah ke kwance rufe tace "Fannah!" Fannah tace "Mmm!" Adija tace "tashi ki sha magani" miƙewa zaune tayi hawaye suna saukowa fuskarta ta zauna,Adija ta kalli ƴar uwarta cike da wani irin tausayinta ta zauna ta ɗauko mata ruwan gora cikin cartoon wanda Baffa ya buɗe ɗazu ta ɓallo mata maganin ta bata,jikinta babu ƙwari saboda yanda zazzaɓin yai mata kwaf ɗaya ta karɓa ta sha,sannan ta koma ta kwanta tana share hawaye,Ashey dai kallon Adija kawai take ta kasa daina mamakin abunda taji,can ta gyaɗa kai tace "Allah ya kyauta" sannan ta fita ɗakin ta tafi ɗaura masu abincin dare,fitowa daga ɗakin Adija tayi ta kamawa Ashey aikin da take suna yi duka sun yi shiru babu mai cewa komai sanin Baffa yana gida bai fita ba,babu halin su yi maganar yanzu dole sai idan ya fita,fitowa Baffa yayi daga ɗaki ya rufe da makulli yana waƙa,Adija ta kalleshi ta wutsiyar ido,yayi murmushi yana kallonsu yace "an bata maganin kou?" Adija tace "ehh!" Bata ɗago daga abunda take ba,yace "tou madalla.." Har yai hanyar soro zai fita ya dawo yace "da wane lokaci Alh Sardauna yake zuwa?" Duka suka ɗago suna kallon Baffa,Adija ta daure tace "after ishaa" Baffa yace "tou babu laifi.. Na fita sai na dawo" taɓa baki sukai a tare sannan sukai masa fatan dawowa lafiya,ya sa kai ya fice daga gidan. Wuraren ishaa ya dawo gidan da wani sallamar da kana ji ka san yana cikin nishaɗi ne,suka amsa duka suna cikin ɗaki,basu yi zaton ɗakin zai shigo ba sai da yazo ƙofar ɗakin sannan suka ji yana magana yana cewa "bismillah.. Ƙaraso Honourable" muryarsa da ba ɓoyayye ba yasa Aalima yin wani tsalle ta rarumo hijabai ta ciccilowa su Adija itama ta saka lokacin Baffa ya sake yin sallama kafin su shigo,Adija tace "Aalima janyo darduman nan kisa shi can kamar tare yake da baƙo" Aalima tayi yanda Adija tace mata,Baffa dake gaba ya ɗaga labulen ɗakin ya fara shigowa sannan Alh Sardauna dake biye da shi cikin wani irin farin shadda sai ƙyalli da ƙamshi yake zubawa turarensa har ya gama cika ɗakin,Aalima tana ganinsa ta sunkuyar da kai cike da kunya tace "sannu da zuwa" ya kalleta yana ɗan murmusawa yace "anya zan amsa kuwa?" Aalima tayi ƴar dariya kawai ta gaisheshi,sai kuma ya amsa yana tambayar me jiki,Adija da Ashey ma duk suka gaisheshi ya amsa yana masu ya me jiki,Fannah dai na kwance har lokacin zazzaɓin ya tafi ya dawo yake mata,yinin ranar kawai idan kaga yanda tai zuru² za ka rantse ta fi wata tana ciwo,in fact bata ma cikin hayyacinta bare ta gane su waye a ɗakin,muryoyi da yawa kawai take ji shima bata san su waye da su waye ba,Alh Sardauna yana kallon yanda ta rufe har kanta ya kalli Baffa dake tsaye yace "an kaita hospital ne?" Baffa yace "a'a andai siyo magani" Alh Sardauna ya girgiza kai yace "think bai kamata a barta a gida ace za'a siyo magani without ta ga Dr ba,Taya za'a bawa mutum magani da ka ba Dr ya bada umarnin shi za'a bata ba.. Please a shiryata muje Hospital taga Dr right now" Baffa ya wani washe baki yace "Allah ya taimakeka duk yanda kace ai haka za'a yi" Baffa ya kalli Adija yace "ki shiryata kuje tare" Adija tace "tou" mamakin Baffa fal kanta yanda yake wani rawar jiki akan mutumin,Alh Sardauna ya tashi yana kallon Baffa yace "muje waje muyi magana kafin su fito" Baffa yace "tou ranka ya daɗe" suna fita Adija ta kalli Aalima tace "ku shirya mu tafi tare sai mu kulle ɗakin,ni bazan iya zuwa ni kaɗai ba,kuma idan nace mu tafi dake,Ashey kawai za mu bari a gida,which is not good" Ashey tai dariya tace "kawai kuje zan zauna har ku dawo kada aga rashin hankalinmu" Adija tace "a'a ki shirya muje dai taren zai fi.." Amsa mata tayi saboda ba ta cika son aita jan zance ba ko taita jayayya da mutum,tare suka fito dukansu Adija da Ashey sun riƙo Fannah dake kuka,tunda suka fito yake kallonsu,Baffa dake tsaye ya kallesu yace "ba dai duka za ku bisu ba?" Adija tace "Baffa ni nace masu muje tare,ni kaɗai bazan ji daɗin tafiya ba,idan muka tafi da Aalima kuma Ashey kawai za mu bari a gida,ka ga dare ne baza ta ji daɗin zaman ba" Baffa zai magana Alh Sardauna yace "barsu muje ɗin kawai ai tafiya mutum ɗaya baida daɗi,itama da za'a bari idan babu kowa baza taji daɗin zaman ba" Baffa yace "tou babu matsala.. Ku rufe gidan zan je unguwa nima" Aalima ta koma ta rufe gidan lokacin duk sun shiga back seat na ƙaton Prado ɗin da yazo a cikinsa,Aalima ta buɗe front ta shiga,Baffa yana tsaye yana masu addu'ar Allah ya tsare hanya,Alh Sardauna yaja motar suka tafi. Direct UMC Zhahir Hospital dake No. 1C Forestry Road (Dorayi Babba Jambulo) ya nufa,sanda yayi parking cikin premises na hospital ɗin ya sauka motar,Aalima ta fita itama da sauri ta buɗe masu Adija duk suka sauko suka nufi cikin hospital ɗin,yanda masu kuɗi ke walagigi cikin hospital ɗin dake nan kamar ba'a Nigeria ba yasa su Adija raina kansu da irin shigar dake jikinsu,sai dai fuskokinsu kawai mutum zai kalla yayi zaton ƴaƴan wani hamshaƙin me kuɗi ne,tunda suka shiga ake gaishe da Alh Sardauna respectfully,yana amsawa cikin sakin fuska,office ɗin wani consultant Dr suka tsaya sanda yayi knocking sannan ya buɗe ƙofar yana yin sallama,Dr dake zaune ganin wanda ya shigo yasa shi tashi da sauri yana masa maraba,Alh Sardauna ya amsa sannan ya zauna yana amsa gaisuwar Dr Sadeeq,after then yana kallon Fannah dake jikin Adija yace "me yake damunta?" Adija tace "daga ciwon kai ne rashin lafiyar nata sai kuma ta fara zazzaɓi" ya gyaɗa kai sanda yayi ƴan rubuce-rubuce kan file da ya ɗauka yana tambayar sunanta,Adija tace "Fannah Farouk" Dr Sadeeq ya rubuta komai sannan ya kallesu yace "mutum ɗaya ta riƙeta muje laboratory" Aalima tace "Yaa Adija kuje kawai sai mu zauna da Yaa Ashey mu jira ku" Adija ta ɗago Fannah da kawai binta take,ko yaya aka motsata sai tai squeezing face ko hawaye su fara biyo fuskarta,she's so tired and weak,komai da ya kamata ayi mata Dr Sadeeq yasa akai mata bayan sun dawo ya kaita ward aka bata special room,ya buɗe cannula Adija na zaune har sannan gefen Fannah dake kwance,Dr Sadeeq ya gama haɗa drip da some injections na zazzaɓi ya kama hannunta yasa mata ƙarin ruwa,sanda ya gama komai sannan ya yiwa Adija Allah ya ƙara sauƙi ya fita,yace bari ya sanar da Honorable Sardauna,not too long ago suka buɗe ƙofar suka shigo dukansu har Dr Sadeeq,Alh Sardauna ya kalli yanda take kwance kan gadon cikin yanayin jin jiki yace "Dr Sadeeq a duba ta sosai Please idan da matsala ko yaya yake a sanar min.." Dr Sadeeq yace "in sha Allah ranka ya daɗe ai inaga za mu riƙeta a nan ta kwana biyu,idan ta dawo back to normal sai mu sallameta" Alh Sardauna yace "good.." Sun jima a hospital ɗin sannan yace su Ashey suzo ya mayar da su gida,da safe sai su dawo suga jikin nata,while Adija kuma za ta zauna tare da ita har ta samu sauƙi,sukai sallama da Adija ta basu saƙon abunda za su kawo masu gobe idan za su dawo sannan suka tafi,har sun fita Alh Sardauna ya dawo yana kallon Fannah dake bacci yace ma Adija "i forgot to get ur number zan kira saboda naji idan an samu improvement" Adija tace "tou" ta karanta masa number ya kira sai yaga ta fito da wani jagwal ɗin waya babu kyan gani gara ma na Aalima akan wannan,ya mata sallama ya fita dan shi su Ashey suke jira,yana fitowa kuwa suka tafi,sanda ya kai su gida,bayan sun masa sallama sannan ya kama hanyar gidansa. Da safe ko da su Aalima sukai shirin tafiya hospital bayan sun gama komai,sai da suka tsaya jiran zuwansa,tunda ya sanar masu zai zo da safe ya ɗauke su,yauma Aalima ce a front bayan sun fito unguwar Zango,maimakon su miƙi titin da zai kaisu har gidan sarki daga nan su wuce har flyover na kabuga sai ya juya motar suka koma IBB way,su dai basu san ta ina zai biba tunda ba yawo suke ba basu san kan hanya ba,su ne har Beirut road kasuwar siyar da waya,ya tsaya bakin wani shagon da banda Apple phones da danginsu babu abunda suke siyarwa,tunda suka tsaya Aalima ke kallon shagunan siyar da wayoyin,ya sauka motar while yana masu magana su sauko,babu musu duk suka fito suka bishi cikin shagon da ake masu barka da zuwa,Ashey da ba sanin me suka zo yi suka yi ba suka nemi guri suka zauna AC na kaɗa su,shi kuma yana amsa tambayar wani guy da yace "ranka ya daɗe me kuke so?" Yace "wayoyi za ka bamu" yace "kamar wane iri?" Alh Sardauna yace "ɗauko su duba" tafiya yayi ya fara ɗauko masa different tun daga 7+,8,9,10,11,12 har 13 pro Max duk ya zubesu,Alh Sardauna ya kallesu yanda suke ɗan magana suna kallon wayoyin cikin shagon yace "hey! Will u come over and join us?" Suka kalleshi,yace "kuzo kowa ta ɗauki wanda take so" kallon juna suka yi sai suka girgiza masa kai,ya buɗe ido yace "halin Aalima ya shafi kowa ne halan?" Aalima ta ɗauke kai tana dariya,yace "kuzo ku duba da sauri kada muyi late zuwa hospital" Aalima ta kalli Ashey dake girgiza mata kai,duk yanda zai masu magana ya yi amma sam suka ƙi zuwa su ɗauka,ya rabu da su duk ya ɗaukar masu 13 pro Max,sai ɗaya 14 irin nashi gold color,har accessories na wayan sai da yasa aka ɗauko ma kowa kalar nata daban,akai masa totalling bill ya basu ATM suka cire sannan aka haɗa masu komai then suka fito shagon,har sim cards ya siya masu akai registration sannan suka tafi,still basu wuce kai tsaye ba sai da suka tsaya wani mall yayi masu siyayya kamar hauka,sanda ya tsaya eatry yayi masu take aways da fruits then suka tafi hospital ɗin,Adija kawai ganinsu tayi da ledoji,tai masu sannu da zuwa ta gaisheshi,akan Fannah dake bacci idanunsa suka fara landing,while yana amsa gaisuwar Adija ya tambayi me jiki ta amsa masa,lokaci ɗaya yana ɗaga waya da tambayarta Dr Sadeeq ko ya shigo? Ta amsa masa da bai jima da fita ba,fitar shima yayi yace bari yaje ya sameshi a office,kamar wanda suke jiran ya tafi,nan suka hau bawa Adija labari suna nuna mata kayan da ya siya masu da sababbin wayoyinsu,Adija ta dunga juya wayarta tana murmusawa,wai yau itace riƙe da tsadadden waya irin wannan,sam ta kasa gasgata idanunta,nan kuma duk suka hau rige²n saka charge sannan suka zauna hiran siyayyar da ya dunga yi a hanya kamar bai san ina ake samo kuɗin ba,Adija tayi murmushi tace "ku daina damuwa Allah ne ya aiko mana shi tsuntsu daga sama gasasshe,domin ya cire mu daga irin wahalar rayuwar da muke" suka sa dariya duka na kalmar tsuntsu daga sama gasasshen da tafe,Aalima tana dariya tace "shi kenan sai ci kawai tunda a gashe ya faɗo" suka sake yin dariya tana tambayar su Baffa suka ce yana gida ya ce ma a gaishe da Fannah da jiki kafin yazo,Adija ta gyaɗa kai tace tana amsawa. A week later... Zuwa lokacin Hamdiyya duk ta gama guje²nta,kasancewar Monday to Friday duk sintirin zuwa office bai barsu sun zauna ba,kullum Malam Ado zai kaita banking da take aiki idan lokacin tashinta ya yi zaije ya ɗaukota,sanda za ta dawo gida a gajiye sosai take shigowa,duk inda ta ci abinci ta watsa ruwa a jikinta sallah kawai za tayi ta kwanta,wani lokaci ma ko sallar ba ta yi saboda gajiya za ta kwanta nan za tai bacci idan ta tashi kuma babu tabbacin ta rama sallolin saboda addinin ba wani damunta yayi ba,in fact a gidansu ma ba sosai take ganin Mummy'nta tana yi  ba,sam ba'a bambance lokacin da take da tsarki da lokacin da take menses,daga nan sai gobe kuma idan Allah ya kaimu,haka shima Mutallab a nasa gefen,sam bai da lokacin kansa kullum sassafe yake fita office yana aiki military headquarters,amma dake babbane shi a Department Of Army Logistics shi ne Chief of Army Logistics (COLOG). Bayan nan yana da alaƙa da wasu departments ɗin kusan shi ne na huɗu gaba ɗaya a Land army na Nigeria,but zai mugun wahala ka iya ganewa cewar wai shi ɗin wani ne,idan ba wanda ya sanshi ya faɗa maka ba,kou ka binciko ma kanka ba,dan shi bai cika saka kaki ba kullum suite yake ta'amalli da shi,kansa ko yaushe da beret kalar suit ɗinsa kalar hular dazai sa,idan ka ganshi cikin shigar nan za ka rantse wani ma'aikacin bank ne ko Company,sam rayuwarsa babu tashin hankali,sai dai bai da sakin fuska ko kaɗan,kallon farko kayi masa za ka ɗauka wani kurma ne,dan magana bai cikin ɗabi'arsa,idan ka ga yana hira ko dariya tou a gaban mutum ɗaya ne which is his Mom,Wanda a duniyarsa ita kaɗai ta rage masa bai da kamarta,because mahaifinsa ya jima sa rasuwa shekaru da dama kenan,Captain Abdulmaleek Muqaddas shi ne cikakken sunan mahaifinsa,haifaffen garin Kano ne kuma tsohon Sanata a jihar Kano,bayan nan ya taɓa zaman ɗan majalisar wakilai,sannan shi ɗin tsohon matukin jirgin sama ne (pilot),kafin rasuwarsa kuma ya kai matakin Minister of aviation. And his Mom Mr's Abdulmaleek Muqaddas babbar lauye ce wanda ta taba riƙe muƙamin shugaban kula da ɓangaren shari'a na tsohuwar jam'iyyar PP ta shugaban da ya gabata,sannan secretary a ƙungiyar kare hakkin ɗan Adam ta duniya (Human right) da ake ji da ita,asalinta ƴar jihar Gombe ce,aure ya kaita Abuja a lokacin iyakar karatunta secondary lokacin da baban Mutallab ya aureta,sai bayan aurensu ne sannan ya mayar da ita makaranta inda ta karanci LAW,har kuma Allah ya kaita matsayin da take a yanzu wanda ake damawa da ita a siyasar ƙasa tun bayan rasuwar mijinta (wannan kenan). Yana zaune parlour ya ɗaga kai ya ɗan kalli Hamdiyya dake saukowa,a hankali ya lumshe idanunsa ya janyesu ya mayar kan ball ɗin da yake kallo,ƙarasowa tayi cikin parlon tana kallonsa,a hankali ta zauna next to him ta ɗan kwantar da kanta jikin shoulder ɗinsa tace "good evening Honey" bai kalleta ba yace "ya kike? And how are u feeling?" Tace "ohh! Dama ka san banda lafiya ne?" Yace "not at all.. Ni da kike gudu ya za'ayi na sani,am just asking if u were ok" ta ɗan yi ajiyar zuciya tace "ai ka azabtar da ni ranan nan wallahi,gaba ɗaya kaƙi jin tausayina" yace "ni dake waye yake azabtar da wani?" Shiru tayi saboda ba maganar da ya sauko da ita ba kenan a lokacin,ta ɗan turo baki tana shagwaɓewa tace "ni dai magana nazo muyi da kai" yace "uhmn! I'm all ears" ta kallesa yanda hankalinsa ke kan ƙaton plasma TV da ake haska live match ɗin ranan da ake da Real Madrid,and he's fan of the team,ta kamo face ɗinsa tace "tou ai ba ni kake sauraro ba fa" kallon cikin idanunta yayi yace "wa yace bake nake sauraro ba?" Tace "tou ai kallon ball kake" yace "wai ba da kunne ake ji bane?" Tace "Mmm!" Tana zumɓuro masa baki,yace "faɗi abunda kike so ina ji" tace "dama maganar nan nake son maka,na ji baka ce komai akai ba har yau" ya ɗan kalleta a wani iri yace "ni kike jira na maki magana,akan me kenan?" Tace "tou ai ban sani ba ko ka yarda ayi?" Yace "okay!" Tace "kamar ya okay?" Yace "me kike so nace?" Tace "ka yarda ayi ɗin?" Yace "Diya! Don't start please" da sauri ta dakatar da shi tace "answer me first" kallonta ya dunga yi yai shiru,lokaci ɗaya ta tashi ta wuce sama cikin sauri kamar za ta tashi sama,ya bita da kallo har ta haura kafin ya tashi ya biyota,a bedroom ɗinta ya tarar da ita ta kwanta ruf da ciki tana kuka,ya shigo ya zauna a hankali ya kai hannu bayanta yace "tashi ki zauna muyi maganar" wani irin ɗagowa tayi ta kalleshi tana sake fashewa da kuka tace "i know yanzu ba ka sona Abdulmutallab.. Sam baka damu da ni ba yanzu" yace "waye ya faɗa maki haka?" Tace "if u really care about me why kake ƙin abunda nake,me yasa duk abunda ya shafe ni Ka dena ɗaukarsa da mutunci? Da ai ba haka kake min ba" ɗan girgiza kansa yayi cikin wani irin yanayin damuwa yace "ba haka bane Diya! Sam kin kasa fahimta ta,kin kasa gane me nake hangowa zai faru nan gaba" cikin ihu tace "mene ne zai faru? Indai ba wai kana da wani ɓoyayyen manufa a ranka ba,mene ne zai faru Mutallab? Ka fito ka sanar min ka bar min ɓoye²" shiru yayi kamar wani soko yana kallonta,tace "shi kenan kawai,mu barshi tunda ba ka son maganar,nima na haƙura zan jure zagi da ƙiyayyar family'nka,amma wallahi ka rubuta ka ajiye tunda ka hana ni wannan damar nima baka isa kace za ka auro min wata mace ka haɗa ni kishi da ita ba.. Idan kuwa ka dage kace za kai min kishiya,zan barka ka auro ko wace ce,amma wallahi sai dai ayi ko ni ko kuma ita,amma bata isa ta shigo ta haihu da kai ba ina kallonku ba.."


   '''#Hello guys! Ina maku tuni da cewa mun kusan kaiwa ƙarshen free pages,so ina bada shawara a hanzarta zuwa ayi payment,babu tabbacin idan mun kai end of free part za mu tsaya,za mu ɗaura ne daga inda muka tsaya in sha Allah,na gode sosai masoyan gaskiya,a koda yaushe ina alfahari da ku,more especially ƴan VIP da SP,saboda yanda kuke patronazing duk paid books ɗina. ILYSM💔'''

           This book isn't for free,normal ₦300 posting 5 days excluding weekend,VIP ₦500 posting daily,SP VIP 1K all via 0060746882-Hauwa Muhammad Usman,access bank. Then u show ur evidence of payment via https://wa.me/+2348165726609. If u are willing to pay,my sister pay it now before the price will go up,after it is completed the price is ₦500.



#Follow
#Vote
#Comment
#Share fisabilillah!
#Asli Smasher.

CIWO A JIKIN WANI!Where stories live. Discover now