Sirri

72 6 9
                                    

💠💠💠💠💠
©®AS-2022.





              *♡CIWO A JIKIN WANI¸.•💥*
                            '''(Kᴡᴀʀɪ)'''
                           


   *HAWWA__B__KUMO.*
     (Rᴇᴀʟ Sᴍᴀꜱʜᴇʀ).💕
*WATTPAD:@REAL-SMASHER.*
*AREWABOOKS:@REALSMASHER.*

     '''Iɴ ᴅᴇᴅɪᴄᴀᴛɪᴏɴ ᴛᴏ ᴍʏ ʟᴀᴛᴇ ᴅᴀᴅ Aʟʜ Mᴜʜᴀᴍᴍᴀᴅ Bᴀʙᴀ Usᴍᴀɴ (B–KUMO).'''
••••••••••••••
     '''Masu buƙatar a tallata hajarsu u should contact me ta number na,kou kuyi magana kai tsaye ta https://wa.me/+2348165726609.'''

                               05

#Sirri

            Tunda ta farka taga Mutallab a kusa da ita hannayensa a saman ƙirjinta ta wani ɗaure fuska haɗe da turesu ta sauka daga gadon tana jan shegen tsaki,rigarta dake yashe ƙasa ta ɗauka tasa ta wuce bathroom,a hankali ya buɗe idanunsa masu cike da bacci,ganin Hamdiyiya bata nan yasa shi shafa kwantaccen beard ɗinsa kafin ya sake lumshe idanunsa,almost 3 minutes ya buɗesu jin an sake buɗe ƙofa,da kallo yabi Hamdiyiya data fito daga toilet ta nufi ƙofa,har ta fita daga ɗakin ba tare da ta kalli inda yake ko ta gaishesa ba,numfashi sosai ya saki alamunta ya gwada masa har yanzu tana kan fushi da shi,and hakan na nufin zai sha fama da ita kafin ta sauko,tashi yayi ya zauna ya kifa fuskarsa tsakanin palms ɗinsa,tunanin maganganun Mimi yasa shi yin shiru yana tunanin mafita,lallai kam yau ya kamata shima ya nuna mata shi namiji ne,kuma shi ya kamata tabi ba wai shi yaita binta ba kamar wata uwarsa,saurin zura bed shoe yayi ya tashi,toilet ya fara shiga sanda ya wanke baki sannan ya sakarwa jikinsa ruwa,a nutse ya gama komai ya fito da wani irin towel bathrobe a jikinsa,ɗakin yabi da kallo tuna komai nasa yana ɗakinsa yasa ya nufi ƙofa ya fita heading to asalin master bedroom ɗinsa ya buɗe ƙofar,tsayawa yayi ya dunga bin ɗakin da kallon mamaki,yanda ya ganshi tas² anyi tidying unlike daren jiya,duk abunda ya lalace an fitar da shi,ya girgiza kansa saboda takaici,mamakin Hamdiyya fal ransa dan ya san wannan ba aikinta bane,and the worst part of it ma shi ne ya sha faɗa mata ba ya so tana sa maids suna shigar masa ɗakin bacci,idan baza ta iya gyarawa ba ta bar masa abunsa zai gyara da kansa,akan haka bazai iya lissafa sau nawa sukai faɗa da ita ba,but ya san duk wannan abun da take bazai rasa nasaba da faɗan da sukai daren jiya ba,a duk lokacin da irin haka ta faru tsakaninsu komai ƙanƙantar laifi sai ta yi ƙoƙarin ganin ta ɓata masa rai fiye da zato,irin matan nan ne da suke zuzuta laifi da kumburasa,gashi bata san ayi abu ya wuce a gurinta ba riƙon bala'i ne da ita,ko zai ba ta haƙuri kafin ta sauko sai ta garasa,wucewa yayi ya buɗe wani irin haɗaɗɗen reach-in closet dake nan idan ba an faɗa maka ba za kayi zaton kawai decorations ne a gurin saboda yanda ya saje da marble 3D wall sticker da aka yiwa ɗakin,duk abunda yake buƙata ya ɗaukarwa kansa tun daga kan inner wears,ya ƙarasa bakin gadon ya zube komai yana kallon tarin pillows da aka shiryasu kan gadon kai baza kace sune aka watsar jiya ba,fuskarsa ɗaure saboda takaici yaja siririn tsaki,a gurguje ya shirya cikin wani checks red wine suit ya kawo beret ya ɗora akansa kalar suit ɗinsa,after ya gama ya gyara beard ɗinsa ya fito zuwa bedroom ɗinta sai ƙamshinsa da ya cika corridor ɗin,yau yake so suje hospital ayi mai yiwuwa ya gaji da ƙumbiya²n da take masa,if akwai matsalar da take ɓoye masa ne ma gara ya bincika ya sani,sosai ya ɗaure fuskarsa saboda bai son abunda zai kawo masa cikas a duk abunda yai niyyar aiwatarwa,knocking bedroom ɗinta yayi tana ciki kwance har sannan bata tashi ba,sanda ya sake knocking kafin ya buɗe ƙofar ya shiga,bacci ya tarar da ita tana yi ya dunga kallonta da mamaki kafin ya zauna gefen gadon ya kai hannu ya matse hancinta,saurin ware idanunta tayi jin iska ya dena kaiwa cikin hunhunta,sakin hancin nata yayi yace "sai yaushe za ki tashi?" Fuskarta ɗaure tace "wai me yasa kake son tashina ne? Yau naga weekend ne kou?" Yace "tashi ki shirya za mu fita" ta masa wani kallo tace "zuwa ina? I think na faɗa maka jiya nima ina da gurin zuwa yau,right?" Bai amsa ta ba yace "get up i'll wait u downstairs" ta turo baki kaɗan kafin ta tashi ta zauna,miƙewa yayi ya nufi ƙofa while yana cewa "don't keep me waiting.." Daga haka ya fita bedroom ɗin,ba don ranta na so ba ta tashi ta shiga tai wanka,sanda ta shirya cikin wani black arabian gown ta ɗauki heel takalmi da pos mai kyau silver colours,fuskarta babu makeup ko kaɗan sai lip balm data shafawa lips ɗinta kawai ta fito tana tafiya,sam Hamdiyya ba ta cikin matan da suke ɓata lokacinsu gurin makeup,tana yawan faɗa cikin ƙawayenta her natural beauty is enough for her,she doesn't want ta tsaya fente kyakkyawar fuskarta,ta fi son asalin natural face ɗinta a ko wane lokaci,ƙaran footsteps ɗinta da uban ƙamshin turarukanta masu hawa kai yasa shi ɗagowa sanda take saukowa daga sama,da kallo ya bita har ta ƙaraso inda yake ta zauna saman kujera tana ɗaukan telephone ta kira kitchen,cook ɗin ya ɗauka cikin Pidgen English ya sanar mata breakfast is ready yana dining room,bata ce komai ba ta katse wayar ta tashi tayi gaba,tashi Mutallab yayi ya biyo bayanta also suka zauna dining kowa yayi serving kansa,lafiyayyen breakfast suka yi irin na gidan masu shi,after then suka fito yana gaba tana binsa a baya har compound da bai cike da tarkace,tent ne kawai dake ɗauke da wasu irin maka²n luxury cars,driver da suke zaune tare da almost 4 militant gate keepers suna hira,yana ganin fitowarsu ya taso da ɗan sauri ya ƙaraso yana gaida su,Mutallab ya miƙa masa key ɗin mota,Malam Ado ya karɓi key yace "oga ina muka nufa?" Mutallab yace "Nisa Premier Hospital" Malam Ado yace "an gama ranka ya daɗe" da hanzarinsa even though ya kusa haifarsa ya buɗe masu motar suka shiga,kafin yayi horn ɗaya cikin gate keepers ya buɗe masu,suka fita suna masu addu'ar Allah ya tsare hanya,tunda Hamdiyya taji ya ambaci hospital gabanta ke faɗuwa,ta kasa daurewa ta kalleshi tace "wai hospital ɗin dai za mu?" Ba tare da ya kalleta ba yace "in sha Allah" ta dunga kallonsa ta kasa ɗauke idanunta lokaci ɗaya tace "amma na faɗa maka ina da abun yi yau fa" yace "save ur words Diya,don't start please.." Shiru tayi saboda yanda yake magana yau,she even made sure akwai abunda ya taka,har suka shigo cikin premises na hospital ɗin babu wanda ya sake magana,Malam Ado yayi parking carline ya fito ya buɗe masu motar,Mutallab ya fara fita yace "ka jira mu" Malam Ado yace "tou yallaɓai sai kun fito" ba don ranta na so ba ta fito tana kiran number Mom ɗinta ta sanar mata suna hospital,Hjy Shafa'atu na ta sauraranta lokaci ɗaya cikin faɗa tace "ke kuma kika yarda kika bishi?" Tace "Mummy bai sanar min ba,ai da na san nan za mu zo bazan biyoshi ba wallahi" uwar tace "ai shi kenan tunda haka kika so ya faru,yanzu kuma sai da kuka je za ki kirani ki sanar min,kamar dai baki san komai ba,da kafin yanzu ne ai da na kira Dr na ce kuna hanya ya san abunda zai faɗa masa,kada ya ɓaro mana aiki" Hamdiyya kamar za tai kuka tace "Mummy ba hospital ɗin da muke zuwa bane,wani ne daban wallahi.. I'm scared,kada a gano matsalar nan a sanar masa yau" shiru uwar tayi ta kasa magana,ita kanta a tsorace take,can tace "kuma babu yanda za'ayi ki samo number Dr ɗin mu san abun yi kafin ya gano kan matsalar ya sanar masa?" Hamdiyya tace "bari na gwada Mummy sai na turo maki,tunda ni muna tare babu yanda za'ayi nayi magana da shi" Mummy Shafa'atu tace "tou ki hanzarta kafin su dama mana aiki" Hamdiyya tace "Allah yasa na samu" daga haka ta katse wayar da sauri tana tunanin yanda za'ayi ta samu number Dr ɗin da za su gani,ba suyi tafiya mai nisa ba suka iso bakin office ɗin Dr Jim,da yake weekend ne ba cikowa asibitin,Mutallab yayi knocking ƙofar office ɗin,daga ciki Dr Jim ya bashi izinin shiga,ya buɗe ƙofar ya shiga,Hamdiyya ta shiga itama tana yi masa sallama,wani kallo Mutallab dake shirin zama ya mata,ya rasa me yasa Hamdiyya ta kasa ganewa,duk sanda za su je guri sai yai mata maganar ba'a yiwa Christian sallama,amma ita har yau bata fasa ba,ya yi siririn tsaki a ciki ya zauna yana miƙawa Dr Jim hannu tare da masa barka da aiki,suka gaisa Dr Jim yana sakin fuskarsa kafin yace "meke tafe da ku ranka ya daɗe?" Mutallab da fuskarsa ke kadaran kadaham yace "Dr kan matsalar nan dai da mukai magana da kai muka zo" Dr Jim ya kalli Hamdiyya dake gaisheshi ya amsa,hankalinsa akan Mutallab dake magana yace "alright! Yanzu za muje ayi test,after then za'ayi scanning,idan mun tabbatar komai normal sai mu san irin shawarwarin da za mu ɗaura ku akai" Mutallab ya amsa ya tashi,Hamdiyya ta faki idon Mutallab ta turawa Dr Jim wayarta ta masa alamar yasa mata numbersa,sanda ya gama rubuce² sannan ya tashi suka fita tare,a hanya ya miƙawa Hamdiyya wayarta,shi ya kaisu duk inda ya dace,after an gama komai suka dawo office ɗinsa,kaf results ɗin ya haɗa yana dubawa kafin ya shiga yiwa Mutallab bayanin komai ta ɓangarensa shi lafiya lau,but a gefen Hamdiyya ne there's some issues,Hamdiyya gabanta yana faɗuwa sosai ta dunga kallonsa tana jira taji me zai ce,ya kalleta yanda ta firgice lokaci ɗaya yace "i'm sorry Madam but kada ki tunanin akwai matsala ne babba,mahaifarki ne bai da ƙwarin da zai iya ɗaukan Baby,idan an takura kuma za'a iya samun matsala.. But tunda u're newly wedded zan iya baku shawara" Mutallab dai kallonsa kawai yake ya ƙi cewa komai saboda yanda yaji maganar ya saɓa da sauran da ake sanar masu,Dr Jim yace "think a maimakon kuyi adopting child from orphanage,me zai hana ku iya neman wanda za ta rainar maku ciki,because mahaifarta bai da ƙwarin da yaro zai rayu a ciki har a haifesa,and idan aka takura sai lallai ta ɗauki cikin tou ina tabbatar maku za'a iya rasa duka ku biyun.. Abu mafi alkhairi gareku ku nemi surrogate mother,in dai kuna son haihuwa,ko kuma ku haƙura duka" wani irin relieved ajiyar zuciya Hamdiyya ta dunga saukewa,Mutallab da yai shiru lokaci ɗaya saboda yanda maganar ya dakesa,ya kalli Dr Jim yace "yanzu babu yanda za'ayi mata ta ta iya ɗaukar ciki kake son cewa?" Dr Jim yace "babu Mr A.A,kawai dai shawarar da na baku shi ne ta hanyar surrogate za ku iya samun jaririnku,duniya an samu ci gaba,ba sai ka je ka yi adopting child daga orphanage ba" Mutallab ya girgiza kansa still ya ƙi cewa komai,Hamdiyya dake kallonsa tace "kamar yaya surrogate? Akwai wani tsarin da ake bine idan za'ayi shi?" Dr Jim yace "yes akwai" kamar Mutallab bai gurin,Hamdiyya tace "okay! Dr muna saurarenka,we need more information about it please" Dr Jim ya gyara zamansa sannan ya fara masu bayanin komai da tsare²n da za'a bi wajen yin surrogate "Surrogacy tsari ne that often supported by a legal agreement,wanda mace ta yarda da bayarwa/aiki ga wani mutum ko kuma ma'auratan da za su zama iyayen yaron bayan haihuwa. Surrogate wani lokaci ana kiransa da Gestational carrier,and is a woman who convinces,ta ɗauki ciki sannan kuma ta haifi yaro ga wani mutum ko ma'aurata (intended parents). Hanyoyin da za'a bi wajen dasa ciki ga wata mata wanda ba ta hanyar aure ba kamar dai irin wannan,hanyoyi ne kamar haka:1)Traditional surrogate:-Mace ce take samun ciki ta hanyar artificially inseminated. Yawanci ana samun cikin ya shiga mahaifarta ne ta hanyar intrauterine insemination (IUI) za'ayi amfani da donor sperm (maniyyin mai bayarwa) maniyyin wanda zai zama uba,daga nan sai su ɗauki jaririn da suka haifa for u and ur partner to raise. And a traditional surrogate jariri ne na biological mother. That's because it was their egg that was fertilized by the father's sperm,and donor sperm can also be used. 2)Gestational surrogate:-Tsari ne da ake kira "in vitro fertilization" (IVF) yanzu yana ba da damar tattara ƙwai daga uwa (or an egg donor) da maniyyi daga uba (or a sperm donor),wanda za'a sanya embrayo a cikin mahaifar mai mayewa (ma'ana wanda za ta maye gurbin uwa) wanda za ta ɗauki jaririn a mahaifarta har zuwa haihuwa. Sai dai a nan uwar mayewa (Surrogate mother) ba ta da wata alaka ta ƙwayoyin halitta da yaron saboda shi ba kwanta aka yi amfani da su ba. Ana kiran Gestational surrogate da "birth mother." A kowace shekara akan iya samun kimanin jarirai 750 ta hanyar yin amfani da gestational surrogacy. Sannan a ƙasar Amuruka (U.S) gestational surrogacy is less complex legally,that's because both intended parents suna da alaƙar ƙwayoyin halitta da jariri. A sakamakon haka gestational surrogate ya zama ruwan dare fiye da traditional surrogate.. Idan kun amince da irin wannan tsarin,ina ganin zai zama hanya mafi sauƙi da za ku samu jaririnku cikin sauƙi kamar sauran iyaye." Tunda yake magana idanun Mutallab ke kansa,sanda ya dasa aya Hamdiyya ta gyaɗa kai tana murmusawa tace "and how much can it cost?" Dr Jim yace "the average cost of surrogacy can range from $90,000 to $130,000 depending on the individual arrangements. Kamar a states like California da surrogates are in high demand,the cost may be slightly higher. And legal requirements and the costs of other services can also vary from state to state" Hamdiyya ta sauke wani numfashi ta kalli Mutallab da bai ce komai ba har sannan ta riƙo hannunsa,ta wutsiyar idanunsa ya kalleta sai dai bai ce mata komai ba ya miƙe yace "thanks Dr.." Hamdiyya ganin ya miƙe itama ta tashi tace "mun gode Dr sai ka ji daga gare mu" ya amsa yana masu fatan komawa gida lafiya. A hanya kallonta kawai Mutallab keyi tunda suka fito office ɗin Dr Jim,bayanan da yayi masu game da matsalar da suke ciki da bai ga damuwa a fuskarta ba duk ya ɗaure masa kai,sai kuma maganganun Dr Jim game da surrogate da yasa shi haɗe girarensa dan ya san ba hankali ne da ita ba,yanda ta ɗauki maganar tasa a ranta,yanzu sai ta tada masa hankali tasa yayi abunda ba shi kenan ba,Hamdiyya da tai fuskar tausayi tunda suka taho take masa maganar yai fuska ya ƙi tankata,tana kwantowa jikinsa tace "tou wai ya kake so ayi ne Honey? Nifa Ina ganin bamu da wani mafita sai wannan,tunda ni bazan iya ɗaukan cikin ba,why baza mu biya wata ta ɗaukar mana ba? Idan ta haihu shi kenan sai mu karɓi ɗanmu mu sallameta,ni na fi yarda ma da wannan tsarin akan muyi adopting from orphanage kamar yanda Dr yace" Mutallab da ya juyo lokaci ɗaya yana kallonta yace "Diya mu bar maganar nan haka ina ganin zai fi mana alkhairi" cikin ɓacin rai tace "kamar ya mubar maganar?" Cikin zafin rai yace "haka nace" tace "saboda ni matsalar ya shafa shi yasa kake cewa a barshi,right?" Ya ɗauke kansa yana kallon waje sam bai jin daɗi yau,and yanda yaga ita abun bai dameta ba sai yake hasashen kamar ta san wani abu dake faruwa shi kawai take ɓoyewa,Hamdiyya tace "kayi magana Mutallab,saboda kana da damar sake yin aure ka haihu shi yasa ni kake cewa ba ka son abunda zai zamar min farin ciki?" Ta faɗa da rauni a cikin maganarta,Mutallab yace "wannan abun ba dai² bane Diya,kada mu mafara maganar nan dake,wace ce wanda za ta yarda da wannan tsarin? Baza'a samu ba a nan ƙasar saboda babu wanda za ta yarda ta lalata rayuwarta saboda farin cikinmu,nima kuma ba na sonsa dan Allah kawai mu nemi wani hanyar amma banda wannan,ina so maganar nan ya tsaya tsakaninmu dan ba na son Mimi taji,kin san abunda zai iya faruwa idan na biye maki.." Cikin hayaniya tace "kamar ya kada Mimi taji? Sai dai in kai za ka faɗa mata,amma idan ba haka ba har ayi komai a gama baza ta taɓa sani ba,tunda ba gidanmu take zuwa ba.. Kawai ka amince ni zan nemo wanda za ta rainar mana cikin,idan ta haihu mu karɓe Baby mu sallameta shi kenan fa" wani kallo ya dunga mata yace "ba shi kenan ba Diya,i'm really scared tunda kikai maganar nan,zuciyata bata nutsu da maganar ba,in fact bazan iya bada sperm ɗina ma wata ƴa mace ba indai ba mata ta ba,kin san hukuncin da zai biyo baya idan akai haka? Gaskiya i'm confused about the matter" dariyar rainin wayo tayi mai cike da shewa irin wanda kana kallonta ka san na dole ne a babu yanda za tayi,tace "okay! Na ji tunda baka yarda ba,ka san dai babu yanda za'ayi kayi aure kaima kou?" Ya mata wani kallo ya kasa magana,ta buɗe masa idanu tace "yes! This is ur promise.." Yace "Diya stop.." Tace "ai gara na tuna maka ne,dan wallahi kace za kayi aure zan iya kashe duk me tsautsayin da ta yarda za ta zama matarka.. Ina da kishi sosai irin wanda ni kaina nake jin tsoron ranar da wata mata za ta buɗe baki tace she's ur legally wife.. Dan wallahi ranan akwai bala'i ne,da haka ta faru gara ace matan waje ka nema ko kuma na mutu.." Wani irin kallo yake mata zuciyarsa na bugawa yace "did i made any promises to u?" Tace "ehh kafin aurenmu" yana girgiza kai yace "this is impossible.. Ni da bakina nai maki wannan alƙawarin?" Da wani irin murya kamar wanda ke magana da ɗanta tana masa faɗa tace "stop Mutallab kada ka nemi raina min wayau,dan ka ga yanzu ina cikin matsala shi ne za ka nemi kayi min butulci? Sau nawa muke maganar da kai kana ce min kai ba ka da tsarin mata biyu,sai yanzu ka fara ɗauko wani zancen daban" ɗan murmushi yayi yace "that's the point.. Ni ban taɓa maki alƙawarin bazan ƙara aure ba,i'm just saying it ba ni da ra'ayin tara mata,kada ki juyan magana please,and stop lying to me wai na yi maki alƙawari" ta gyaɗa kai hawaye suna kawowa idanunta tace "na ji ba ka da ra'ayi,but haka na nufin za dai kai auren kenan? Za kai min kishiya kake son faɗa min? Abunda ban tashi na gani a gidan mu ba,shi kake so ya faru a kaina?" Ya ɗaga shoulders yace "wannan kuma wani magana ne daban,idan Allah ya tsara ni ban isa hana haka faruwa ba" ihu tayi masa tace "wallahi baka isa ba Mutallab.." Ya kalleta ransa a ɓace yace "okay! Za kiyi jayayya da hukuncin Allah kenan?" Tace "i swear duk ranan da kace za kayi aure,kou zan yi yawo tsirara bazan barku ku zauna lafiya ba,ko zan rasa komai nawa sai na yi yanda zanyi na watsa maganar" kallonta ya dunga yi mamakinta ya cikasa,ganin babu amfani ya biye mata kawai ya buɗe motar ya sauka yana wani irin gasping for breathe,wani zafi yaje ji yana taso masa tun daga zuriya yana biyo duk matsiran gashin jikinsa,Malam Ado driver da ya gama jin duk hayaniyar da suke ya bishi da kallo,lokaci ɗaya ya buɗe motar yana kallon Hamdiyya data kifa fuska tsakanin tafukan hannayenta,ya gyara zama ya juyo sanda ya rufe glass ɗin gefensa,tun lokacin da Mutallab yace ya tsaya,bayan yai parking gefen hanya yace ya fita ya basu guri,tunda ita mahaukaciyar tasa bata san wane magana ne ya kamata suyi gaban wasu ba da kuma wanda basu kamata ba,so kafin ya fita sanda ya ɗan sauke glass ɗin saboda ya fara jin maganar da suke,kuma bai son ya rasa jin ƙarshen zancen,Hamdiyya dake cikin tashin hankalin maganganun Mutallab,ta yi zaton shi ne ya dawo cikin motar,bata ɗago ba tace "yanzu ka fi son danginka suyi ta min gorin rashin haihuwa kenan Mutallab?" Malam Ado yayi ɗan gyaran murya kafin yace "Madam ai ba shi bane" saurin ɗagowa tayi idanunta da hawaye ta kalleshi,ta girgiza kai ta juya tana kallon waje tana goge idonta,Malam Ado yace "idan baza ki damu ba Madam ni ina so muyi magana dake" girgiza masa kai tayi tana fashewa da kuka sosai,Malam Ado yace "kiyi haƙuri Madam,na san rashin haihuwa abune mai ciwon gaske a gurinmu,amma idan za ki yarda da maganata,ni zan nemo maki mafita" Hamdiyya dake kuka tace "ta ina za ka nemo min mafita? Kana ganin kou Mutallab ya ƙi ba ni haɗin kai,ta ina zan fara ni kaɗai babu mataimaki?" Malam Ado ya sauke ajiyar zuciya yace "idan kin bani dama ni zan zama mataimakin da kika rasa" Hamdiyya ta girgiza kai tana share hawaye,Malam Ado yace "akwai wani mutumin da na sani a garinmu,akan kuɗi wallahi babu abunda bazai maki ba,in fact babu abunda bazai iya yi maki ba ko ya baki matuƙar za ki biyashi" Hamdiyya tai saurin juyowa ta kalleshi,ya gyaɗa mata kai yace "abokina ne tare mukai aiki da shi,yana da ƴaƴa huɗu mata namijinsa ɗaya ya mutu,idan kika je masa da buƙatar ki wallahi na tabbatar zai maki,musamman ace ni na maki jagora,ai matsalarki ya zo ƙarshe kenan,ke da kuka sai dai kiga ana yi.. Amma matsalar ɗaya ne" da sauri tace "mene ne shi?" Yace "yanda za'ayi yallaɓai ya amince,na ga kamar bai son maganar ne,ni kuma ina jin tsoron sa kaina ciki yazo ya sani daga baya a samu matsala,na san zai iya korata daga aiki,kin san kuma da aikin nan na dogara" ɗan murmushi tayi tana goge hawayen da suke idonta tace "ni ban damu ba in dai zan samu biyan buƙata,ko babu amincewarsa zan yi,kawai ka gaya min inda za mu samu shi abokin naka.. Ni zan ji da sauran matsalolin" Malam Ado yace "ai kada ki damu Madam,har gidansa zan kaiki ayi komai a gama,amma ki min alƙawarin ko ya sani daga baya suna na bazai fito ba" ta gyaɗa masa kai tana dariyar farin ciki tace "Malam Ado kada ka damu haka bazai taɓa faruwa ba" yace "na gode Madam" Hamdiyya dake jinta cikin farin ciki tace "idan haka ya faru ban san da me zan biyaka ba,dan ka magance min matsalolin da suke neman zama barazana ne a rayuwata" Malam Ado yace "babu komai Madam ai duk abunda nayi maku ban faɗi ba,yanda kuka riƙeni kamar ɗan uwanku,idan nai maku tamkar yiwa kai ne.."



           This book isn't for free,normal ₦300 posting 5 days excluding weekend,VIP ₦500 posting daily,SP VIP 1K all via 0060746882-Hauwa Muhammad Usman,access bank. Then u show ur evidence of payment via https://wa.me/+2348165726609. If u are willing to pay,my sister pay it now before the price will go up,after it is completed the price is ₦500.

#Follow
#Vote
#Comment
#Share fisabilillah!
#Asli Smasher.

CIWO A JIKIN WANI!Where stories live. Discover now