Tsoro

65 5 2
                                    

💠💠💠💠💠
©®AS-2022.






              *♡CIWO A JIKIN WANI¸.•💥*
                            '''(Kᴡᴀʀɪ)'''
                           



   *HAWWA__B__KUMO.*
     (Rᴇᴀʟ Sᴍᴀꜱʜᴇʀ).💕
*WATTPAD:@REAL-SMASHER.*
*AREWABOOKS:@REALSMASHER.*

     '''Iɴ ᴅᴇᴅɪᴄᴀᴛɪᴏɴ ᴛᴏ ᴍʏ ʟᴀᴛᴇ ᴅᴀᴅ Aʟʜ Mᴜʜᴀᴍᴍᴀᴅ Bᴀʙᴀ Usᴍᴀɴ (B–KUMO).'''
••••••••••••••
   '''Masu buƙatar a tallata hajarsu u should contact me ta number na,kou kuyi magana kai tsaye ta https://wa.me/+2348165726609.'''

                               07

#Tsoro

            A soron gidan Aalima ta sameshi yana tsaye,babban mutum sosai ƙamshinsa ya cika soron,tana ɗan murmushi cike da jin kunya ta gaishesa ya amsa yana haskata da tsadadden wayar dake hannunsa ƙiran iPhone 14 Pro Max da bai jima da shigowa ba saboda babu wutar NEPA,yace "da bance ya faɗi haka ba na san baza ki fito ba,right?" Aalima ta saukar da idanunta ƙasa cike da kunya tace "ai ban san kai bane shi yasa" ya gyaɗa kai yace "ina ƙanwar nan taki kuwa?" Aalima tayi dariya tace "Auta tana ciki tana karatu" yace "Allah sarki kou za ki iya kiranta mu gaisa?" Aalima tace "why not?" Tana dariya ta juya ta shiga gidan,Alh Adam yayi wani murmushi yana gyara tsaiwarsa,bata jima ba suka yi sallama ita da Fannah,Fannah ta durƙusa ta gaishesa ya amsa yana haska fuskarsa yake cewa "kin gane ni kuwa?" Fannah ta girgiza kai bata iya kallonsa ba tace "a'a" ya zaro idanunsa yace "are u sure?" Ta gyaɗa kai,yace "jiya kin fita muka haɗu fa" Fannah da ta sauke kanta ƙasa tace "ni banje ko ina ba jiya ai" yace "haba dai?" Ta gyaɗa kai,Aalima sai dariya take masu,yace "a'a ki tuna dai,jiya fa muka haɗu dake da daddare,har gida na rako ki" ɗan yatsina fuska tayi tana tunani sai ta ɗago,da Baby voice ɗinta da kamar za tayi kuka tace "ni babu inda naje jiya wallahi" ya sake zaro idanuwa yace "har kina rantsuwa?" Ta ɓata fuska kamar za tayi kuka,yayi murmushi yace "it's ok.. Na yarda babu inda kika je,ba da ke bane na tuna Aalima ce kou?" Aalima ta gyaɗa kai tana dariya,lokaci ɗaya Fannah ta hau zaro ido tana kallon Aalima tace "did i go out jiya da dare?" Aalima ta fashe da wani dariya tace "ehh mana" ai Fannah na jin haka ta wani kwasa da gudu tai cikin gida,Aalima ta sake fashewa da dariya har tana riƙe ciki,Alh Adam yayi murmushi yana kallonta,sanda tayi mai isarta sannan ta tsagaita,yace "dariya na maki kyau sosai Aalima,ita kuma Fannah.." Sai kuma yayi shiru yana murmushi,ɗan rufe fuskarta Aalima tayi cikin jin kunya,ya ɗan kalli soron da suke ciki kafin yace "ya Mama?" Lokaci ɗaya mood ɗin Aalima ya canja,hawaye suka cika idonta ta ƙurawa guri ɗaya ido kamar tana neman amsar da za ta bashi a gurin,yana kallonta yace "did she died?" Ta gyaɗa masa kai jikinta a sanyaye tana share hawaye,yace "eyyahh! I'm sorry Allah ya mata rahama,ya gafarta mata" Aalima tace "ameen" yace "so yanzu ku kaɗai ne a gidan kenan?" Ta gyaɗa masa tace "ehh mu huɗu ne sai Baffanmu" yace "kuna da yayyu ne?" Tace "ehh muna da su" yace "what's their name?" Tace "Yaa Adija itace babba sai Yaa Ashey,sai ni sannan Fannah" ya gyaɗa kai yace "Allah sarki" daga haka sukai shiru bai sake tambayarta ba,itama kuma bata sake yin magana ba,can yace "bari na tafi kou kada suga na riƙe ki,dama zuwa nayi nan majalisa sai na zo mu gaisa da ku" tayi ɗan murmushi tace "Allah sarki" yasa hannu aljihu ya zaro sababbi fil ɗin ƴan 1k guda biyar ya miƙa mata,ta girgiza kai bata ɗago ta kalleshi ba tace "a'a ka barshi na gode" yace "ai ba naki bane wannan,na Yaa Adija ne" tasa hannu biyu ta karɓa tace "an gode,Allah ya saka da alkhairi" yayi murmushi yace "ohh! Idan ke na bawa baza ki karɓa ba kenan?" Tayi shiru ta ƙi cewa komai,ya sake zaro wasu biyar ɗin ya miƙa mata,ta ɗago da sauri ta kalleshi yace "ki kaima Yaa Ashey" ta karɓa suma tayi masa godiya,sanda ya kuma zaro wasu sun fi 10 ya bata yace "ga na Auta ki kai mata ta siya sweet kafin nazo na kaiku shopping" tayi masa godiya,yace "tunda ke baza ki karɓi kuɗi ba me kike so na kawo maki?" Ta sunkuyar da kanta tana murmushi tace "babu komai" yace "a'a ki faɗa min dai" ta sake girgiza kai tace "babu komai" ya gyaɗa kai yace "alright! Ina wayarki yake?" Ta ɗago ta kalleshi tace "tana cikin gida" yace "je ki ɗauko min na gani sai nasa maki number na idan kuna da wani damuwa ki dunga kira kina sanar min" tace "tou" ta juya ta shiga gidan,tana shiga ɗakinsu ta bawa kowa kuɗin da akace ta bashi,Adija ta kalleta tace "wannan fa?" Tace "shi ne yace na kawo maku" Adija ta zaro ido tace "ke me kuɗi ne?" Aalima tace "wani sugar daddy ne ya ce ya san Baffanmu" Adija tace "ai kuwa mun gode sosai wallahi,ki masa godiya on behalf of us" Aalima ta gyaɗa kai tace "tou" bayan ta ɗauki ƴar wayarta ta fita tana girgizawa Adija dake tambayarta nawa aka bata tace "a'a banda ni,kuma da kuka samu ai kamar tare muka samu ne" tana fita tayi sallama soron Alh Adam dake waya yayi saurin amsawa yace "za muyi magana later" ya katse wayar da sauri yayi concentrating kanta yace "ina wayar?" Miƙo masa ƙamar wayarta tayi,ya dunga kallon wayar ya kasa karɓa yace "wannan shi ne wayar naki?" Ta gyaɗa masa kai ta kasa kallonsa,yayi murmushi yace "kamar ki ai kin fi ƙarfin riƙe wannan wayar sai dai babba,and Auta tana da shi?" Ta girgiza masa kai alamun a'a,ya dunga kallonta kawai yana tunani,Ita dai tayi murmushi ta ƙi cewa komai,yace "mu ganshi?" Ta miƙa masa a kunyace,ya karɓa yana juya wayar sanda yaga ba ta kallonsa ya zaro 10k ya haɗa mata da wayar yace "take please" hannu biyu tasa tana riƙewa taji wayar yai tudu fiye da sanda ta bashi,yana sakin mata ya nufi ƙofa yace "sai gobe idan na zo in sha Allah za mu yi magana dake akan wani abu.. Ki gaida su Yaa Adija,and kice ma Auta ta kyauta,amma ni ba dodo bane ta daina guduna ba zan cinyeta ba,ba na nufinta da komai sai alkhairi" Aalima data bishi da kallo cike da mamakin yanda bai jin fitar kuɗi tace "za suji.. Na gode Allah ya saka da alkhairi ya ƙara buɗi" yana fita ya amsa sai ya ɗan tsaya ya juyo daga ƙofar gidan yana mata murmushi yace "in sha Allah zan bada tukuici gobe" sannan ya juya cikin sauri yace "sai gobe idan na zo" tace "Allah ya kaimu,Allah ya mayar da kai gida lafiya" ya amsa ya sake juyowa yace "na ji daɗin addu'ar nan,gobe zan bada tukuici idan nazo,saura kice baza ki karɓa ba" da sauri ta juya tana dariya ta shige gida,yayi murmushi also sannan ya tafi. Tana shigowa Adija ta bita da kallo cikin farin ciki tace "in Allah ya kaimu gobe za muje kasuwa muyi siyayyar kayan abinci tunda mun samu kuɗi yau,idan muka barsu hannunmu da matsala in dai Baffa ya sani,muma ma ci me kyau kamar kowa kafin Allah ya sake hore mana" Aalima ta miƙa mata kuɗin hannunta tace "ga wasu ki haɗa ki ajiye mana" Adija ta karɓa tana kallonta tana ƙirgawa taga 10k cif,tayi wani ihun murna tana faɗin "Alhamdulillah! Idan aka haɗa kuɗin yanzu za su ishemu mu sai komai da bamu da shi" Aalima da ta zauna gefen katifa tace "Allah ya kaimu goben da safe sai muje" Adija ta ɗaga katifar daga inda take ta cusa kuɗin tace "in sha Allahu kuwa" Fannah da tai shiru tana tunani hawaye suna cika mata idanu jikinta a sanyaye tace "na yarda Allah ba ya taɓa tozarta bawansa,matuƙar bawa ya roƙesa" Adija ta kalleta tayi murmushi tace "haka wannan magana take.. Allah ka ƙara mana daga cikin falalar ka." suka amsa duka da "ameen.." Da sauri kuma Adija ta kalli Ashey tace "ki rubuta komai kada mu manta" Ashey tace "tou.. In sha Allah da safe zan rubuta.." Kallon kyakkyawar fuskarta yake cikin wani irin yanayi tana miƙo masa wani irin kyakkyawan jariri a cikin white set kayan sanyi an naɗesa cikin baby towel,fuskarta mai ɗauke da wasu irin baƙaƙen hawaye da ya ɓata shi,yayi kamar wanda aka fainting fuskar nata da baƙin coalter,jikinsa a sanyaye yasa hannu ya karɓi yaron yana kallonta fuskarsa babu annuri,a wani irin tsorace kamar zai yar da yaron ya ɗago kansa,kafin yayi magana yaga ta matso ta fizge jaririn ta rungumesa a jikinta,ya ɗaga kai ya ci gaba da kallonta ya kasa furta mata even a single word,tana masa wani irin kallo still baƙin hayen suna rolling down a fuskarta da babu abunda yake gani face manyan idanuwanta,sai kuma yaga ta juya tana tafiya cikin wani irin sassarfa ba tare da ta yi masa magana ba itama,ta dunga bin saharar dake gabanta da babu gini ko ɗaya a gurin har tai masa nisan da ya kusan daina hangota,da sauri ya buɗe baki zai kirata even though bai san sunanta ba,kiran sallar da aka fara masallacin dake cikin estate ɗin yasa shi buɗe idanunsa,jikinsa a mugun mace ya tashi ya sauka gadon ya nufi bathroom,ko da ya ɗaura alwala ya fito,sai da ya fara yin nafila yayi raka'atanil fajr,sannan ya nufi ƙofa ya fita,bakin ƙofar ɗakin Hamdiyya ya tsaya yayi knocking ya kirata,sai da ta amsa yace "ki tashi asubah yayi" sannan ya nufi ƙasa ya fita. Bayan an idar da sallah ya fito daga masallaci ya nufo gidansa,a ransa yake tunanin irin mafarkin da yayi,sai lokacin ya fara ƙoƙarin tuna fuskar wanda ya gani amma sam ya rasa wace ce,a haka ya shigo gidan ya haura sama ya buɗe ɗakinsa ya shiga,har ya tuɓe jallabiyar da ya fita masallaci yana shirin sake kwanciya ko me ya tuna kuma sai ya ɗauki ƙaramar riga yasa ya nufi ƙofa ya fita,bedroom ɗin Hamdiyya yayi knocking yana kiran sunanta "Diya! Diya!!" Cike da magagi ta amsashi,yace "kin tashi kuwa kin yi sallar?" Cike da jin haushinsa tace "na tashi mana" yanda ta amsa yasa shi yin murmushi ya juya ya koma ɗakinsa ya kwanta kan gado yana ɗan danna wayarsa yana azkarus'sabah,sai kusan 7am sannan bacci ya sake ɗaukarsa. Da safe shayi me kyau suka sha da bread da ƙwai da suka siya cikin irin kuɗin da suka samu,suna gama karyawa Adija da Aalima suka tashi sukai shirin tafiya kasuwa,suka bar Ashey da Fannah a gida suna aikin gidan,Fannah tayi wanke² kafin ta gama Ashey har tai sharar tsakar gida zuwa soro,tana gama wanke² ta wanke banɗakinsu ta shiga kitchen ta gyara,ganin Fannah na wancan aikin ita kuma sai ta share masu ɗakinsu sannan suka zauna jiran dawowar su Adija da cefanen da za suyi girkin rana da dare,Fannah ta ɗauko wayar Aalima da ta bari a gida ta fara duba inda litattafan ta suke tana duba littafin Ifzaa kafin su dawo ta ɗan karanta itama ko shafi ɗaya ne,Ashey dai kallonta kawai tayi batai magana ba,kusan hour ɗaya sannan su Adija sukai sallama daga kasuwa suka fara shigo da kayan da suka siyo,shinkafa ƙaramin buhu sai sauran kayan abinci da cefanensu na kayan maggi da mai,Fannah sukai masu sannu da zuwa sannan suka fara fitar da wanda za'a kai kitchen ita da Ashey,kayan abinci kuma suka barsu nan cikin ɗakin kafin Fannah ta haɗa wuta ta ɗaura masu abincin rana. Kou da ya fito cikin shirinsa ne cikin wani irin Dasiki royal blue dake da zanen cheeter a gaban ƙirjinsa zagayensa da ratsin yellow and white colours,har zai sauka sai kuma yayi knocking ƙofarta yace "Diya i'm going out.. Ki fito dan Allah ki bar wannan camping kanki ɗin a ɗaki,zanje gida mu gaisa da Mimi jiya ban samu zuwa ba" shiru tayi masa saboda haushinsa da take ji,har ya ƙaraci maganarsa ya bar gurin kou tari batai ba bare yasa rai ta ji,ya juya ya fita abunsa,da kansa yai driving cikin wani mad black Maybach mercedes benz zuwa Asokoro,manyan gidaje ne na alfarma jere a line,kai baza ma ka iya tantance wanne yafi wani kyau ba saboda yanda kowanne aka zuba basira da tsabar millions of Naira gurin ginashi,gets ɗinsu ma kawai abun kallo ne bare gidan,gaban wani irin makeken get mai kama da mirror ya tsaya yayi horn,sojojin da suke gadin gidan suka taso da sauri dan sun san shi ne mai irin horn ɗin nan suka buɗe masa sunai masa barka da zuwa respectfully,ya shiga yana amsa gaisuwar da suke masa yayi parking ƙasan tent da luxury motoci ke jere reras kamar gurin siyar da su,duk da ba kowacce ake hawa kullum ba,amma duka tass suke suna ɗaukar ido,ya fito ya rufe motar kansa da beret da ya rufe sumarsa da bai da yawa ya nufi balcony,murɗa handle ɗin dake jikin entrance ɗin yayi ya shiga da sallama,wani irin babban parlour ne dake ɗauke da babban hotonsa sai na wata kyakkyawar mata dake sanye da kayan lauyoyi idonta da photo chronic glasses tana murmushi,sosai tai kyau a hoton kamanninsu da Mutallab ya fito musamman idan yai murmushi shima,ganin babu kowa parloun ya nufi stairs zai je sama dan ya san maybe tana aiki ne shi yasa bata samu damar saukowa ba,da sassarfa ya haura ya wuce parlon saman ya buɗe ɗakinta ya shiga da sallama a bakinsa,tana zaune bakin gadonta idanunta sanye da glass gabanta Macbook ne na apple tana rubutu,sanda ta ɗago ta amsa masa sai tayi murmushi tace "yaushe ka shigo?" Yace "yanzun nan" ya ƙaraso ya zauna a hankali kusa da ita yace "good morning Mimi" tace "mrng how are u? Ya weekend da iyali?" Yace "alhmdllh! Weekend ya ƙare" tace "uhmn! Gobe sai office" ya ɓata fuska yace "ni Mimi babu inda zanje gobe" tace "saboda me?" Yace "i hate Mondays" tayi murmushi tace "tou ya za'ayi kenan? Dan ba ka son Monday kuma haka za kayi haƙuri ka fita aiki,tunda ba mutum bane Monday ɗin bare kace za ka hukunta shi" yayi murmushi yana kallon yanda take aiki cikin ƙwarewa yace "Mimi kawo na tayaki" ta girgiza kai tace "um'um! Na gode" hira sukai ta yi kai baza kace Mutallab ne yake surutun nan ba yana dariya,Mimi tana ta aikinta sai can ta ɗaga waya tasa a kawo masu breakfast nan sama,sanda maid tayi knocking Mimi ta bada izinin ta shigo,ta buɗe ƙofar da turanci ta sanar da Mimi an kawo abincin yana parlour,Mimi tai mata godiya sannan ta juya ta tafi ta rufe masu ƙofar,ranan a gidan Mutallab ya yini sai after maghreeb ya yiwa Mimi sallama ya wuce gidansa,tana bashi saƙon ya gaisar mata da Hamdiyya. Kamar yanda yai alƙawari zai zo,after ishaa dai² time ɗin jiya yaro ya shigo kiran Aalima,tayi murmushi tace da Adija "gashi ya zo" da yake ta sanar da Adija komai da yace mata jiya,Adija tace "jeki zansa Auta ta kawo" Aalima ta ɗauki babban sallaya da suka shimfiɗa tsakar ɗakin yai kamar carfet ta fita,cikin irin gift ɗin Fannah ne da take samu daga mutane iyayen yaran da take shiga class ɗinsu a islamiyya ko a musabaƙa,yau bai shigo soron ba har ta shimfiɗa masa daddumar sannan ta leƙo ƙofar gida,yana cikin wani irin dalelliyar mota irin nasu na manyan masu kuɗi,hankalinsa duk yana kan ƙofar gidan,sanda ta fito bata ganshi ba ta ɗan tsaya tai shiru,buɗe motar yayi ya sauko yana kallonta yayi murmushi,Aalima ta fito da idanuwa sai kuma ta bashi hanya ganin ya tsaya gabanta na faɗuwa tace "sannu da zuwa" ya amsa yana tahowa ta koma cikin soron gidan tana cizar lips ɗinta saboda tsoro,yau da yake akwai wutar NEPA a unguwar tar take ganinsa,ya zauna saman sallayar data shimfiɗa,dake a tsorace take sosai da abunda idanuwanta suka gani yau,sam hankalinta taji bai nutsu ba ta daure ganin irin kallon da yake mata ta gaishesa ya amsa yana karantar tsoron da ya gani a fuskarta,yace "Aalima me yake faruwa?" Ta girgiza masa kai da sauri tana ƙirƙirar murmushi tace "babu komai" yace "sure?" Ta gyaɗa masa kai,yayi murmushi kawai yana danna wayarsa da tayi haske,almost 3 minutes sun yi shiru sannan ya ajiye wayar yana kallon Aalima,ita dai fidgeting fingers ɗinta kawai take ta kasa sakewa da zaman,ya tashi a hankali yace "think zan tafi na ga kamar yau ba kya jin daɗi" ta sunkuyar da kanta ƙasa kamar za tayi kuka ta ƙi cewa komai,ya ɗauke pray mat ɗin yana naɗewa zai sake magana,Fannah tai sallama hannunta ɗauke da tray da plates masu kyau da jug ɗan dai² na robber,yana kallonta sosai ya amsa ta sunkuya ta ajiye tray ɗin kafin ta tashi ta gaishesa har lokacin idanuwansa akanta yana kallonta ta tashi za ta tafi yace "Fannah wannan fa?" Ta juyo tana ɗan dariya tace "cewa akai na kawo" daga haka tace "sai an jima" ta juya za ta shige gida,da wani irin murya mai taushi ya kira sunanta "Fannah!" Amsawa tayi ta dawo,ya kalli tray ɗin yace "yi haƙuri ki mayar da shi gida,tafiya zan yi ina sauri ne.." Ta kalli Aalima da keta wasa da hannunta ta ƙi ɗauka tana jira taji ta yi magana,ganin ta yi shiru yasa ta sunkuya ta ɗauka tace "sai an jima" za ta tafi Aalima tace "baki ji ba" tsayawa tayi tana jira tayi magana,Aalima ta tashi tace "ina zuwa please" ya gyaɗa mata kai yace "no worries!" Bin Fannah tayi suka shiga gida tare,da sauri ta samu su Adija a ɗakinsu tace "Yaa Adija wai fa tafiya yace zai yi" Adija tana kallon Fannah data shigo da tray ɗin data aiketa ta kai,Ashey tace "tou ki samu abu ki juye masa ya tafi da shi mana" Aalima tace "tou dan Allah bari na samo container sai a juye.. Auta ki kawo da sauri please" Fannah ta gyaɗa mata kai,kitchen Aalima ta shiga ta duba wasu sauran containers da ba'ai amfani da su ba,tun na wani walimar da akai a islamiyya Director ya bawa Fannah kwangilar yin kayan snacks,da suka yi ragowa yace ta barsu,ta ɗauko ta fito ta basu sannan ta koma gurinsa,yana tsaye har sannan tayi sallama,ya amsa yana ƙureta da kallo,yace "hope babu wani matsala?" Ta gyaɗa masa kai tace "Mmm!" Yace "are u sure?" Tace "ehh!" Yace "but it seems like baki da lafiya? Idan akwai matsala ki kira Auta muje hospital" tayi ɗan murmushin yaƙe tace "a'a babu.. Kaina ne kawai yake ciwo kuma da na sha magani shi kenan" yace "a'a ba shi kenan ba.. Ki bari muje likita ya duba ki,ba na son wani abu yazo ya faru daga baya" tace "in sha Allah babu abunda zai faru,hayaniyar da muka shiga ne ɗazu" yace "hayaniya?" Ta gyaɗa kai tace "munje kasuwa ne ɗazu ina ganin shi ne yasa min ciwon kan" yace "eyyahh! Sannu dear.. Amma kin tabbatar idan kin sha magani zai miki?" Tace "in sha Allah" yace "okay! Idan bai ba ki kira ni dan Allah ki sanar min" tayi murmushi kaɗan taƙi cewa komai,ɗan durƙusawa yayi gabanta yana kallonta sympathetically yace "baki ce komai ba" ta sunkuyar da kanta ƙamshinsa duk ya cikata ta daure tace "tou" yace "good girl.." Sanda ya duba agogon dake ɗaure wrist ɗinsa ya ɗan zaro idanuwa yace "oops! Bari na tafi kada na dameki tunda baki jin daɗi,amma za muyi waya naji ya jikin ki in sha Allah,sannan maganar da nace za mu yi dake ina ga za mu yisa ta waya" ta gyaɗa masa kai kawai,yana shirin yai mata sallama Fannah ta fito da babban leda a hannunta mai kyau ta ƙaraso da sallama tace "wai gashi inji Yayarmu tace dan Allah ka tafi da shi babu yawa" ya kalli ledar kamar bazai karɓa ba ya amsa yana murmusawa yace "kice mata na gode sosai" tayi murmushinta mai kyau sannan ta juya za ta tafi ya sake kiranta "Auta!" Dawowa tayi ta tsaya tana kallonsa da manyan idanuwanta,yace "zo muje zan baki saƙo" ta gyaɗa kai suka fita daga soron,kallonsa ta dunga yi ganin irin motar da ya buɗe gabanta yana faɗuwa ta tsaya daga nesa ta ƙi yarda taje kusa da shi,ya ajiye ledar da ta kawo masa sannan ya kalleta yace "a ina za mu samu yara su shiga da kayan dake cikin booth?" Ta watsa hannuwanta da baby voice ɗinta tace "sai dai almajirai" yayi murmushi yace "su nake nufi" tana sakin ƴar dariya tace "bari na duba can line" yace "okay!" Not too long ta dawo tare da almajirai 3 ƴan matasa,ya kallesu ya buɗe booth ɗin ya fara sauke kayan da suke cikin motar,babban buhun shinkafa sai cartoons na spaghetti da su Indomie,sai kuma drinks da ruwa manya,bayan sun gama shiga da kayan ya basu 1k yace su raba sukai masa godiya suka tafi,wasu manyan ledoji ya ɗebo a back seat guda huɗu,ya shiga soron ya ajiye gaban Aalima da suke magana da Fannah,lokaci ɗaya suka dunga kallon ledojin kafin Fannah ta kalleshi idanunta sun yi rau² ta kasa magana,yana mata wani irin kallo mai wuyar fahimta a ƴan shekarunta yayi murmushi yace "ko dai kema Aalima ta koya maki halinta ne?" Fannah ta sunkuyar da kai taƙi cewa komai,Aalima kallon ledojin kawai take tace "amma kayan sun yi yawa" yace "a'a basu yi ba,kin manta jiya nace zan bada tukuici? And saboda kayan ne nazo da mota ban so a ganni da kaya a hannu.." Ta gyaɗa kai tace "ehh duk da haka" da sauri ya tari numfarfashinta yace "hold on! Ba naki bane sorry na manta bakya so,na su Auta ne" tace "ko na wane ne ma ni dai kayi haƙuri amma kayan sun yi yawa,sannan motar da kazo da shi,zai zama magana a unguwar nan" ya ɓata rai yace "okay! Na dena zuwa kenan ba kwa so?" Ta gyaɗa kai tace "ehh!" Yace "tou shi kenan na gode,sai da safe.." Yana faɗan haka ya fita soron gidan da sauri ya shiga motarsa yaja yai gaba da wani irin speed,Aalima ta juyo ta kalli Fannah tace "ɗauki muje bazai tafi da su ba tunda ya tafi" biyu Fannah ta ɗauka da ƙyar saboda nauyin da sukai,itama Aalima ta ɗauki biyu suka shiga gidan,uban sun kayan da Adija da Ashey suka gani duk yasa jikinsu yin sanyi,suna shiga ɗakin Adija tace "ke mutumin nan kuɗi ne da shi har haka?" Ta gyaɗa kai taƙi cewa komai,Ashey tace "ai da gani ma ba sai kin tambaya ba" Aalima ta zube masu ledojin gabansu tace "gashi injishi naku ne" Adija dai jikinta duk ya mutu sosai tsoronsa ya shigeta,lokaci ɗaya tace ma Aalima "gaskiya i'm scared da mutumin nan.. Anya baza mu sanar da Baffa ba,tunda ya ce ya sanshi?" Ashey tace "gaskiya dai a sanar masa" Fannah dai wucewa kawai tayi ta nemi guri ta zauna tai tagumi,tunda ta fara ganinsa take jin gabanta na faɗuwa,ta kasa gane ma'anar irin kallon da yake mata,me zai sa bayan yana tare da Aalima amma ita take jinta cikin yanayin tsoro,Aalima da suke magana da Adija tace "sai kunga a irin motar da yazo ma" Fannah tai rau² da ido tace "ni wallahi tun daga nan naji kaina yana sarawa" Aalima tace "kuma fa da na tambayesa me yasa yazo da mota yau shi ne yace min wai dama saboda kayan da ya siyo ne bai so a ganshi ya taho da kaya niƙi² aita kallonsa ya san unguwar nan akwai munafukai" Adija da tai tagumi tana kallonsu tace "tou ni dai zan jira Baffa ya shigo yau na sanar masa,duk hukuncin da ya yanke shi kenan" duk sukai na'am da zancen kafin su haɗa kayan guri ɗaya,kaf har ledojin babu wanda suka taɓa suka zauna jiran shigowar Baffa...




           This book isn't for free,normal ₦300 posting 5 days excluding weekend,VIP ₦500 posting daily,SP VIP 1K all via 0060746882-Hauwa Muhammad Usman,access bank. Then u show ur evidence of payment via https://wa.me/+2348165726609. If u are willing to pay,my sister pay it now before the price will go up,after it is completed the price is ₦500.

#Follow
#Vote
#Comment
#Share fisabilillah!
#Asli Smasher.

CIWO A JIKIN WANI!Where stories live. Discover now