💠💠💠💠💠
©®AS-2022.*♡CIWO A JIKIN WANI¸.•💥*
'''(Kᴡᴀʀɪ)'''
Bʏ
*HAWWA__B__KUMO.*
(Rᴇᴀʟ Sᴍᴀꜱʜᴇʀ).💕
*WATTPAD:@REAL-SMASHER.*
*AREWABOOKS:@REALSMASHER.*'''Iɴ ᴅᴇᴅɪᴄᴀᴛɪᴏɴ ᴛᴏ ᴍʏ ʟᴀᴛᴇ ᴅᴀᴅ Aʟʜ Mᴜʜᴀᴍᴍᴀᴅ Bᴀʙᴀ Usᴍᴀɴ (B–KUMO).'''
••••••••••••••
'''Masu buƙatar a tallata hajarsu u should contact me ta number na,kou kuyi magana da ni kai tsaye ta https://wa.me/+2348165726609.'''04
#Fannah
Mutumin da aka kira da Alh Sardauna yace "Falaki taso dan Allah kai ne ɗan unguwa" saurin tashi Falaki yayi yasa takalminsa ya tsallako titin while yana cewa "ina za taje ne?" Alh Sardauna yace "kai dai duk ba wannan ba,zo ka duba yarinyar nan kaga kou ka santa?" Falaki da ya ƙaraso ya kalleta da kyau lokaci ɗaya yace "a'ah! wannan ai ƙawar ƴata ce Nana Hafsah.. Na santa wallahi babanta maƙocina ne,mutumin ma ka sanshi wani Alh Umar,yana yawan zuwa majalisar mu sosai ayi hira" Alh Adamu yace "ba dai Harkas ba?" Falaki yace "shi kuwa" Alh Adamu yace "Alhamdulillah ta kwana gidan sauƙi" yana riƙe da hannunta yace "muje dan Allah ka rakani mu mayar masa da ita,ina ga ba'a san ta fito daga gida ba" Falaki yace "tou bismillah muje,dama ina son keƙawa gida.." Tunda ya fara janta take binsa kamar raƙumi da akala har suka iso ƙofar gidansu,Alh Sardauna yai sallama soron gidan da yake bai da zurfi,Falaki da suke tare yace "bari na shiga na fito" Alh Sardauna yace "alright! Hope ba zaka daɗe ba?" Yace "ehhh yanzu zan fito" Alh Sardauna yace "a fito lafiya" bayan ƴan mintuna wata ƴar budurwa da baza ta wuce 19yrs ba ta fito gidan,itama fara ce kamar yarinyar da suka rako sai dai bata kaita kyau ba,ganin babban mutum ta gaishesa,ta kalli yarinyar da yake riƙe da hannunta lokaci ɗaya ta wani zaro ido tace *"FANNAH!* Ina kika tafi? Daga tashinki kiyi fitsari shi ne kika fita?" Alh Sardauna yayi murmushi yana kallon mai maganar yace "ƴan mata babanku yana nan?" Ta girgiza masa kai tace "bai dawo ba" yace "okay! Idan ya dawo kice masa Alh Adam Sardauna yana gaisheshi" ta gyaɗa kai tana kama hannun Fannah tace "zo muje ki kwanta,banza me magagin bacci kawai" ɗan dariya Alh Adam Sardauna yayi yace "ke ya sunanki?" Tace "Aalima.." Yace "maa sha Allah.. Aalima ku dunga kula da ita a dena bari tana fita da dare,tunda kun san tana da nauyin bacci a samu wani ya dunga rakata,saboda duniya babu gaskiya,kada wani abu ya sameta,though ba fata muke ba" Aalima ta gyaɗa kai tace "tou! In sha Allah" 5k ya ciro aljihunsa ya bata yace "ga wannan babu yawa ku sai sweet" Aalima ta girgiza kai tace "a'a ka barshi mun gode" yace "karɓa ai ku ƴaƴana ne,kou dan ban taɓa zuwa gidanku ba?" Ta girgiza kai tana sakin murmushi,yace "karɓi tou idan babanku ya dawo ki tambayeshi shi ya sanni ai" hannu biyu tasa ta karɓa tace "angode Allah ya saka da alkhairi" yace "babu komai ku shiga gida" tace "tou" tana juyawa ya bisu da kallo,a zahiri Aalima ba daga nan ba itama mai kyau ce,sai dai idan Fannah tana kusa an gama magana,yarinya ce amma Allah yai mata kyau sosai²,duk inda mace take ta kai har tana neman fi ma a kyaun fuska da surar jiki,Falaki da tun zuwansu ya shiga gidansa ya fito yaga sai murmushi Alh Adam Sardauna yake,ya kalleshi yace "tou ya akayi ne? Akwai latest?" Alh Adam Sardauna yace "kai haka mutumin nan yake da kyawawan yara ban sani ba?" Falaki yayi wani dariya yace "wallahi banda dai kajin maƙota ne nima da tuni na jima da dafa su a tukunyata,tou wai ina fita hakkin maƙotaka ne" Alh Adamu yace "ehhh! Dama ku idan kun ɗaga ƙafa babu laifi,mu dai mu ɗaga ɗin ne yake da matsala.. Yanzu duk bama wannan ba shi Harkas ya san akwai irin ɗanyen jinin nan a gidansa yake haɗa mu da tsofaffin guzumaye?" Falaki ya fashe da wata dariyar mugunta yace "a'a tou wannan kuma sai kayi magana da shi" Alh Adamu ya wani haƙiƙance yace "wallahi zan yi masa,kou ɗaya cikin na gidansa ne ya bamu mu taɓa,wancan duk tsofin hannu yake nemowa,ka san shi kuma inji yana son service,amma idan da hali ni sai na aure ɗaya ciki kawai na samu ta fita zagayen duniya.." Suna ta hira da dariya har suka koma majalisa. Suna shiga gida sai da Aalima ta kai Fannah tai fitsari sannan ta kama hannunta suka shiga ɗakinsu,wasu ƴan mata ne guda biyu kwance kan ƙatuwar katifa,kowa da inda take sai dai duka karatun novels suke a waya,a hankali suka juyo suka kallesu lokaci ɗaya suka kalli juna,ɗaya tana dariya ta nuna Fannah da idonta ke cike da bacci tace "a ina kika samota? Yau kuma wace hanyar tabi?" Aalima tace "kema Yaa Adija kin san halinta kika ce taje tayi fitsari,Allah ne fa ya kiyaye wani abokin Baffa ya ganta ya dawo da ita gida,kinga ma har ya bamu 5k musai sweet" wani saurin ƙwace kuɗin Adija tayi tace "dallah can kiyi ƙasa² sai kin janyo Baffa ya shigo yana tambayar ina kuɗin suke,kin san dai karɓewa zai babu abunda ya damesa,kuma da safe ya tambayi abun kari" Aalima ta turo baki tace "tou ai baya nan fa bai dawo ba" Adija tace "dallah ki rufawa mutane baki,kin san shi dai ana maganar nan yanzu ya shigo wallahi ƙwacewa zai babu ruwansa,da safe idan yaga babu labari yai ficewarsa mu ta shafa muci ko mu mutu bai damu da cikinmu ba" ɗayan budurwar ta taɓe baki tace "ai ni na rasa wane irin sabo Baffa yayi da kuɗi da ko a zuci ka ambacesu sai yace "na ji ana maganar kuɗi a fito da su ko nayi caje" Adija da Aalima suka fashe da dariya,Adija tace "gaskiya Ashey baki da dama" Aalima tace "yanzu Baffan kike kwaikwayon yanda yake yi?" Ashey ta juya ido cike da tsoro tace "Aalima stop mentioning his name,idan ya shigo Allah zance bansan da wa kike ba" Adija da Aalima suka fashe da dariya har da ƙyaƙyatawa,Fannah kam tunda ta samu guri ta kwanta bata sake sanin me suke ba,sosai suka raba dare suna ta hira,yayin da fiye da rabin maganar tasu ya ta'allaƙa kan maganar Baffa da kuɗi har dai suka gaji suka kwanta bacci.
BINABASA MO ANG
CIWO A JIKIN WANI!
Romance...Shin me yasa mahaifi zai mayar da ƴaƴansa tamkar hannun jarin da zai tsammaci samun riba a ko da yaushe? '''ƊANƊANO..''' •••Hawaye sosai suke saukowa idonta da wani irin Baby voice tace "ban yi sallama da su Yaa Aalima ba" Hamdiyya dake ku...