TANA TARE DANI

58 0 0
                                    

TANA TARE DA NI
BY
MIEMIEBEE

PAGE 4

 
       Cikin kuka tace, “dan girman Allah bawan Allah kayi hak’uri I beg of you please.” Jikinta se rawa yake tana hawaye. “Bawan Allah dan Allah kayi hak’uri I'm just 15 ba abinda zan iya baka have mercy on me please dan Allah.” Ko k’adan be saurareta ba hijabin jikinta yasoma k’ok’arin cirewa. “Wayyo Allah Mami na! Baba! dan Allah kuzo ku taimakeni! ihu take sosai.”

     Hannu yasa ya rufe bakinta. “Duk mata haka kuke, mesa zanji tausayinki? Data gudu tabarmu ta tausaya mana neh? Why will I have mercy on you? I hope you tell her abinda zan miki yanzu saboda itama ta d’and’ana little daga cikin bak’in cikin data sanyamu time da ta tafi ta barmu” Yana d’aga hannu daga bakin nata ya yaga hijabin nata into two. Ihu ta sake sakarwa “bawan Allah dan Allah kayi hak’uri karka lalatani dan girman Allah, kaji tausayi na I'm just 15 years dan Allah ka rufa min asiri karka b’ata min future”

     “Data tafi ita taji tausayin mu ne?”

       A rikice bakin ta na rawa tace, “ww..wa ce? Ni bansan wacce kake fad’a ba bawan Allah ban tab’a ganinka ba seyau kayi hak’uri dan Allah, karka lalata ni.” Be saurareta ba ya yaga kayanta. Nan ta shiga tare k’irjinta kuka sosai Fannah takeyi tana rok’an wannan bawan Allah'n haka ba tausayi ba inani yayi raping (fyad’e) nata.

     Tun tana iya jure zafin har ta sume wajen, kaca-kaca yayi da ita sannan ya fice yabarta ruwan sama ma dukan sumemmiyar jikinta. Shi kansa besan ya akayi ya isa gida ba a daren, kawai ganin kansa yayi bisa kan gado.
    
             A hankali ya bud’e blue eyes nasa wansa Shettima yagani a kansa. Tunanin meya faru yakuma yake nan ya soma lokacin da aka soma ruwa yace dasu Baana ze tafi sukayi k’ok’arin hanasa amman ya k’i jinsu ya hau tafiya can cikin wata lungu.. Wata lungu... Daga.. Can kwata kwata seya kasa tuna meya sake faruwa.

         “Anas how are you feeling? Sanda na fad’a maka karka bi su Baana kak’i kasan yadda ruwan saman nan yamaka duka kuwa? In akayi wasa seka kamu da mura.” cewar Shettima fuskarsa a d’aure

     “Ina Abuu?” Anas ya tambaya. “Ka gode wa Allah be ganka ba sanda nashigo dakai nan. Anas fisabilillahi mesa baraka rungumi k’addara ka manta da zancen Ummimi (mahaifiyarsu) a rayauwarka ka yafe mata ba? You're blaming yourself for her mistakes, misleading your life in the process. Haba mana Anas. Saboda Ummimi kasoma shaye shaye me haka please? Yanzu saboda ita ka kusan kashe kanka, abinda tayi ya riga ya wuce se mu rungumi k’addara mu barta da halin ta.”
  
        “No Shettima I can never do that, tariga ta juya min rayuwa, my life can never be normal kamar yadda kakeso, I can never move on barni haka kawai inta misleading rayuwar nawa har zuwa sanda zan mutu. Images of yadda ta tafi ta barmu will never leave my head, they are stuck in it forver”

       “Anas wai kai mesa bakajin magana ne ko dan ni k’aninka ne kafisan babba ya maka magana? Bari Abuu ya dawo I think is about time yasan gaskia shima, I've been keeping your secret for how many years now? A ganina with time zaka mance komai amman tunda you are not ready to change, tunda baka iya rungumar k’addara ba zan fad’a wa Abuu komi idan ya dawo.”
             Sede daya juyo ya kalli Anas yaga ko k’adan ma hankalin sa ba a gunsa yake ba, yayi nisa cikin duniyar tunani.

     “Anas?” Ya kira sunansa. Shiru Anas yayi be amsa ba dan haka ya d’an jijjik’a sa. “Yarinyar...” Anas yace fuskarsa cike da damuwa. Se yanzu ya tuna yaga wata yarinya acikin lungun. Amma sam ya kasa tuna ya fuskarta take ko fara ce ko bak’a ko kyakkyawa ko munana, ko doguwa ko gajeriya shide yasan yaga yarinya cikin lungun.

         “Wata yarinya kuma Anas? Yau kai ke kirar mace cikin gidan nan?”

     “Yarinyar Shettima ina take?”

Tana tare dani by miemie bee Where stories live. Discover now