TANA TARE DA NI
BY
MIEMIEBEEPAGE 3
FANNAH‘kauyen Bama dake jihar Maiduguri, Borno.
Kyakkyawar budurwa ce zaune cikin wata ‘yar k’aramar d’aki bisa gaban wata ‘yar madubin da aka mak’ala a jikin bango. Ba komai bane a d’akin illa katifan dake shimfid’e a k’asa seda bakunan sa kaya da leather carpet ciki. Ba shakka basu da arziki. Dududu wannan ‘yar budurwa baratafi 15 years old ba. Tanada haske sosai, da sirirn hanci dakuma plumpy lips, idanunta ba laifi ‘yan manya ne dadai. Gashin girarta acike yake mekyawun gaske ba ruwanta da zana artificial gira [ba erinsu ni ba;( ] in kuwa aka k’are mata kallo sosai za’a ga alamar had’ewar girar ta guda biyu gu d’aya sede be munanta taba hasali kyau ma yak’ara mata. Gashin idanunta a cike suke kuma dogaye, saje ne a fuskarta kwance luf-luf wane na miji (kaman nawa, lol) gashin kanta dana girarta sun had’e dan yawansu. Hannunta gashi ne a kwance dogaye masu mugun kyau.
Siririya ce de tanada tsawo daidan shekarunta, tana sanye da wata atamfa maroon da torches na white and green, se murza wata ‘yar jan baki pink take a lips nata hankalinta kwance da anganta ansan batada matsala. A lokacin da wayarta k’irar Nokia Asha dake kan cinyarta tayi k‘ara, a hanzarce ta duba tana ganin sunan daya bayyana kai _Ya Ahmad_ tayi murmushin jin dad’i sannan ta bud’o sakon ta karanta kamar haka;
_my Fannah I'm outside waiting for you yanzu shigowa na gari ko gida ban lek’a ba just wanted to see you_
“yeyy!!” Ta fad’a a fili tana murna. Data gama sa jan bakin ta shafa powder tareda sa kwalli a fararen idanunta take ta dawo wata balarabiya. A garin mike’wa d’an kwalinta ya since ya fad’i k’asa tare da ribbons data k’ukk’ula gashin nata dashi. Fans ko kunsan ya gashin buzayen Maiduguri yake? Erin bak’i k’irin me santsi da tsawo kamar haukan nan? Haka gashin wannan ‘yar budurwa yake.Ni kaina miemie dana gani sanda na tsorata dukda cewar ita kad’ai ce a d’akin hakan be hanata yin saurin tattara ribbons d’in gu d’aya da sauri ba tasoma k’ok’arin faka gashin nata gu d’aya saidai dan cikar gashin ta kasa, hannun nata suna nan sirara ba fad’i ga uwa uba gashi har tsakiyar bayanta. Kamar wacce zatayi kuka tafito d’akin “Mami! Mami!” Shiru kukeji wani mutum ne wanda bara’a kirasa da dattijo ba danko befi shekaru irin 44-45 dinnan ba ya lek’o daga wata d’aki wanda ya kasance opposite daga d’akin da Fannah tafito da alama mahaifinta ne dukda cewar basu kama kuwa. “Fannah uwata ya akayi? Tsaya mesa kike yawo da kanki a bud’e haka?”
Kamar wacce zatayi kuka tace, “Baba ribbon d’in ne yafita kuma nakasa d’aure gashin, Mami nake nema ta tayani.”
“Shine zakiyi kuka uwata?” Cewar mahaifin nata “Mami batanan tashiga mak’ota.”
“To baba Ya Ahmad fa yazo yana jirana a waje ko gida be wuce ba ya zosa nan.”“Oh! Keda Ahmad d’inkin nan se Allah. Ina Afrah da Aiman toh?”
“Sun tafi islamiya Baba.”
“Yoh! Kekuma fah?”“Kai Baba wai yanzu so kake kace ka manta sauk’an nawa? Abinda har Hajji kaje da kujerar da aka bani danayi na biyu.” “Haka fah, taho to in kama miki kan.”
“ Yawwa Baba na.” Da gudu taje ta zauna gabansa shima sanda yayi dagaske sannan ya kama uban gashin nata gu d’aya. Banda tsawon gashin gu d’aya. Wawan cika ne dashi saisa Fannah batta iya kamawa. “Toh nagode Baba.” “Yawwa ‘yar akbarka se ganin Ahmad ko?” Ta giad’a masa kai. “Ki sa hijabi fa tukun kuma kice ya gaishe min da mahaifinsa naji wai ya d’anyi rashin lafiya kwana biyu kuma ban samu na lek’a sa ba.” “Toh Baba zan fad’a masa in shaa Allah.”D’akinta takoma tad’au wata maroon hijabi wanda ya sake ciro da hasken ta tasa, tare da d’aukar wayarta sannan tafito waje idanunta suna sauk’a kan Ahmad nata ta sakar dawata murmushin jin dad’i. Ahmad saurayi ne me k’imanin shekaru 23. Chocolate skinned yake, yana da kyau dadai gwargwado gasan murmushi. Tsayyayen na miji ne masha Allah!