TANA TARE DA NI
BY
MIEMIEBEEPAGE 8
Kasa cemasa komai tayi, kallonsa kawai take hawaye na gangarowa kan kumatunta, kuka ne yafi k’arfinta juyawa tayi tashiga gida da gudu ta tsaya daga wata lungu ta share hawayerta sannan ta k’arasa ciki. Mami da Baba ta tarar zaune yadda ta barosu. Basu ce da ita komai ba dan haka tashige d’akinsu da Afrah ta fashe da kuka bata san da wanne zata ji ba da rabata da akayi da budurcinta martabarta na k’arfi da yaji ne kokuma da auren wannan monster me suna Farouq tun be aureta ba ma yasoma mata rashin mutunci yana zaginta bale ace in sunyi aure, kwata kwata baida slightest regard mata.Bada jimawa ba Mami ta aike Afrah shago siyo man giad’a tun kafin Maghrib yayi gudun kar abinda ya faru da Fannah yakuma samun Afrah. Afrah ne tashigo d’aukan hijabi a d’akinsu, Fannah dake kwance a kan katifa da Qur’ani tana karatu ta d’aga kai tare da tambayarta. “Ina zakije haka?”
“Shago fa Mami ce ta aikeni siyo man giad’a.”
“Okay, jirani muje tare nagaji da zama nan shiru ni kad’ai.”
“Toh sanya hijabinki muje Ya Fannah.” Nan Fannah tasa hijabi suka fito tare, “ya haka ina zaki Fannah?” tambayar Mami ga Fannah.
“Zan bi Afrah ne Mami nagaji dazaman cikin.”
“Toh Allah kare dan Allah in har babu anan shagon Ya Wakil dana mak’otansa karkuyi nisa ku dawo gida kawai, kunji?”
“In shaa Allah Mami” cewar Fannah sannan suka fice. A shagon Ya Wakil suka samu man giad’an sun jiyo zasu fice sega yaran unguwa sun taru suka soma wak’a“Fannah kariya me bin maza Fannah kariya me bin maza.”
Hawaye tasoma yi bata tab’a tsammanin zatayi witnessing rana kamar ta yau ba, ranan da za’a ce tafita waje ana binta ana zaginta me bin maza.
“Ku wai bakuda hankali ne?” cewar Afrah “wanj irin ‘yan iska ne ku? Wallahi in baku bar nan ba zan jefe wannan munanan bak’ak’en kankun da dutse, jahilai kawai. Bara ku matsa bane?”
Ko ajikinsu ma magana ake masu wak’an su suka cigaba dayi. Mari wani ya sake ma babban cikin nasu Tasss! Kukeji a fuska take ya soma kuka saurayin na juyawa suka had’a ido hud’u da Fannah take ta kau da kanta. Kolar rigarsa Ahmad ya rik’e da hannu d’aya “kanajina in sake jin ka kira Fannah ko wata mace a garin nan da kariya kaga abinda zan maka ba kai kad’ai ba dukanku nan” ya nunasu da yatsa. “Kunjini ko bakuji ba?”
Baki na rawa babban yace, “munji dan Allah kayi hak’uri.” Ahmad na sakesa suka kwasa da gudu suka bar wajen. K’arisowa gabansu Ahmad yayi “Fannah kiyi hak’uri kibar kuka dan Allah, karki bari maganan yaran nan to get to you.”
“Ya Ahmad dan Allah kayi hak’uri” Fannah tace tana hawaye hannu kawai tasa ta rufe bakinta ta ruga a guje se kiran sunanta Ahmad yake ko sauraransa batayi ba. Juyawa yayi ya kalli Afrah da itama idanta suka cike da hawaye. “Afrah kiyi sauri ki bita kar wani abu ya sameta. Tell her tayi hak’uri ta rungumi k’addara in shaa Allah, Allah ze sak’a mata kuma kice mata I will never stop loving her koda ban aureta ba, da santa zan mutu kice mata tayi hak’uri, ina kan mata addu’a.” Kai kawai ta giad’a masa tabi bayan Fannah da gudu.Tana isa gida ta tarar da Mami a tsakar gida se safa da marwah take. “Mami ga man giad’an.”
“Afrah meya samu Fannah tashigo tana kuka ta rufe k’ofar d’akinku nayi nayi da ita ta bud’e tak’i wani abu ne?”
“Mami wallahi Ya Afrah tausayi take bani, yanzu fitan mu almajirai suka taru suna mata wak’a suna kiranta da munanan suna Mami.” Ta k’are maganar tana hawaye.“Allah sarki Fannah” cewar Mami itama tana hawayen, “Afrah inda zan iya karb’e pain da Fannah ke feeling danayi wallahi, it hurts me seeing my daughter in a horrible situation like this kuma ba abinda zan iya mata.” Hannu tasa ta share hawayerta addu’a zamu mata Afrah ko a islamiya ki fad’awa Malamanku su sata cikin add’ua kinji?”
“In shaa Allah Mami barinje in sameta.” Tana tashi taje ta k’ofar d’akinsu tun daga bakin k’ofar take jin sautin kukan Fannah. “Ya Fannah dan Allah kibar kukan nan batada amfani, addu’a zamu dage dayi, bud’e k’ofar kinji? Ya Ahmad yabani sak’o in isar miki, yi hak’uri ki bud’e.”