TANA TARE DANI 6

46 1 0
                                    

TANA TARE DA NI
BY
MIEMIEBEE

PAGE 6

  
          “Ni ba abinda nake nufi ba kenan, my point is adena kirar ‘yata kariya. Alhj Suleiman kai da d’anka zaku iya tafiya, abincin wani gub’an wani kamar yadda ka k’yamaci Fannah haka wani zeji kamar ya mutu mata. Ahmad Allah had’aka da rabonka, ka kasance masoyin Fannah na hak’ik’aamman there is nothing you can do now dole ka hak’ura kabi umarnin mahaifinka, in zakumin uzuri, I need to see my daughter.” Yana kaiwa nan ya shige d’akin Fannah.

       Idanun Ahmad take suka kad’a sukayi ja, koda wasa be tab’a tsammanin akoi abinda ze shiga tsakaninsa da Fannah ba, yana santa fiye da yadda yake san kansa. “Abba dan Allah kar muyi haka, wallahi nasan Fannah is innocent.”
      “Ahmad kaji na rantse maka kasake min maganan wannan kariyan zan tsine maka, ai saisa akace a bincike mutum shiru-shiru. Maza mu wuce gida, Alhj Khaleel nagode sosai Allah bar zumunci.”

      “Bakomai Alhj Suleiman, ita gaskiya haka take daga k’in jinta kuma se b’ata. Allah rufa mana asiri.” Da fad’in “ameen” Ahmad dake hawaye shida mahaifinsa suka bar asibitin. Suna ficewa ya Khaleel ya b’alle da dariyar mugunta. “Ai dama nace in shaa Allahu ‘yarka barata auri wani ba inba d’ana ba. Kyakkyawar mace me addinin muslinci Farouq ya cancanta kuma ba kowa bace illa Fannah saboda haka tana warkewa zanje in samu Baba (mahaifinsu) in masa magana.”

      Gida ya zarce yana isa ya soma k’olla ma d’ansa Farouq kira. “Farouq! Farouq! Zo nan” alokacin ya zauna kan wata tabarma bada jimawa ba Farouq d’in yafito da angansa an ga d’an iska wata shegiyar crazy wando ne a jikinsa da singlet. Ba laifi yanada kyau dadai dakuma tsawo. Bayan ya zauna yace, “gani Baba.” Ya Khaleel ya kallesa sannan yace, “d’ana ka kwantar da hankalinka Fannah ta kusan zama taka, Fannah taka ce! Yanzu ana sallamota daga asibiti zan wa kakanka magana.”

       “Baba dagaske!” Farouq ya tambayi mahaifinsa cike da jin dad’i. “Da dana ce maka seka auri Fannah ka d’au wasa nake maka ne? Ai Fannah taka ce.”  “Kai Baba na gode amman da akoi matsala Baba.”
      “Ina jinka Farouq mecece matsalar yanzu in warkar maka da ita?”
       “Fannah... Bata so na Baba ko kad’an zan iya irga sau nawa muka tab’a magana da ita, sam bata sona ta tsane ni.”
      “A da kenan...” Ya khaleel ya fad’a yana murmushin mugunta.
      “Ban gane a da ba kenan Baba.” Farouq ya fad’a a little bit confused.

      “A da datake da tabbacin cewa akoi masu santa amman banda yanzu data rasa budurcinta, kap ba na mijin da ze so ta yanzu, ta zamo tamkar k’azantar da akeson a yasar ne yanzu. Ko baka gane ba?”
      “Sosai na gane Baba na gode.”
    
    ***
       Afrah ce tsaye kan Fannah tana kallonta hawaye suna gangara kan kumatunta a yayinda Baba da Mami suke zaune kan wata kujera, Aiman kuwa an mata shimfid’a a k’asa tana bacci. Hannu Afrah ta mik’a dan ruf’e Fannah mekyau da  bargo taga kamar Fannah tad’an motsa.

     “Barin je in kama ruwa” cewar Mami “ina zuwa yanzu.” Kai Fannah ta kad’a a hankali again. “Ya Fannah! Baba! Mami! Fannah tayi motsi.” Kafin su Mami su k’ariso Fannah ta soma bud’e ido a hankali tagama bud’e idanun nata ta sauk’esu kan family’nta dake tsaye a kanta suna murmushi da zubda hawaye a lokaci d’aya, murmushin tayi k’ok’arin mayar masu da k’yar.

     “Ya Fannah!” Cewar Afrah
     “Fannah! ‘yata” cewar Mami.
      “Mama na!” Cewar Baba.

      Kallonsu take a hankali cikin wata dashasshiyar murya tace, “Mami, Baba, Afrah.” Dad’a k’aruwa murmushin fuskarsu yayi Baba yace, “Afrah jeki kira nurse kice mata Fannah ta farfad’o.” Bayan minti d’aya Afrah dawata nurse suka shigo d’an dube-dube tayi wa Fannah sannan taceda su Mami “Alhamdulillah condition na ‘yarku is stable. Inda hali a had’a mata tea me kauri tasamu tasha se abata magunanta. Excuse me.”

Tana tare dani by miemie bee Where stories live. Discover now