TANA TARE DANI 7

44 1 0
                                    

TANA TARE DA NI
BY
MIEMIEBEE

PAGE 7

        *FANNAH*

      _3 days later..._
   
     Kwanan Fannah uku a asibiti tasamu k’arfin jiki aka sallamesu, ayau suke shirin dawowa gida, Alhamdulillah jikin nata da sauk’i sosai saboda anti-biotics datake sha masu k’arfi ne sosai. Baba ya sayarda shanunsa da shi ya samu ya biya kud’in asibitin ta da kuma na magunanta.

     Daidai sun sauk’o daga keke na pep kenan se ga irin almajiran unguwan nan sunzo sun tsaya gabansu.

         “Fannah! Dama ashe ke d’in kariya ce me bin maza, sekitayin abu kamar ‘yar malam saliha to Allah ya tona miki asiri tunda saurayi yayi miki ciki.” Hannu Mami ta d’aga ta wanke sa da mari. “In na sake jin wannan munanan kalamu daga bakinka kaji na rantse seka kwana a asibiti, bakai kad’ai ba dukanku nan. Fannah ba kariya bace abinda ya sametan nan k’addara ce. Maza ku fice min daga kallo.”

    Baya sukayi kad’an sannan suka soma wak’a “kariya! Kariya! Fannah kariya Fannah kariya!” Hannun Fannah kawai Mami taja suka shiga ciki a yayinda Baba ya koresu.
    Kuka Fannah keyi sosai. “Yanzu shikenan Mami kallon kariya za’a na mun? Shikenan rayuwata ta lalace Mami.”
        “Shhh karkiyi magana haka, karki saurare wad’ancan almajiran basu masan me suke fad’i ba.” Hugging nata tayi har sanda Fannah tayi shiru.

      Da yammacin ranar around k’arfe 4:45PM Ya Khaleel da d’ansa Farouq suka shigo gidansu Fannah. Mami da Afrah suna had’a girkin dare suka masu sannu da zuwa, ba abinda Afrah ke masu se harara. “Ke Afrah jeki kira min mahaifinku dakuma ‘yar ku kariyan can.” cewar Ya Khaleel.

           “Kawu Khaleel bamuda kariya a gidan nan.” Ta fad’a stubbornly.
          “Ke ni keke gaya wa magana? Iyye?”
     “Kawu kayi hak’uri Afrah kibasa hak’uri kije ki ma Babanku da Fannah magana.” A sanyaye ta mik’e taje ta kira Baba sannan takira Fannah a tare suka fito. Fuskar Baba a tamk’e ya zauna kan tabarman da Ya Khaleel da d’ansa ke kai ba tare da ya musu magana ba.

       “Ina wuni kawu?” Gaisuwar Fannah.
        “Yawwa sannu an sallamoki kenan. Se a kiyaye aukuwan na gaba kafin wani saurayin yasake fiad’e ki.”

     Har tsakiyan kanta tajiyo wannan kalamai ba ita kad’ai harsu Baba da Mami da Afrah. “Ya Khaleel in kasan batun daya kawo ka gidana dan kaci zarafin ‘yata ne dan Allah kayi hak’uri na had’aka da Allah ku tashi ku tafi.”

       “Ba seka koremu ba yanzu zamu tafi. Magana d’aya biyu na zoyi nan saboda haka nakeson ku bud’e kunnuwanku ku saurareni. Kunfi kowa sanin yadda ake k’yamatan kariya a gari, ba uban da ze so d’ansa ya auri macen da batada budurci. Fannah kuwa ‘yata ce dukda abin kunyan da ta mana ina san ta saboda haka zan bata wa d’a na Farouq.”

     “What!?” Baba yayi exclaiming.

     “Bari na gama mana k’ani na. Na riga nayi wa Baba magana kuma ya goyi bayan zancen d’ari bisa d’ari bawai nazo nan bane in baku choices saboda bakuda choice inbanda ku yarda mu rufa wa kariyarku asiri dan na tabbata kap garin nan bame san aurenta. Kinji ai Fannah? Ga Farouq nan mijinki, kina k’are secondary ze rufa miki asiri ya aureki zaki iya gode masa saboda wannan jahadi yayi. Auren kariya ba wasa bane.”

     D’ago jajyen idanunta tayi ta azasu kan Farouq dake ta mata murmushi. Hawaye se gangara suke kan kumatunta, kuke take sosai. Tasani a yanzu kam kamar yadda Kawu ya fad’i ba na mijin da zeso aurenta saboda ta rasa budurcinta martabatar ta, amman duk da haka gomma ta mutu batai aure ba data auri Farouq. Farouq baida tarbiyya ko kad’an d’an iska ne ba aikinsa se bin mata Allah kad’ai yasani ko baida cutar k’anjamau ma. Ba yadda za’ayi ta auresa.

Tana tare dani by miemie bee Where stories live. Discover now