TANA TARE DANI

260 8 0
                                    

TANA TARE DANI
  BY MIEMIEBEE

PAGE 1

ANAS
     K’auyen Bama dake jihar Maiduguri, Borno.

            Da yammacin ranan Asabar misalin k’arfe biyar da mintuna aka. Ruwan sama akeyi me ni’iman gaske, ga wani iskan dake hurawa me kad’a bishiyoyi da flawoyi, ko ina ya d’au sanyi. Tsit kukeji a garin, yara da manya, maza da mata kowa na cikin gdajensu, masu tafiya akan hanya kuwa sun faka gu d'aya, motoci dabasu fi a k’irga ba ke wucewa time-to-time. Can k’ark’ashin wata bishiyar ’yim na hango wasu samaruka guda hud’u wanda barasu gaza kuma barasu fi shekaru 17-18 ba.

        Daga nesa nake, amman hakan be hana ni tantance kyakkyawan cikin wad’annan samarukan ba. Wani kyansan ma sanda na gama k’arisowa, fari ne yellow shar da gashi kwance a duk sassan jikin d'an Adam da akasan na tsirar da gashi. Gashin kansa nada yawa saidai bawai afro tayi ba saboda tsantsin gashin bai tsayuwa, luf-luf yake kwance a kansa, bak’i k’irin yana yalk’i wane yasha mai.

      Saje ne kwance akan farar fatar fuskarsa wanda da ace yanada gemu da sun had’e. Gashin girarsa ba a cike take erin thick dinnan ba, silky yake a kwance d’an siriri wane yayi carving nasu. Dogayen eyelashes nasa wanda suke kallon k’asa santsi ne dasu. Bashida dara-daran idanunu, idanun nasa suna nan madaidaci da k’wayoyin idan nasa light blue wane na bature.

          Nasha jin ana cewa a Africans akoi masu blue eyes ban tab’a yarda ba sanda naga wannan saurayi. Hancinsa ma ba dogo har bakan nan bane, daidai yake cikin 'yar fuskarsa wanda yakasance shi ba dogo ba bakuma gajere ba. Bakinsa light red yake d’an madaidaici cikin fuskar tasa. Dukda cewar ya d’aure fuska hakan be hana dimple na kumatun damarsa lotsewa ba wanda babu hakan a na hagun.

   A zaune yake amman hakan be hanani tantace tsawonsa ba, dogon na miji ne, yanada faffad’ar k’irji duk da cewar siriri ne. Ofcourse ana cewa d’an Adam bai cika goma but za’a iya kiran wannan saurayi hallitar data cike goma bansani ba halan ya gaza ta hali amman inde ta hallita ne kam masha Allah, Allah yabasa, ban tsammanin akoi macen da zata ga wannan saurayi bata kuma kallonsa ba. I mean ba mace kad’ai bama kowa in all.

      Sanye yake da mint blue T shirt wanda ya mugun amsar farar fatarsa, jeans na jikinsa kuwa tad’an kod’e alaman tasha ruwa. Rik’e yake da kara a hannunsa yana wasa dashi da siraran yatsunsa wanda suke nan kan ba na miji ba.

      Gefensa saurayi ne me kama da shi sak, saidai komi na wannan kyakkyawan yafi nasa, kuma shid’in be kai kyakkywan fari da k’war jini ba, duk yadda akayi wansa ne na jini saidai na kasa tantance wane babba cikinsu. Sauran biyun k’arshen kuwa chocolate skinned suke, saidai still d’aya yafi d’aya haske.

     “ANAS na mata kenan!” Cewar d’an bak’i na k’arshen tare da kewayo da kallonsa kan kyakkyawan cikin nasun wanda nake da tabbacin shine ANAS d’in yana mai murmushi wanda hakan ya bayyano da brown teeth nasa, tabbacin kanuri ne shi kenan. “Uhm uhm fa BAANA!” cewar me haske na gefen d’an bak’in da yayi magana yanzun kenan. BAANA yace, “ah’ah barni in tsokanosa de.” Shide kyakkywan nasu da ake kira da ANAS be tanka saba, hasali, yi ma yayi kamar besan ana magana a gefensa ba se b’antare karan dake hannunsa yakeyi yana kallon yadda ruwan saman ke sauk’owa.

        Wanda nake kyautata zaton wan Anas d’in ne yace da d’an bak’in gefen nasa “barsa de KASHIM, neman magana yake yau gun ANAS.” KASHIM ya karkato da kallonsa kan BAANA “aikam naga alama rad’au a fuskarka, kuma wallahi kasan inya shak’ure ka bame k’wato ka, kasan halin mazan namu. Ko mata ma bai ragar masu ba bale kai,” ya d’an yi shiru sannan ya k’arisa “gardi” Yafad'a cike da gatsine.

     BAANA yace, “hummm zagen dai, naga kap nan gardawa ne har Shettima k’anin mun ma(k’anin Anas knan)” Duk suka k’yalk’yale da dariya illa shi wannan kyakkywa da suke kira da Anas wanda yayi burning face sekace besan me kalmar dariya ba.

Tana tare dani by miemie bee Where stories live. Discover now