TANA TARE DANI
BY
MIEMIEBEEPAGE 2
Tafiya suke a sahu d’aya, tsayin nan nasu na nan d'ai da kad’an Anas ya d’ara Shettima inba wai ance ya da k’ani bane za’a zata agemates ne. Daidai lokacin da suka yanko wata corner kenan Anas yasa hannu a aljihu yaji wayam ba komai, cak ya tsaya hakan yasa Shettima tsayawa shima. “Ya maza lafiya?” “Ba lafiya ba, go ahead I'll catch up nayi mantuwa.” cewar Anas. Shettima ya tsaya ya k’are ma d’an uwan nasa kallo sannan yace, “bade blessing d’in ba.”
Anas ya kallesa da gira d’aya d’age sannan yace, “toh meh? Kadega yadda su Kashim suka sani tono maganan chan definately nasan ciwon kai ze kamani and despite that, yadda akayi ruwan saman nan I'm gonna enjoy sleeping.” tare da d’anyin murmushi wanda ya sake bayyano da kyansa tare da lotsar da dimple nasa dake kumatun dama. “Kona yau baraka hak’ura ba?” Shettima yasake tambaya. “Se in na amso karka sha” cewar Anas.
Dariya kad’an Shettima yayi “zan d’an tab’a mana, naji ance da akoi dad’i cikin tea.” Anas ya dafe kafad’arsa “lets go?” Da d’aga kan da Shettima yayi suka juya suka dawo gun Kashim da Baana. Suna iso wurin nasu, Anas yace, “maza bani!” Baana yaci fuska “ban gane baka ba, mezan baka?” “Wai me ka maidani ne? Give me!” Anas ya fad’a a little bit pissed. Dariya Kashim yayi “basa please kaga har yafara losing temper.”
Nan Baana yasa hannu a aljihu yaciro wata leda ya raba into two saidai d’aya yafi d’aya yawa sannan ya mik’a wa Anas kad’an din. “Are you serious? Naga fa wannan abu ni nasaya da kud’ina so kabani me yawan ko in hanaka duka.” Baana yace, “haba! Anas namu na kanmu, kap qauyen nan fa kai kad’aine me blue eyes yi hakuri mana. Aikasan da inada kud’i dana siya nima.” “Toh ni na hanaka yin noma ka samu kud’i? Abeg give me and stop wasting my time.” “Dan Allah fa nace” Baana yafad’a pleadingly. “Okay naji talaka kawai semun had’u a masjid then.”
Daidai sunkai ga shiga corner'n gdansu kenan wata budurwa tafito daga wani gida, sanye take da hijabi iya guiwarta, dududu barata fi shekaru 15-16 ba. Idanunta suna sauk’a kan Anas ta sakar dawata murmushi. Tsuka Anas yaja yasa qaninsa a gaba yana tunkud’esa dan suyi sauri subar gun shiko Shettima daya gano haka tuni ya rage saurin tafiyarsa dukda tunkud’in da Anas kemasa.
Se k’arisowa wajen nasu wannan budurwa ke. “Anas kamar kayi bak’uwa ko? Wannan ba Aisha bace? Ka tsaya kaji me zatace mana.” Cewar Shettima yana murmushi. “Wallahi in bakayi shiru ba zan mareka, kuma barakayi tafiya bane?” Daya wani tunkud’a gaba Shettima besan sanda yasoma matching dasauri sauri suka bar wurin ba.
Isarsu gidah keda wuya suka tarar da Ummee a tsakar gidah tana tsince shinkafa. Da sallama suka shiga ta amsa da fara'arta. ‘yar dattijuwa ce wacce barata fi shekaru 45 a duniya ba, tanada haske sosai amman bara’a kirata da fara ba, ga kyau daidan gwargwado masha Allah!. “Ohhh mazan nawa sun iso ne? Sekuma ruwa ya tareku a hanya ko?” “Eh Ummee” cewar Anas yana k’arisowa wajen da take. “Me kikeyi haka?”
“Tsince nake baba na, tuwon shinkafa Abuu keson ci gashi har ruwan ya tafasa ban gama ba.” “Toh Amal fa mesa bata tayaki ba? Anyways kawo in tayaki Ummee.” “Kai Baba na kaide Allah shi maka albarka” ta d'ago kai tana kallon Shettima dayayi kamar besan ma me suke fad’i ba. “Kai yanzu Shettima koda aiki ze taru ya kasheni ba ruwanka da bari ka tayani ko? Baka ganin wanka ne?”
“Toh Ummee fisbailillahi ina aka san maza da tsintar shinkafa.” Baki wangalau ta bud’e tana kallon Shettima dududu shekarunsa sha shida ne fa da abu aka yake wannan tsiyar bayan ga wansa Anas me shekaru sha takwas bece komi ba. “Ehh hakane, sannu fa” tafad’i cike da gatsine. “Oyoyo Ya Anas” cewar wata kyakkyawar yarinyar da baratafi 8years ba fitowarta daga wata d’aki, ba shakka itace sistersu da suke kira da Amal, kyakkyawace sosai kamar sauran yayun nata bata gama kai Anas fari ba amman tafi Shettima. Su uku kap kamanninsu d’aya.