TANA TARE DA NI
BY
MIEMIEBEEPAGE 10
“Last words da mukayi exchanging da ita are forever stuck up in my head.”
_[“Ummimi dan Allah karki tafi kiyi hak’uri indan plates dana fasa ne I promise baran sake ba. Ummimi I am sorry dan Allah karki tafi. Abuu ka hana Ummimi tafiya dan Allah kace mata I will be a good boy from now on.”]_ “Haka nata had’ata da Allah ko saurarena batayi ba”
_[“Yanzu Aysha bara kiji tausayin yaranki ki hak’ura ki zauna dasu ba? Kalli yadda suke kuka fa?”]_ cewar Abuu
_[“Mstww wannan kuma ku ya shafa nagaji da zama cikin talaucin nan, ace kullum se atashi ba’a san me za’a karya dashi ba gaskia nagaji daman tun farko sanda Abba na yace kar in aureka matsiyaci ne kai amman nak’i sauraronsa. Ga can miji Allah yamin har k’asar waje ze kaini saboda haka ban ga abinda zesa in cigaba da zama a wannan gidan ba.” Jakarta ta ja ta soma tafiya da sauri naje na kama k’afarta ina kuka ina rok’arta. “Ummimi please don’t leave us we love you dan Allah karki tafi, Abuu will find a better job dan Allah karki tafi...” wani wawan ball tayi dani da k’afa nafad’i na ji ciwo a elbow na har d’inki sanda aka min wajen...”]_
“Kun ga ci won?” Ya mik’o hannunsa ya nuna masu Musty. Ciwo ne babba sosai ace yau shekaru kusan goma amman hakan besa ciwon ya rage girma ba. Komawa yayi yasake kishingid’a._[ko waiwayo wa ta dubani batayi ba jakarta taja ta fice, asibiti Abuu yayi rushing d’ina. Tun daga ranan Abuu ya rasa walwala, Abuu da mukasani da fara’a da murmushi ya koma wani abu daban. Kullum cikin tunani, nida Shettima tun tafiyar Ummimi muka rasa gatanmu, kakarmu bata raye bale ace ita zata kula damu, abinci ma waninsa’in mancewa ake damu haka zamu kwana da yunwa Ummie sister’n Abuu ce data dawo daga Maiduguri tayi alk’awarin zama damu. A lokacin ina primary 5 zamuyi common entrance, ikon Allah ne kawai yasa nayi passing exams d’in saboda tafiyan Ummimi yayi affecting d’ina psychologically, mentally and socially.]_
_Tun daga lokacin na canza, na dena dariya, nadena wasa koda da Shettima ne kullum cikin tunani nake har wani psysho psycho na soma zama. Ganin haka Kaka yabawa Baba shawara akaini Maiduguri Boarding school a tunaninsa in ina cikin yara zan sake, unfortunately koda aka kaini can abun nawa be ragu ba sede worse da yayi ma, bana cin abinci bana magana da kowa karatu na kawai nakeyi saboda blue eyes d’ina yasa yara dayawa suna san zama friends dani ace warsu ma ni bature ne sam bana basu chance guda biyu ne sukaci galaba a kaina Baana da Kashim, su biyu kawai suka samu na sake dasu muka zama friends.]_
_[A lokacin da mukayi second term hutu bayan na dawo gida na tarar da Ummie da jaririya kuma a iya sani na Ummie bata da aure. Tambayarta nayi ko ‘yar wace me kama dani haka amsar data bani ne ya mugun sake tada min hankali.]_
_[“k’anwarka ce Anas, uwar ku d’aya uban ku d’aya. Shekranjiya Ummimi tasa wani almajiri ya turo ta cikin wata basket da wasik’a.” Zafaffun hawaye ne suka soma gangarowa kan kumatu na. “Mesa Ummimi zatayi haka Ummie? Mesa barata tausayawa wa baby’n nan ba? Me tamata itakuma da zata rabata da d’umin jikinta? Mesa Ummimi ta tsane mu haka Ummie?”]_[“Anas nima bansani ba hak’uri zakayi, I'm here for you guys, bar kuka Baba na.” “Ina wasik’ar Ummie?”_ Na tambayeta. Acikin wata drawer ta d’auko ta mik’a min na karanta kamar haka...]_
[_ Ibrahim ‘yar da ke cikin wannan basket, ‘yarka ce da cikinta nabar gidanka. Allah ya taimakeni nasamu na haifeta ga abinka nan na kawo maka, banasan abinda ze sake had’ani da kai ko da ‘ya‘yanka..._]
[Hawaye ne suka soma sauk’owa kan kumatu na hannu na mik’a na amshi sister na da ko suna Abuu be sa mata ba dan tashin hankali. Hawayen idanuna na d’iga kan fuakarta ta bud’e idanunta a hankali tana kallo na se kamar Ummimi nake gani, *Amal* na kirata dashi ina hawaye. Daidai lokacin Abuu yashigo. “Amal kasa mata Anas?” Alokacin ban fahimce abinda yake nufi ba sanda na tambayesa yake fad’a mun yak’i sa mata suna ne saboda ni yake jira nayi naming nata tunda nace mata Amal sunan ta Amal kenan. Tun daga ranan na d’au alk’awari zanyi protecting Amal da raina, zan zame mata uwa.]_