TANA TARE DANI

39 3 0
                                    

TANA TARE DA NI
BY
MIEMIEBEE

PAGE 5

  
       “Malam baran iya shiga ganin Fannah ba, if only zan iya bata raina wallahi zanyi.”
           “Addu’a zamu mata Maman Aiman kinsan dole ke zaki kwana da ita.”
     “Yanzu Malam kud’in asibitin fa? Taya zamu biya? Wallahi duk d’an iskan da yama Fannah wannan abu be kyauta ba.” Ta kuma fashewa da kuka hak’uri Baba ke ta bata. “Karki damu da wannan, zan sayar da shanu na in shaa Allah zamu biya bills nata dashi, fatan mu Allah bata lafiya”

               “Shikenan yanzu dama shanun nan kad’ai muka mallaka, Allah ya isa wallahi.” A sanyaye suka mik’e zuwa d’akin Fannah, Baba na bud’e k’ofa suka hango Fannah kwance kan gado ba alaman nishi a tattare da ita.

        Da gudu Mami tayi kanta ta tsuguna tare da rik’o hannunta se kuka take zubawa. “Maman Aiman addu’a zamu mata kuka baida amfani barin koma gida in d’ibo muku abubuwan da zaku buk’ata, kiyi hak’uri” ahaka ya fice isarsa keda wuya ya tarar da Afrah se safa da marwah take a parlour tana ganinsa tayo kansa. “Baba ya kun sami Ya Fannah?” Kallon daya mata yasa jikinta yayi sanyi take idanunta suka cike da hawaye “Baba dan Allah meya sami Ya Fannah?” ta tambaya tana kuka.

           “Afrah da rungumar k’addara aka san musulmi, mun samu Fannah amman yanzu haka tana asibiti.”
          “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un Baba me kake nufi? Meya samu Ya Fannah?”
          “Bata da lafiya Afrah, mun... Mun...” Sekuma yayi shiru hawaye na cika a idanunsa sakamakon hakan ya sake tada ma Afrah hankali. Tana kuka tace, “Baba dan Allah ka fad’a min meya samu Ya Afrah.” Zaunar da ita yayi ya bata labarin komai kuka Afrah keyi sosai kamar zata cire ranta sam tace seta bisa asibitin taga yarta.

        Ba yadda Baba beyi ba dan hanata amman ta dage setaje. Aiman kuwa ta jima da bacci, bayan sun gama had’a abubuwan da zasu buk’ata Baba ya rakata ya tsara mata abin hawa sanda suka b’ace ya dawo ciki. Tafiyar minti 15 ya isar da Afrah asibitin, bayan ta biya sa kud’insa tashigo ciki direct d’akin Fannah ta wuce.

      Tana bud’o k’ofar taga Mami tsugune gefen Fannah se kuka takeyi take itama wani kukan ya faso mata da gudu taje ta rungumi Mamninsu suna kuka sosai. Sunjima suna abu d’aya sannan Mami ta tambayeta “Afrah me kkeyi anan ina Babanku?”
       “Mami yana gida na zo ne in tayaki kwana.”

       “Afrah bekamata kiga yarki a wannan yanayi ba da kin koma gida.”
      “Haba Mami! Ya Fannah fa yayata ce taya zakice haka?” Nan ta jiyo tana kallon Fannah wacce take kamar gawa. Wani sabon kukan tasoma ta rungumeta, tana kuka “Ya Fannah dan Allah karki mutu ki barmu, Allah ze sak’a miki in shaa Allah.” Da kyar Mami ta lalasheta tayi shiru.

       Mami ko kayan tean da Afrah ta had’o musu susha tea ma takasa sha hankalinta duk yabi ya tashi. Afrah bata tab’a ganin Maminsu cikin tashin hankali irin wannan ba.

     Kwana Mami tayi tana nafilfilu tana rok’an Allah haka itama Afrah bawanda yayi bacci cikinsu.

     ****
  
     Washegary da safe misalin k’arfe 8:00AM babban likita daga TH na Maiduguri ya iso. Aikin kusan awa uku akayi kan Fannah sannan likitan yafito. Baba, Mami, Afrah da Aiman dake rik’e a hannun Afrah duk sukayi kansa “likita ya jikin ‘yar tawa?” Cewar Mami jikinta se b’ari yake.

       “Ku kwantar da hankalinku in shaa Allah ‘yarku zata samu sauk’i tana cikin state of coma ne yanzu within 5-7 days in shaa Allah zata farfad’o.”

     “Alhamdulillah!” kukeji a wajen. “Likita amman har kwana biyar? Kana nufin barata san inda take ba har nan da tsawon kwana biyar ko bakwai?”

Tana tare dani by miemie bee Where stories live. Discover now