*BAKI... Shike yanka wuya*
Na
Rahma Kabir mrsMG.
Wattpad @rahmakabirPage 04.
Freebook.Yaya Aisha ta fito tare da Inna Habee suka kama hanya, Zahra kuwa banda kuka babu abinda take yi kafa ba takalmi duk tayi muzu muzu gaba daya kwalliyar ta goge, duk da mutane na kallonsu amma bata damu ba domin kuwa tashin hankalin da take ciki ya wuce abin lissafi, taya ma zata yarda ta zauna da shi bayan duk duniya babu halittar data tsana sama da shi, ga kuma karin yaudara da cin amanarta da yayi akan ya aureta bata sani ba, mugayen kudurori kawai take kissimawa a zuciyarta, dan sai tayi masa abinda zai saketa dan dolensa, ji take yi har barazanar kashe shi zata yi dan ta samu ya saketa, suna isa titi yaya Aisha tace Inna Habee ta koma gida kawai kar su wahalar da ita ga gajiya tunda gidan da nisa, hakan yayi mata matukar dadi dan dama saboda kar tacewa dan uwanta ba zata je bane dan bata so komawa gidan Zahra ba tunda dazu dasu aka je kaita, haka ta juya tace su sauka lafiya ta koma gida, Yaya Aisha ta tare napep suka shiga, sai da suka fara tafiya kafin mai napep ya tambayeta unguwar da zai kaisu dan baya so yayi nisa saboda dare ya fara yi kuma baya aiki in karfe tara tayi, ta sanar da shi sunan unguwarsu saboda ta riga ta yanke shawarar kai Zahra gidanta ta kwana acen kafin zuwa safiya su san abinyi, dan ba zasu yarda su kaida wannan daki ba dole sai sunyi ciku ciku sun samar mata wasu kayan daki kodan su fita kunya, duk da anyi abin kunyar an zubar musu da shi galam galam, zahra da sauri ta waigo ta kalleta kafin tayi magana Aisha ta rigata da cewa.
Nayi magana da mama tace ki kwana gidana da safe sai mu san abin yi. Tunda ba zai yuwu ki kwana gidanki da wannan tsinannun kayan ba.
Hmmm ai ni da kun barni na je masa yau mu yi ta ta kare, ko ni ko shi, wlh banga abinda zaisa na zauna da wannan mummunar ba.
Zahra Hakuri fa za kiyi dan aikin gama ya gama, tunda an riga da an daura auren, Allah ya riga ya bude miki littafin kaddararki dan haka hakurin dai ya zama dole kiyi, ki zauna a dakinki ko dan a bawa makiya kunya.
Hmmm kawai zahra tace mata dan bata jin zata iya yarda da zancenta, har suka isa gidan basu sake yiwa juna magana ba, Aisha ta biya mai mashin suka shiga cikin gidan ta bude dakinta suka shiga, Allah yasa mijinta yayi tafiya dan haka ta ce Zahra ta kwana anan da safe zata dawo ta fada mata yadda suka yi da mama, saboda dole yanzu ta koma gida ta sanar dasu ta kaita sannan ma duk yaranta suna can saboda dama nan zasu kwana har a gama biki, Zahra to kawai tace mata sai ta wuce zuwa gidansu, Zahra ta rufe dakin ta zame net din da aka yi mata dauri dashi ta ajiye a gefe, ta isa uwar dakan Aishan ta dubi kanta a mirro taga duk ta fice hayyacinta, ido yayi kodai kodai kamar tsohon zani, tayi guntun tsaki kana ta koma gefen gadon ta zauna ta rafka tagumi, ta soma tunanin hanyar da zata bi dan kashe wannan auren dan ba zata taba yarda ta zauna da shi ba, inta zauna ma ya riga gama da rayuwarta gaba daya, duk wani burinta ya kashe mata shi, yadda take ganin kanta tafi karfin ta zauna da miji irinsa, a kullun hangenta ita matar manya ce mai kudin da yaci ya bayar, saboda Allah ya zuba mata kyakkyawar halittar da bata ajiye kanta kusa ba sai nesa, wato inda zata ji dadin rayuwa har wani yaci arzikinta, a haka ta cigaba da saka wasikar daji da tuna asalin haduwarta da Basiru.
***
Wata uku daya wuce, Zahra tana hanyar dawowa daga kasuwa mama ta aiketa cefane, Allah Allah take ta isa gida saboda rana dake dukanta ga shi kuma yunwa yana damunta dan lokacin misallin karfe sha biyun rana ne, bata yi aune ba taga ansha gabanta an tsaya, saboda ta kaici ko daga kai ta kasa yi, sai kaucewa tayi amma duk inda tabi shima zai tare ya tsaya, cikin bacin rai ta dago kai tana wurga masa harara, ganin fuskarsa ya kara mata jin wani haushi sai dai ta daure tana kallonsa bata ce masa komai ba, Basiru daya kafeta da ido yana yi mata murmushi ya nisa yace cikin tattausar murya.Ranki ya dade yan mata, kiyi hakuri na tsaidake a cikin ranar nan, kawai dai ba zan iya hakura bane yasa nace bari yau nayi miki magana, dan a bari ya huce shike kawo rabon wani, a gaskiya duk lokacin da zaki je kasuwa ko kika dawo ina yawan ganinki saboda can ne shagona.