*BAKI... Shike yanka wuya*
Na
Rahma Kabir mrsMG.
Wattpad @rahmakabirPage 12.
Freebook.Yaya Aisha ta zauna a kusa da Zahra wacce ta rafka tagumi tana tunanin mafita, dago kai tayi suka hada ido sai ta kauda kai cike da damuwa dan tasan maganar dawowar mijinta zata yi mata.
Zahra hakuri za kiyi da kaddarar da ta sameki, In Sha Allah komai zai yi daidai, yanzu ina ganin me zai hana ki koma gidanki ki cigaba da zaman idda a can tunda musulunci ya yarda da haka, tunda kudin hayar ku bai kare ba kila kafin lokaci sai kiga Allah ya sanyaya zuciyar Basiru ya mai da ki dakinki, ko kuma Baba ya sauko sai ki koma can gidanmu.
Hmmm shikenan sai na koma can din Allah yasa kar Basiru yayi mini wulakanci.
Bazai ma yi ba, watakila ba nan yake kwana ba, ga dubu biyu ki rike a hannunki nima na kudin jallin zobo dana ke saidawa ne na baki, kafin su kare zan zo na kara miki wani abu.
Nagode Yaya Aisha Allah ya saka miki da alkhairi ya kara zumunci.
Amin Zahra, sai dai don girman Allah ki kama kanki ki shiga hankalinki, kinga dai abinda kika jawa kanki wannan ya isheki darasin rayuwa, auren da kike wulakantawa sai gashi yanzu shine rufin asirinki, duk da Basiru ya yaudareki amma kuma ya rike ki amana ke ce dai kika kasa danne zuciyarki, dan haka sai ki kara natsuwa sosai.
Zahra ta gyada kai tare da gasgata maganar yaya Aisha kana ta mike jiki ba kwari ta sanya hijab suka fito, Aisha ta rakata har bakin hanya ta samu abin hawa ta wuce gidanta. Da fargaba ta shiga gidan saboda tunanin irin wulakancin da Basiru zai yi mata in ya dawo ya ganta a gidan, su Maijidda duk suna tsakar gidan, suna ganinta suka mike cike da farin ciki sunaa ga Zahra ga Zahra, da murmushi ta bisu ta isa kofar dakin ta bude da key kana ta juyo tana kallonsu suka gaisa, ganin yadda take ba walwala yasa su shan jinin jikinsu basu tambayeta abinda ya faru da ita ba, dan Basiru ya shaida musu an ganta tana gidansu sai dai bai sanar dasu abinda ya faru ba, ta shiga daki ta cire hijab ta duba taga Basiru ya dauki jakar kayansa, hakan ya tabbatar mata da ba a gidan yake kwana ba, sai ta ji dan natsuwa ta fito tsakar gidan ta tambayesu.
Ummm Basiru baya kwana a nan ne?
Eh tun shekaran jiya ya yiwa baban Salma sallama cewar zai yi tafiya.
Cewar Maijidda, Zahra tace.
Ok sai ta yi yunkurin komawa daki, suka tsareta da tambayar abinda ya sameta, murmushin takaici tayi ta tsaya ta basu labarin abinda ya faru a takaice sai dai bata badu labarin sakin da Basiru yayi mata ba, nan suka jajanta mata da nuna alhininsu, kana maman Imran tace.
Dama Zahra sai da nace karki je amma kika dage, gashi akan dubu goma kin rusa mutuncinki, kuma gaskiya dillaliya bata kyauta ba.
To ya zanyi kaddara ta riga fata, nima wannan ya zame mini izina da darasi, In Sha Allah hakan ba zai sake faruwa ba, na kama kaina.
Kin yiwa kanki farar dabara, Allah ya kyauta na gaba.
Cewar Maijidda, Zahra ta amsa da amin sai ta shiga daki ta soma kokarin daura abincin da zata ci na rana.
Zahra tana ta zuba ido ko Basiru zai zo sai dai har ta kwana biyu a gidan bashi ba dalilinsa, hakan yayi mata dadi, sai dai tayi matukar natsuwa dan ko tsakar gidan bata fita balle suyi hira, hakazasu leko suce lafiya bata fito ba? sai dai tayi murmushi tace kalau, suma da suka ga bata shiga lamarinsu sai suka rabu da ita. A hankali har aka dauki kusan sati biyu, wanda a lokacin mama da Aisha sun zo mata tare da dan cefane suka sake yi mata fada akan ta natsu ta kuma kama mutuncinta, a nan ne take sanar dasu tana so ta fara siyar da awara me miya da yamma dan ta rika samun abinda zai debe mata kewa sannan tana samun kudin kashewa, dan ta rika tallafawa kanta tunda suma ba wadata suke da shi ba, mama taji dadin haka tace hakan zai taimaka mata matuka, da zarar baba ya sauko ya nima Basiru sai ya maida auren, haka suka barta tare da kudi dubu daya da mama ta bata wanda da shine ta siyo kayan hadin awara ta yi kudirin farawa a washe gari, dan haka ta sanar da matan gidansu tasa yaransu suka yi mata talla a makota da samarin waje. Cikin ikon Allah Zahra ta soma sana'ar awara me miya da yamma bayan sallar la'asar, lamarin yayi matukar amsuwa ga mutane wanda ta samu almajiri mai amso kudin samari tana ba shi awara yana kai musu. Mata da yara kuma suna shigowa siya, cikin kankanin lokaci Zahra ta soma samun manyan riba Allah yasa mata albarka sosai, sai ta shiga tara kudin in kuma sun taru ta soma sayan kayan kitchen wanda ba tadasu, ta dauki kudurin sauya kayan katakon da aka yi mata in zata sake wani auren, dan zuwa yanzu ta gama cire rai Basiru zai maida ta, a hankali tayi kumari haskenta ya fito sosai saboda tana cin guminta, sannan ta cire duk wata damuwa ta mai da hankali wajen sana'arta, wanda yanzu ta shafe kusan watanni biyu saura kwanaki ne ta fita iddarta.