*BAKI... Shike yanka wuya*
Na
Rahma Kabir mrsMG.
Wattpad @rahmakabirPage 03.
Freebook.Gadon karfe bono amma ba mai rumfa ba irin na da ɗin nan shi ne Aisha ta yi tozali da shi a ciki, sannan da wani yalolon katifa akai wanda da gani second hand ne, dalilin da ya sanya ta tsorata kenan tana rafka talati, mamaki ya gama cikata, ace taya kayan dakin Zahra zai zama irin haka, bayan Zahra ita tace kar ayi mata kayan daki Basiru yace zai yi mata kayan daki royal bed zai sanya mata a dakunansu, sannan da manyan kujeru na gani na fada, ko kayan kitchen cewa ya yi zai zuba mata su amma Mama tace ko yayane za a yi mata kayan kitchen ta tafi dasu gudun gorin namiji, abin takaici shi ne zasu zo suga gida ba filat ba sannan ma gadon bono wanda ko a dakin tsaffi sai mutanen kauye ake samun irinsa, ace shi ne gadon zahra kyakkyawar budurwa mai cin zamani. A gaskiya ba yaudara kadai Badiru ya yi musu ba hadda wulakanci da cin fuska, Aisha bata dawo daga duniyar da take ciki ba sai taji mutane suna salati, da sauri ta jiyo taga sun tike Zahra da ta suma, tsabar bakin ciki da abinda ta gani a dakin yasa taji numfashinta yana yi mata wuyar shaka, har ta soma ganin duhu duhu ta nima zubewa a kasa mutane suka tarota suna yi mata fiffita, A matukar fusace Aisha ta yi hanya fita daga dakin domin ta ci uban Badiru da yace ba shi ne angon ba, kafin ta fita daga dakin sai tayi kiciɓis da daya daga cikin abokan angon yana leko kai tare da cewa.
Jama'a ku fito, ku fito ku kama gabanku ango zai shigo dakinsa, sannan ma ko wata shegiya ta kama hanyar gidansu babu zancen zuwa wani dinner ehe.
Kutumar kaza kazan ka ne ba mu fito ba, wannan tsinannen gidan da kayan dakin shi ne Zahra zata zauna a ciki, shiyasa kuka ki bari muje muga gida kuka ce an gama shirya koma ba sai mun je ba, ashe ku niyyar tozarta mu ne, to wlh Basiru ya shirya sakin Zahra dan babu abinda zata zauna yi a wannan baƙin gidan dole ya rabu da ita.
Cewar Yaya Aisha cike da bacin rai, abokin ango yace cikin fusata.
Haba malama bani nakar zomon ba rataya akabani, ga angon cen a waje kije ki kare masa tanadi amma bani dan aike ba.
Yana gama fadar haka ya fice, Aisha ta juya cikin dakin tana tambayar Zahra ko ta farfado? suka ce mata eh sai ta isa wajen da take zaune ta dagota ta komota suka fito tana cewa mutane su zo su koma gida dan wlh Zahra ba zata zauna a wannan gidan ba, jama'a kuwa duk suka rufa musu baya suka fito, kawayen Zahra sai kuskus suke yi suna kunshe dariyar mugunta tare da fadin Allah ya kara, fatansu su samu damar ganin Zahra daga su sai ita suyi mata wankin babban bargo dan duk sai sun rama wulakancin data yi musu, musamman ma data fi cin fuskar Ma'u. Suna fita suka samu ango da abokansa tsaitsaye da yake akwai wutar nefa to hasken fitila ya gauraye kofar gidan, haka suka tsaya cirko cirko suna kallon juna, Zahra kuwa kanta a sunkuye jikinta ba karfi gaba daya kunyar kanta ma take ji kafin ta kaiga hada ido da sauran mutane, musamman kawayenta data dinga cika musu baki tana yi musu tijara, tsinuwa da Allah ya isa kawai take zubawa Basiru daga cikin zuciyarta, da ace tana da karfin yin fada da tabbas sai ta zage shi uwata uba tayi masa wankin babban bargo, sannan ba zata matsa a wajen ba har sai ya bata takardan sakinta, dan babu abinda za tayi da auren ya gama cutarta, saboda ba yaudararta kadai yayi ba harda cin amanarta ma yayi, dogon tunanin data shiga kenan wanda maganar yaya Aisha itace ta dawo da ita hayyacinta, taji tanata yi musu wankin babban bargo kamar yadda itama da ta samu dama haka zata yi musu, sai kawai ta tsinkayi wata murya da ba zata taba manta shi ba, azabure ta dago kai dai dai lokacin da shima ita yake kallo yana sakar mata wani shu'umin murmushi yana cewa.
Ku gode Allah a iya haka kawai na tsaya, tunda aurenta nayi bawai lalata mata rayuwa nayi ba, ita ta san karona da ita tun farko akan abinda tayi mini, shiyasa na dauki wannan matakin, kuma wlh tsakanina da Zahra ba saki ko taki ko taso ni mijinta ne ko kun maidata gida zata dawo.