*BAKI... Shike yanka wuya*
Na
Rahma Kabir mrsMG.
Wattpad @rahmakabirPage 02.
Freebook.Zahra gidansu suka wuce domin mutane sun fara haduwa saboda daurin aure. Karfe goma da kwata aka daura auren Zahra da Basiru, mata a cikin gida sai guda suke yi suna yiwa Zarha samnarka, sai dai ita da take a cikin dakin mama tare da kawayenta ta shiga cikin rudani har sai da Ma'u ta taɓa ta tana cewa.
Ya naga bakya yin murna an daura aurenki? ko tun yanzu bakin ki ya fara mutuwa ne.
Uhum taya bakina zai mutu kawai dai wani abu nake tanani.
Da alama jikinki yayi sanyi kalau sai kace an ciroki daga ruwan sanyi, an gaya miki aure wasa ne sai ma anjima kin ganki daga ke sai gardi a lokacin zaki gane shayi ruwa ne.
Cewar Fatsima sai duk suka kwashe da dariya, Zahra dai murmushi tayi zuciyarta tana tunanin lokacin da aka sanar da aurensu, cewar Basiru dan gidan Malam Magaji me faci an bashi auren Zahra ɗan ladi a bisa sadaki dubu hamsin, damuwarta taya Baban Basiru za a kirashi da Magaji mai faci bayan ta san shi dan gidan Alhaji Tasi'u mai goro ne ta aura, ko kila waliyyin sane me suna haka? Tambayar da ta yiwa kanta kenan ba amsa, ganin zata sawa kanta damuwa ya sa ta yi saurin kauda tunanin dan karya ɓata shagalin bikinta, ranar farin cikinta wanda ba zata taba manta shi a tarihinta ba, sai kawai ta mike ta girgiza jikinta tana fari da ido.
Yanzu fa ni amarya ne, na zama matar Basiru ko ba poster, gaskiya ku sakar mini sauti na ɗan taka dan kuwa yau ranar tawa ce.
Nan kawayen suka saki guda suna shewa suka sanya wakar amarya a wayar Hafsa, nan Zahra ta shiga juyawa tana rawa cike da nishadi, su kuma suna yi mata guda da kirari, Zahra ta tsaya da rawarta tana kallon saman rufin dakinsu wanda yake ko silin babu idan ana rana kamar ana dafa mutum a ciki, ga shi gadon bono ne me rumfa daki ciki daya kamar zuciyar talaka, ta yi guɗa iya guɗa ta ce cikin fatin ciki.
Alhamdulillah yau Allah yayi zan bar dakin nan na koma gidana filat mai shegen kyau da bayi da komai, kai Allah ya rabamu da talauci wlh talauci bai yi ba, ko sunansa ma ba dadin fada, dan haka ina sanar daku duk wacce zata zo gidana tofa ta kira ni a waya ta fara sanar dani dan bana son zuwan bazata a rika katse mini jin dadi da mijina.
Iye masu miji, ai wlh nasan nan gaba kadan sai kin ce baki sammu ba. Ni daga yau ma ba zaki kara ganina ba sai kin nime ni dan ba zan dauki wulakancinki ba.
Cewar Ma'u tana mele baki, sai sauran suma suka shiga fadar albarkacin bakinsu, a haka mama ta shigo tana cewa.
Tunda an daura sai ku koma can wajen taronku ku bani waje saboda baki zasu zauna.
Suka mike tare da cewa to sai suka fito, Zahra sai iyayi take zubawa da salo, ana fadin amarya zata juyo tana cewa.
Mrs Bas zaku ce.
A haka suka fita zuwa gidansu Hafsa suka cigaba da shagalinsu. Zahra ganin har yamma ta yi Ango bai kirata ba ya sa ta soma shiga tunanin ya manta da ita, duk da ta san yana tare da mutane amma ta yi zaton har nan zai zo ya sameta ayi hotuna, sai dai shuru kamar dan sanda yaci shirwa, sai ta yanke shawarar kiransa ta dauki wayarta ta kirashi, yana dauka suka gaisa ta soma magana cikin shagoba.
Habeebi ka manta dani gaba daya, ko ɗan kirana kayi ka ce ya taro amma shuru.
Murmushi yayi yana cewa.
Ke ma kin san ina tare da mutane, amma nan da anjima zaki ganni dan tare zamu da yan daukar amarya ana yin sallar magrib, zamu dauke ki zuwa gidanmu daga nan mu wuce dinner.
To sai kun zo habeebi love you.
Sai ya kashe kiran ba tare daya bata amsa ba, ta cire wayar a kunnenta tabi shi da kallo, hakanan take jin wani iri kamar ba Basirunta ba mai rawar jiki akanta, ya kamata tunda yasan an daura aurensu ya nuna farin ciki da rawar jiki akanta amma duk bata ga haka ba, sai wata zuciyar kuma tace mata yana cikin mutane tayi masa uzuri, da wannan tunanin ta kauda komai a ranta ta cigaba da shagalin biki. Yamma tana yi suka dunguma zuwa wajen Makeup din dinner, basu suka dawo ba sai gabda kiran magrib, amarya tasha kyau sosai domin tsadadden leshi ta sanya sai walwal take yi a ciki tana,zuma kamshi, gaba daya kayan data saka Basiru shine ya bata kudi ta siye, ta kuma saka shi karya bari a kawo mata akwati gidansu saboda duk kwashewa yan uwansu zasu yi, ya barsu a gidansu a jera mata su saman waldrop dinta, duk wanda yaje ganin daki yaga kalarsu ba dai yaga kayan ciki ba, akan wannan abin da tayi ba karamin fada mama tayi mata ba amma Zahra tayi kememe tace ba za kawo ba akwashe mata kayan ciki, dan ta san halin yan uwansu kuma ita mama ba hamawa zata yi kar a diba ba tunda haka suke al adarsu, da zarar an kawo akwatin auren yarinya kowa zai zati abinda yake so, gashi musamman yadda Yaya Aisha ta ci burib auren Zahra sai ta kwashi garabasa tunda duk cikinsu itace Allah ya buwacewa auren me kudi, shiyasa ta hana Basiru a kawo akwati shi kuwa hakan yayi bala'in yi masa dadi saboda na shi cikan burin.