*BAKI... Shike yanka wuya*
Na
Rahma Kabir mrsMG.
Wattpad @rahmakabirPage 01.
Freebook._Ki tara a wani waje ko kuma ki yi staring dinsa, dan Allah karku rika cewa na baku daga farko dan ina cikin uzuri. Tafiyar a hankali yake ba zancen sauri, dan ba kullun zan rika posting ba in kuma kun samu kullun to haka nima nake so_
*Gargad'i*
_Ban yarda ayi afmani da wani b'angare na wannan labarin ba ko kuma satar fasaha, ko a daura mini shi a wata kafa ba tare da izini na ba, dan Allah a kiyaye_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM.
Karfe takwas saura kwata na safe Zahra ta fito daga dakinsu tana kallon farfajiyar gidansu wanda ya cika da hayaniyar mutane, daga wani bangare abincin biki ake dafawa a manyan tukwane guda biyu, mata sun gaye wajen ko wanne da aikin da yake yi wasu kuma suna hira, sai bangaren hagu yan layin yin wanka ne a bayi wanda yake hade kashi da fitari zagaye yake da kwanon langa, Zahra ta zo wajen bayin ta tsaya a gefe dan jiran yaya Hansai da take ciki ta fito sai ta shige, duk da masu jiran su shiga suna da yawa. Bayan kamar minti shida Inna Hansai ta fito, da sauri Zahra ta rarumi bokiti zata shiga, sai Larai ta kamo mata hijab ta rike gam tana cewa.
Wallahi baki ssa ba, wato ke shafaffiya da mai zaki shige gamu a tsaye saboda kin raina mana hankali, tum dazu muke tsaye a nan dan mu samu muyi wanka amma ke da kika fito yanzun nan zaki kama ki shige.
Haba Larai dan Allah ku bari nayi mana yanzu zan fito, ko kun manta nice dai Amaryar da ake bikinta yau.
Ko uwarki ce Talatu ba zan bari ta shiga ba balle ke, da kike cewa ke ce Amarya, uban waye ya hana ki fito kiyi wankar da wuri.
Hindu ta kunshe hanci, baki da tafin hannunta saboda warin bakin Larai daya notsi hancinta, da kyar ta iya hadiye miyau ta fizge daga rikon da ta yi mata kana ta ja daga gefe, wata mata ta shige bayin dan ba zata tsaya jiran sai sun gama cacar bakin da suka saba yi ba, Zahra ta sauke numfashi tana cewa.
Baki sai hamami yake yi, kina niman ki kumbura min ciki da sassafen nan, akan wannan shegen bayin da babu dadin shiga kike niman ki tada jijiyoyin wuya, to Alhamdulillah na dai kusa hutawa dan wlh bayin gidana sai mutum ya ci abinci a ciki tsabar kyansa, dan haka ki shiga ki kwana a ciki na fasa wankan, bari na je gidansu Hafsa na yi a can dan yafi nan tsafta.
Tana kaiwa nan ta juya zata wuce, Larai ta damko hijab din Zahra ta wanka mata mari, nan take dambe ya kaure ana kaya kaya da kyar aka rabasu suna kallon juna suna huci.
Yar kutumar... mai shegen fariya ke ba yar kowa ba diyar matsiyata, idan kin so ki je gidanki kiyi wankan a can tun kan a daura auren. Ahayye ai na kosa naga gidan da kike ta surutu a kanshi wanda yafi nan gidan. Kuma kika kara zagina da mai warin baki sai na karyaki, ke har wani tsaftace dake, kiyi kashi a wando ki doɗe fishari ma haka da kin gifta mutum sai yaji hamami da wari, yaushe kika yi kilin, ai da ba'a san asalin angulu bace sai tace daga misra ta fito.
Wooo ance mai warin baki, kuma kowa ya san waye kazama a gidan nan.
Cewar Zahra tana dariyar ƙeta, Larai ta zabura zata tsafkota mutanen dake bayanta suka riketa, da sauri Mama ta shigo gidan tana yaye mayafi tare da rafka salati, tun dazu ta fice taje amso dashinta dan karasa siyan kayan kicin din Zahra, a hanya ake sanar da ita fadan da suke yi, ta karaso wajen tana cewa.
Ai dama na san baya wuce da Larai kike fada, kullun bakwa ragawa juna kamar masu ganin hanjin juna. Wato Zahra yau ma ranar aurenki sai kin raba hali.
Ai kin san Zahra da shegen rashin kunya, gwara ki ja mata kunne in ba haka ba wlh zanyi mata tabon da zata je gidan miji da shi.