*BAKI... Shike yanka wuya*
Na
Rahma Kabir mrsMG.
Wattpad @rahmakabirPage 05.
Freebook.Sanin gidansu Zahra bai bawa su Basiru wuyar ganewa ba, saboda bayan kwana biyu da faruwar abinda Zahra tayi masa sai gata ta zo ta wuce zuwa kasuwa ta gaban shagonsa, haka yasa ido har ta dawo ya sanya daya daga cikin yaran shagon ya bi bayanta har gidansu ba tare da ta sani ba. A washe gari ne Hamza ya dira a kofar gidansu Zahra da wata mota me kyau sannan ya yi shigar kananun kaya ya sha tabarau ya tsatso kyau, sai ya aika yaro ya kira ta, da farko tayi tunanin ba zata fito ba amma data tambayi yaron ko ya san mutumin yace a'a amma da mota ya zo, jin haka yasa tayi saurin mikewa ta cewa yaron yace tana zuwa, haka ta sanya hijab ta fito, tana hangensa ta hadiye miyau saboda da alama ta kusa samun cikar burinta, da addu'a ta karasa wajensa akan Allah yasa da soyayya yazo mata, Hamza bai fito ba sai ya bude kofar motar ya zuro kafarsa wake yana juya key din motar, Zahra ta gaishe shi ya amsa yana sakin wani tattausar murmushi, sai da ya ja fasali kafin ya soma koro mata bayanin kansa.
Ni sunana Basiru dan gidan Alh. Tasi'u, wata guda kenan dana dawo daga US karatu, shekaran jiya na ganki a bakin hanya shi ne na tambayi wasu suka sanar dani in da kike, dan haka ni bada wasa nazo ba dan a yanzu haka burin mahaifina kenan yaga nayi aure kafin ya danka mini ragamar companyn mu, dan haka in ba matsala ki bani dama mu fahimci juna.
Zahra saboda farin ciki har sai da ta ja numfashi ta sauke shi a hankali cikin salo ba tare daya gane murnan da take ciki ba, duk da fuskarta ya bayyana haka, sai tace cikin natsuwa.
To ba damuwa Allah yayi mana jagora, ba kada matsala da ni.
Ok to kafin na cigaba da zuwa ina so ki bani damar niman izini ga mahaifinki domin mu cika sharuddan niman aure, kuma hakan zai sa ki tabbatar bada wasa nake ba.
Wannan karan Zahra sai da tayi murmushin jin dadi, dan haka nan take ta amince tace duk lokacin daya shirya sai yazo yaga mahaifinta ana samunsa da dare bayan sallar isha'i, Hamza ya ce zai so washe gari da dare sai ta sanar da baban, sannan yace ta bashi number dinta zai kirata anjima, nan ta karanto masa yayi saving kana suka yi sallama ya wuce. Kamar yadda ya fada washe gari suka zo wajen baba tare da Basiru suka nima izini, Hamza ya nunawa baba Basiru akan shi ne manemin Zahra, kuma da izininta suka zo, Baba ya yi na'am kana ya tambaye shi mahaifinsa Basiru ya sanar dashi cewar mahaifinsa ya rasu dan haka baba ya yi masa addu'a kana suka yi sallama, har kudi suka dauko suka bawa Baba yaki amsa sai suka wuce ba tare da sunga Zahra ba, Baba yana shiga gida ya sanar da Mama cewar maneman Zahra ne suka nima izini daga haka bai sake wani magana ba, mama tayi addu'ar Allah yasa a kulla alkhairi yasa mijinta ne su samu tayi aure su huta da surutu.
Tun daga wannan lokacin Hamza ya rike wuta kusan kullun sai yazo tadi, da sassafe zai zo ya kawo mata abincin kari wanda yake siya a rastaurant, sai kuma ya bata dubu daya na abincin rana, dare kuma in ya tawo hira zai riko mata kayan kwalam dangin su ice cream, shawarma, yoghurt, cire ko kaza, haka Hamza ya shagwaba Zahra wanda har waya ya sauya mata android mai kyau da tsada, nan da nan ta soma yin Whatsap chart da kawayenta na makaranta, cikin kankanin lokaci Zahra ta goge ta zama classy baby, hatta shigarta sai da ta sauya ta ajiye hijab a gefe sai gyale, yawo kuwa sai inda mai ya kare kuma duk inda zata shike kaita ko ya daukota. Wannan sauyi da Zahra ta samu yasa girman kai da ganin ita wata ce dan haka wulakanta mutane kamar an kara mata bata ganin kowa da gashi, tsoffi kadai take takawa burki suma in basu shiga gonarta ba a wanye lafiya, ta shiga cika baki ga kawayenta raini kala kala babu wanda bata yi musu saboda duk ciki itace mai saurayi me kudi, har ma yake siya mata abubuwan da take tsammusu. A haka rayuwar Zahra ya cigaba da tafiya har suka yi wata biyu da haduwa, wanda Basiru yace sun fahimci juna zai turo da iyayensa a santa biki. Haka aka zo aka yi maganar aurensu aka sanya rana wata guda, Zahra duk bata fahimci auren shiri bane, Dan Basiru kanin mamanshi ya turo dake cikin gari kuma yana da rufin asiri har mota gareshi shine ya zo aka yi maganar aurensu, shi kuma baba bai tsaya wani fayyace zancen da suka yi basu ba balle Zahra ta fahimci ba dan gidan Alh. Tasi'u bane. Sai a ranar aurensu da aka daura take jin sunan babanshi Magaji, har kanta ya daure take tunanin ko waliyyinsa ne da baban ya wakilta.
*****