06

22 4 0
                                    

AL'ADARMU🏇
Page 06

©FADILA IBRAHIM

Kasancewar kowacce majalisar ƴan siyasa basu tashi yin meeting ɗin su sai dare ya ratsa ma'ana dayawa tsakar dare lokacin da kowani bawa yake kwance cikin rumfar ɗakin sa,yana mai da minshari...masu hutawa na hutawa killace a gidajen su....to su fa adaidai wannan lokacin suna cen suna gabatar da meeting ɗin su akan siyasa. wannan ma Al'adar ƴan siyasa ne.

House of assembly
KATSINA STATE
9:30pm

Babban Hall ne wanda ya samu halartar taron mutane ƴan siyasa kama daga kan , senators,reps, state house of assembly, senate president, speekers, honarables, chairmans, minister, excellency deputy gvnor, da Excellency gvnor mai barin kujera....sannan da Govnor mai zaman jiran kujerar gado wato Alhaj.Mustapha Alkasim Daurawa wanda yake neman takarar kujerar govnor na katsina state.

Suna tsaka da meeting aka hau haskawa a babban plasma dake babban hall ɗin wanda tashar BBC ne a kai suna bada bayanai akan manya manyan likitocin da aka kai ma hari a garin abuja, biyu sun rasa ransu while ɗaya kuma an neme shi an rasa.......Jin sunan likitan da aka nema aka rasa shine yafi ɗaga ma kowa hankali sanin cewa Babban ɗa ne ga his excellency mai jiran gado ALHAJI MUSTAPHA A. DAURAWA

Cikin mintuna kalilan hall ɗin ya hargitse da surutun mutane, kowa yana jimamin abin da ya faru, yayin da kowannen su yana tofa albarkacin bakin sa.....Baban Sulaiman ya mike tare da jami'ai masu take masa baya ya nufi wajan motar sa kai tsaye, motoci uku ne zuwa huɗu suka sanya motar tashi a tsakiya suna kula da shi.

Cikin rantsastsiyar motar sa yake waya da Inna mune, hankalinta tashe tana kuka akan abin da ya faru da ɗan nasu, kokarin kwantar mata da hankali yayi yana nanata mata cewa yana hanyar dawowa gida shima yanzun nan, hankalin ta tashe ta ce.."Meya sa ka fito cikin daren nan, kasan bibiyar rayukan mu ake yi tun da siyasar nan ta tashi, muka fara takara sai ya zamana kullin cikin barazanar rayukan mu ake, babu gaira babu dalili an kai ma ɗan mu mafi soyuwa a gare mu hari, wallahi hankali na atashe yake yanzu haka"

Kokarin sa wajen jajircewa yana baiwa matar nasa hakuri, yana kara karfafa mata gwiwar cewa da sannu komai zaiyi sauki...ga shi nan zuwa gida...sannan ya kashe wayar.

Karfe ɗaya saura suka iso Cikin estate ɗin su, basu tsaya ko ina ba sai daidai gate ɗin gidan sa yayin da tuni masu gadi sun hangame gate ɗin.

Hankalin sa tashe ya fita daga mota ya shiga main sashin sa in da ya vi karo da Inna mune da Mummy khausar, da Baban gida da mijin Salima wato Zakariyyah, sai Baba Huraira.....sunyi cirko cirko zaune a falon sa kowannen su fuskar sa babu annuri alamar cewa labari ya iso musu.

Tuni Baban Sulaiman ya kira cibiyar bincike ta ƙasa baki ɗaya, ya bada sanarwar a nemo masa in da ɗan sa yake ko a ina ne a faɗin duniyar nan.

Ranar dai haka su kayi kwanan zaune a falon Baban Sulaiman, sai gabanin asubahi mazan suka tafi masallaci, Da misalin karfe bakwai kuma na safe....duk illahirin zuri'ar Gidan Daura sun hallara jikoki da tattaɓa kunne, da iyaye da kakanni, mata suna cen ciki, while maza suna compound ɗin gidan wanda aka saka rumfa.

Haka suka kwana aka wayi gari babu labarin in da Abhi yake....Tsahon kwana ki uku ana abu ɗaya domin kuwa babu inda ba'a bincika ba a faɗin Nigeria amma ba a samu labarin sa ba.

Sunday Morning
Istanbul International Airport
11:00am

11:00am agogon dake manne jikin kyakkyawan hannun ta ya fitar da sauti mai daɗin sauraro, cikin private jet layi na uku wajan kujera mai kallon wata kujerar, sanye take cikin shiga ta jeans black da babban rigar sanyi wanda yakai mata iya gwiwar ta fara kal mai kwalliyar gashi gashi a wiyar rigar.

AL'ADARMU ✔Where stories live. Discover now