10

15 3 2
                                    

AL'ADARMU🏇
Page 10

©FADILA IBRAHIM

Hakika na jima ina tausasa zuciya ta ina mai bama zuciya ta hakuri na rashin Abhi ɗina, Ga ƴan uwan Abhi da muka jima muna so sun saka mu agaba, babu damar nayi abu sai suce zasu hukun tani, ita kuma Ammi sai tayi ta basu hakuri.....duk abin da ke faruwa babu ruwan Kakana Mustapha da Inna mune, don ko bi takan ƴan  gidan ma basayi.

a duk lokacin dana shiga eatery ɗina Abhi ne first thing that comes to my mind.

Kakana Mustapha ya tako kafa har Restaurants ɗina kuma ya yaba da hakan, sannan ya sanya min Albarka, ya kuma ciro kuɗaɗe masu matukar yawa ya baiwa Ammi yana cewa ta karamin akam jari na siya abubuwan anfani, shi zai tafi Abuja ne.

I was very happy, da Grandpa ɗina ya kasance mutum mai kaunar mu tsakani da Allah....muma kuma akwai respect ɗin da muke bashi.

Da fari na fara buɗe page a Social media, duk dama a lokacin social media bai zama ruwan dare kamar zamanin yanzu ba, sa'annan nayi booklet na items ɗin abincin da muke dasu, na yi employing mutane wanda sai da na musu practical na irin salon girkin Anam, na jima ina koya musu yanda nale sarrafa abinci, na jima kuma ina koya musu yadda nake nawa recipe ɗin akan kowani girki.....Spices ɗina, curry na da garnishing ɗina daban yake da kowani resto, da sauran caterers.

Ban taɓa tunanin restaurants ɗina zai yi suna a garin Daura ba, amma sai gashi da kaɗan da kaɗan ana ta zuwa Eatery ɗina, yes ana kuma zuwa Event kowani irin event tun daga kan KAMU, RECEPTION, DINNER da kuma LUNCHING, BIRTHDAY PARTY, BRIDAL SHOWER, BRIDE EVE, MOTHER'S EVE da sauran su, ana zuwa daga garuruwa daban daban.

I am the CEO of *Anam's Eatery* Ammi kuma tana gida ita ce take aje mana kuɗaɗen mu wanda ta sabon bank ɗin ta wanda ta buɗe nan cikin Daura....anan kuɗin suke shiga.

Bana taɓa mantawa da wannan ranar, ita ce ranar da ya kasance Mafarin labari na.

Friday
11:00am

Muna babban kitchen ɗin mu, ni da ma'aikata suna ta faman shirya  take away, Party jollof rice, da Yellow Fried rice, and Cole slow da shredded meat all in one takeaway anyi rapping da tissue and white rubber spoon da rubber lee......Suna ta sakawa a jakan kwali wanda contract aka bamu ni nakai ma Graphic designer ɗina yamin jakan kwalin da hoton baby boy dama na Naming ceremony ne....kuma yau ne Suna ɗin karfe 4:00pm.

Takeaway na biyu kuma ba'a zuba komai ba,Shi amala ne da miyan ogbono soup wanda yaji ganda zaɓo zaɓo da stew wato jar miya mai soyayyen naman akuya a ciki....sai guest ɗin zunzo sai a musu serving.

Sai wani takeaway ɗin kuma, Dambu ne da alale, abincin gargajiya namu na gida, Dambun shinkafa, yaji zogale da gyaɗa da man kuli wanda kafin na samu ainahin man kulin ma sai da nasha wahala, saboda sunce min wai Dambu ya zama special food na bakin su.

Sai wani leda kuma na takeaway snacks ne a ciki dangin su Dough nut and Cake sai drinks da ruwan faro.

Har mun gama decorating wajan yayi sosai, daidai yadda suka kayyaɗe nayi musu, nayi excusing employees ɗina na ko ma gida don nayi wanka na shirya don MC ɗin da zai yi magana baya da lafiya, sai nace kawai tun da Baby ceremony ne zan zo kawai nayi.

Sea green abaya na sanya, nayi rolling da black veil na sanya flat cover na rataye jakana ta goyo mai gashi gashi, mai kirar mikey mouse.....fuskata ko kwalliya babu, don ko kwalli ma ni ban saka ba, na ɗai ɗaura agogo yayin da na fito ainahin musulma tamkar bakaken larabawan nan.

Kasancewar Restaurants ɗinmu yana kan Titin Buhari road, tudun wada Daura katsina state, mun tsaya ana bada hannu, sai naga wata zugar mabarata maza da mata suna bara, sai naji ina son na taimaka muku.....sai na fito daga motar da Ammi ta siya mana karamar 306 na nufi wajan na raba muku kuɗi ɗari biyar biyar suna ta godiya to garin in juyo ne sai wani mai mashin a rashin sani ya kusa banke nina ɗan duka kamar mai sujjada, mutanen wajan suna ta min sannu na tashi na nufi mota ta.

AL'ADARMU ✔Where stories live. Discover now