17

18 2 0
                                    

AL'ADARMU🏇
Page 17

©Fadila Ibrahim

*Nace ba, kuna ta jiran ganin soyayyar AIMAN DA ANAM, to gashi munzo gaɓar soyayyar, sai a baje da kyau a sha karatu*

_________Deen ya ce,"Why!!!!! What's your problem with me nothing can stop me from coming?

Aiman ya ce,"Ka dawo kazo kaga abin da zan maka,"

Deen na fita, gida ya nufa cikin bacin rai da tunani barkate kunshe cikin zuciyar shi.

Kiran waya yake hannun sa kakkarwa yake tsabar ɓacin rai....a ɗayan ɓangaren aka ɗaga wayar anan amsawa muryar dashasshiya mai kama dana ƴan daba masu shan barasa.

"Oga Deen how far???

"Guy i need you urgently, if possible you guys should come today" Deen ya faɗa a tsanake

Daga cikin wayar aka ce,"But, you know what i need first"

"Guy check your account nnnnn I've sent half of it before calling you".....Deen ya bada amsa yana mai da ajiyar zuciya don ranshi ya riga da ya ɓaci makura.....ya sauke wayar a daidai lokacin da Momma take karasowa in da yake, ta jima a tsaye tana karantar ɗan nata da alama an masa wani abin ɓacin rai ne.....Ta na ganin yadda ya aje wayar ya nufi cabinet ɗin da suke ajiye kwalaben Barasar su, ya ɗauki babbar mai tsadar ba tareda ɓata lokaci ba ya hau korawa, sa'i guda giyar ta sanya shi manta duk wani karatun alkur'anin da Anam take koya masa, shaukin giyar ta mantar da shi rayuwar da suka fara da Anam da kyawawan halayen data nuna mata, tsananin tsanar Aiman ya shafe ta wanda tsanar ya manne da soyayyar da yake mata...........Idan ya tuna kallon idanuwan Aiman da yayi babu wani abu a cikin idanun sai rashin tsoro na jajirtaccen Namiji mai jini a jika, abin da yafi sha mai kai shine SOYAYYAR Aiman daya hango a idanuwan Anam.....ya buga wani teburi dake gaban sa da kwalbar giyar tuni teburin ya tarwatse yana yarfe hannu.

Momma na tsaye tana kare masa kallo, ta sani ko ta tunkare shi yanzu ba maganar ta zai ji ba, sai ya aikata duk abin da yayi niya tsabar taurin kai irin na Deen ɗin ta....ta haye sama kawai ta barshi yana ta hauka.

•••••••••••••

Na jima muna kallon kallo tsakani na da Aiman bayan Deen ya fita, ƙunar da zuciya ta take mun ya sa na kasa furta masa ko da kalma ɗaya, na ɓacin rai da Deen ya sani....Ɗaukar jaka ta nayi na fita ganin client, da employees ɗina suna ta kallo na nida Aiman.

Bi na yayi, da sauri na shiga mota, sanin cewa zan iya aikata koɓa mene ne shiyasa ya shima ya shiga motar , ko gezau balle ma nasan ya shigo, na kunna mota nayi reverse na arce da gudun tsiya......Sanin cewa am not my self sai naji ya ɗaura min hannayen sa saman hannun dama na, ya kalle ni ya lumshe idanuwa alamar na sassauta gudun, ban sassauta ba sai da nashiga layin dana san babu mutane sosai kafin na parker.

Fita nayi da sauri na tsaya rai na a ɓace yake, zuciya ta tana min tunanin wata kila Deen zai aikata wani abu babba, don bazai kyale Unknown ba.

Fitowa yayi cikin natsuwa yazo ya tsaya gefen inda nake, hankalin shi kwance ya ce,"Da gaske kike Anam, are you willing to spend the rest of your life with me????

Kwantar da muryar tasa, tasanya min shauki cikin zuciya tuni na manta da tashin hankalin da zai iya risken mu, amma don tsokana sai nace, Aa kawai na faɗa ne don ranshi ya bace,Unknown baka san an kusa ɗaura min aure da shi ba"

"Cikin natsuwa ya juyo ya ce,"Mace tamkar allura ce a cikin teku/ruwa, kuma bana da tantama nine zan nemo ki"

"Murmushi nayi mai sanyaya zuciyar mai kallo na da sauraro na, Idanuwan mu sun sarƙe da kallon juna, yayin da zuciyoyin mu suke bugu lokaci ɗaya muna murmushi....zallar soyayya ce take wanzuwa a sassan jiki da kuma ruhi wanda ban san ta yaya hakan ya faru ba......Na ce,"Ni zan tafi gida, ya kamata ka bar garin nan"

AL'ADARMU ✔Where stories live. Discover now