AL'ADARMU🏇
Page 08©FADILA IBRAHIM
Ammi ta ce,"Mun amince zamuyi rayuwa daku akan yadda kuka ɗaura mu, mun amince zamu biku yadda kuke so, kuma In Sha Allah zaku same mu masu biyayyah ga duk abin da kuka sanya mu"
Wani abu naji ya tokare min kirji, wanda ban san lokacin dana ce,"Ammi idan kuwa muka amince da bukatar su, To su sani yin biyayyah dasu hakan ba shi zai sa ayimin aure da wanda bana so ba....ina da damar da zan zaɓi mijin da nake so, infact ba zan yi aure a dangi ba* ina kaiwa nan na tashi na bar musu falon, kai tsaye fita nayi daga gidan na mike hanya zuwa gidan su Abhi na....Khausar ce ta biyo ni har da ɗan saurin ta tana haki tana cewa,"Anam wait for your sister we need to talk"
Na tsaya ina hararar ta ina cewa,"Hurry up please as am feeling upset" Ta isko ni in da na tsaya, ta na cewa," I think what you did in front of our elders was unfair Anam"
Muna tafiya muna magana na ce mata,
"Khausar, What i did was an act of personal freedom, and am fed up with life in Daura and Nigeria"
Khausar ta kalle ni tana zare idanu tace,"Are you serious Anam?
"Yeah very sure, I wish i could return back to Turkey, where i feel more at home" Nace mata a dai dai lokacin da muke shiga gate ɗin gida, kai tsaye nayi hanyar sashin mu, Khausar ta biyo ni ta rike min hannaye na ta ce,"I promise to take you out tomorrow, and am very sure you will enjoy it"
Nayi murmushi ina cewa,"Alright then, it's important to be clear in our promises, so we don't accidentally cause misunderstanding or disappointment ok" ina kai nan na tura karamar kofar shiga BQ ɗin mu ina shiga bada jimawa ba, Ammi ta shigo.
Shirun ta yayi yawa, ta wuce ɗaki kai tsaye sai da ta sha paracetamol sannan ta samu waje ta zauna ta lumshe idanuwan ta tana nazari....a hankali na zo ina matsa mata hannayen ta, na kwanta saman kafaɗar ta nayi shiru.
*Anam*
Ta kirawo sunana, na amsa a hankali ta ce,"Bana son kiga kaman ina tauye miki hakkin ki, Anam na amince da bukatar su ne saboda ina so mu zauna cikin ƴan uwan Abhi ɗinki, Kinfi kowa sanin cewa na jima ina so muzo Nigeria, sai gashi a cikin kankanin lokaci munzo kuma bamu isa muce zuwan namu ba alkhairi bane Anam, tun da yanzu muka fara zaman"
Ta tsagaita ta sha ruwa, kafin ta cigaba da cewa, "Na sani idan muka koma Turkiyyah hankalin mu zai kwanta saboda babu hayaniya amma bamu san wani hali Abhi yake ciki ba, kar mu guji zuri'ar sa don baya nan, gwara mu so su tun bamu san ko yana raye ko baya raye ba, Anam zama da su shine zai sa mu koyi juriya da jajircewa akan rayuwa, ba komai bane kake so Allah yake baka, muna da kuɗi muna da power ba shi zai sa mu tafi mu bar su ba, Anam muna da ilimi mun san abin da muke yi, tsangwama ba shi zai sa mu koma turkey ba.......... ina so muyi hakuri mu zauna da su daɗi ko wuya Allah na tare damu kinji Anam ɗina"
Na gyaɗa kai sannan nace,"Amma ba shi zai sa suce zasu aura min wanda bana so ba Ammi"....."Shishhhhhhhh"Ammi ta toshe min baki tana cewa ,"Bana son na kara jin wani magana kuma Anam, wai ma yaushe kika girma ne har kikasan wanda zaki aura"
Na zumɓure baki ina buga kafafu, na ce,"Ammi ni babu wanda nake so, kawai ni wannan Al'adar tasu tana bani haushi, wallahi na tsani Al'adar tun da sanadin da ya sanaya Abhi har yayi aure babu wani nashi da yasan da zaman mu sai yanzu.....Ammi ni gwara fa mu koma Turkey saboda muyi rayuwar mu babu takura balle tsangwama.
Ammi ta girgiza kai tana cewa,"Mu zauna for a main time Anam saboda ko zamu ji wani news akan Abhi kinji"
Tashi nayi na koma saman gado ina cewa,"Shikenan sai musa kan mu acikin damuwa da wahalar rayuwa bayan muna da yanda zamuyi maganin abin, zaman mu dasu yana nuna cewa mun amince da duk wata bukata tasu"
YOU ARE READING
AL'ADARMU ✔
General FictionAL'ADARMU No description, Just get your self ready, seat properly and enjoy reading this amazing heart touching story AL'ADARMU