AL'ADARMU🏇
Page 14©Fadila Ibrahim
Rashin lafiyar Grandpa tayi tsanani wanda aka ɗauke shi daga General hospital Katsina aka kai shi babban asibitin dake garin Abuja.
A bangaren Aiman, ya gama duk wani abin da Abhi ya sanya sa yayi, a kallah dai tsahon sati guda ya ɗauka yana bawa Anam sakon Abhi tare da sakon zuciyar sa sai dai yaga alamar Anam bata taɓa karanta sako ko ɗaya ba, jin silent ɗin ta yayi matukar yawa, sai ya fara shirye shiryen komawa Abuja saboda akwai case ɗin da ake ta kiran sa a kai, bugu da kari ga kuma case ɗin Likitoci da suke kai.....Ya shirya tsab ya koma Abuja ranar asabar.
A satin da aka kai Grandpa hospital, a satin muma muka je,Inna Mune, Mummy khausar, Ammi, Ni da Khausar da sauran yaran Mummy Khausar a babban jeep ɗin gidan gaba ɗaya....na samu damar ganawa da sauran ƴan uwa na, munyi wasa da su tamkar ciki ɗaya muka fito, a hanyar mu ta zuwa Abuja.
Mun isa ba da jimawa ba, muka sauka a wani matsakaicin gidan Grandpa wanda ya kasance gidan hutun sa idan yazo siyasa a garin Abuja.....Bayan duk mun huta muna ɗaki ni da su Khausar...Khausar ta ce,"Anam zan so muyi yawo a garin Abuja kafin mu koma jibi"
Nayi murmushi nace,"A bincikena na gano Abuja ita ce City a cikin jahohin dake Nigeria, kuma Nigeria tana matukar ji da ita sosai haka zalika ita ce gari wanda babu hayaniya, masu kuɗin Nigeria ba kowa ba, suna zuwa domin shakatawa da hutawa.....a karamin bayanina na karashe maganar ina kallon Khausar
Khausar tace,"Yes bakiyi karya ba, amma akwai garuruwa da dama da suka tara manya manyan masu kuɗi ba Abuja kaɗai bace, Abuja tayi suna ne kawai saboda ita ce FCT, a cewar Khausar.
Na gyaɗa kai, a dai dai lokacin Inna mune ta leko tana cewa "Maza ku fito zamu tafi asibitin"
Dama mun gama shiri, sai duk muka fita kai tsaye kowa ya zaɓa wajan zaman sa a cikin motar da muka zo
na zaɓa kusa da window ina kare ma garin kallo a wannan lokacin ne na hango wani tsararran park wanda yayi min kyau saboda wajan wasan yara ne dama manya.....hakan ya sa na kudiri aniyar zuwa park ɗin don nishaɗi ina son tuna Abhi na, da old memories ɗin mu.Washe gari da yamma misalin karfe huɗu da ƴan mintuna, na shirya tsab cikin shiga ta riga da wando shigar ƙasar Turkey, rigar silk material ce ya wuce gwiwa mai botura tun daga sama har kasa, long sleeve wato dogon hannu, sai bakin wando shi ba palazo ba kuma shi ba pencil ba, dai dai ankle ɗina wato idon sawu, sai white canvas da kuma black veil....Khausar na gani na sai da ta ɗauke ni hoto wai nayi kyau, ni kai na dana kalli mirrow sai naga ainahin kama ta sak ƴan ƴasar turkiyyah saboda kamannin Ammi kaɗan da yau suka bayyana a fuskata da sura ta.
City Park Abuja
Abuja City Park wanda yake kan titin Ahmadu bello way wuse, ni da Khausar ne wanda ita tayi shigan doguwar rigar abaya...Kai tsaye filin kwallon su na nufa, in kallon yadda suke buga wasan kwallon kafa wanda yana ɗaya daga cikin favorites ɗina da ina school.
******
Cikin motar taxi kampanin peugeot, kujerar mai zaman banza, sanye yake da kayan lauyoyi bakin wando, farar riga ƴar ciki da neck tie, sai bakar rigar da ake ratayawa ta lauyoyi, sannan ya rike ta a hannu , da akwai wrist watch a hannun sa na dama, sai ya kara kyau kamar dai ba Aiman ba.
Ko dayake ma wannan ɗin is not your regular Aiman wannan ɗin *Barr. Sulaiman Yusuf Zaria* kenan. matashin saurayi mai cikar kamala, A hankali cikin natsuwa ya sake leken driver wanda yake ta faman kunce tayar motar yana kokarin ɗaura wata, daga bisani ya fita daga cikin motar yana tambayar, direba
"Wai har yanzu baka gama ba?
"Kayi hakuri yallaɓai, motar dole kuma sai mai gyara yazo ya duba min saboda na kunna ta taki tashi"
YOU ARE READING
AL'ADARMU ✔
General FictionAL'ADARMU No description, Just get your self ready, seat properly and enjoy reading this amazing heart touching story AL'ADARMU