AL'ADARMU
Page 38
Mallakin DielaMALI/MELI
ƙasar Mali,(Meli) ƙasa ce dake yammacin afrika, Mali tana ɗaya daga cikin manyan ƙasashen afrika na 8 takwas, ƙasa ce wacce masana ilimin kimiya da masana hasashe suka ce girman ta da tsarin ta kamar girman ƙasar texas, wasu kuma suka ce ƙasar california, waɗannan ƙasashen Amurka ne.
ZANTIGUILA
Zantiguila kan hanyar birnin Segou mai nisan kilomita 70 saba'in, daga babban birnin ƙasar Bamako.Babban birnin tarayyar ƙasar meli.
Kai tsaye jiragen mu suka soma sauka ɗaya bayan ɗaya muna afkawa cikin kauyen.
Kewaye garin mu kayi kafin wasu daga cikin mu suka shiga masarautar kauyen muka samu damar shiga fadar, wanda gini ne na asalin gine ginen ƙasar mali ginin laka wanda ake cuccura shi da da itace anyi shi mai tsayi kamar bukka.
Da ni da commander muna fadar sarki muka kuma sanar da abin da ya kawo mu.
Yayin da idanuwana suka sauka akan wata mace banda matar da take gefen mai martaba, Da alama ita ce gimbiyar da take zaune gefen hannun damar mai martaba sarkin nasu, Jin dalilin zuwan namu ya sanya idanuwan ta suka kaɗa sun canja launi, jin dalilin zuwan mu, mun zo tafiya da ɗan ƙasar mu ne, kuma babu ruwan mu da cewa sun ƴan tashi, abin da muka sani shine shiɗin dai ba bawa bane don haka dole su bamu Ayman.
Ran gimbiya ya yi dubu ya ɓaci, ina kallon yadda ta mike buguzun buguzun ta wuce fuuuuuu gasu irin matan nan da Allah ya basu murjajjan jiki, ga kiba ga koshi ga tsayi.
Awan mu ɗaya muna zaune a ɗan tsukukun fadan nasu, Commander ya ce, "Idan fa ba'a bamu ɗan ƙasar mu ba to zamu ɗauki gimbiya da sarkin garin su tafi da su..Duk suka yi banza damu, ta shi nayi na shiga ciki , sai wasu dakaru suka nuna min wuka, banyi wata wata ba na harbe su da bindiga, karar bindigar ta sanya wasu sojojin suka biyo ni ciki, daga nan muka fara neman in da suke, ido rufe, dakaru na ta zuwa muna harbe su, har wani ya yanki hannu na da wuka, sosai jini yake zufa na samu kyalle na ɗaure wajan na miki nayi wata hanya cike da kwarin gwiwar zan samu Ayman saboda zuciya ta na bani ta wajan yake.
Na hango ana ta kokarin fito da mutane maza da kuma mata suna yin wata hanya da ta bi jeji, waya ta na sojoji na ciro nayi magana da commanda na faɗa musu in da nake.
Sai dai kafin su karaso an min tarko aka jefa ni cikin wani babban keji wanda suka ɗaura shi saman wata babban mota hanya ce mikakkiya bamu kaɗai bane a wajan, har da mata da maza da aka kama.
Cikin wannan yanayi na ɗaura idanuwa na a kan masoyi na, ya rike min hannun da aka yanka, idanuwan sa suka kalli idanuwa na, sai naji wani farin ciki da nayi tozali da Ayman ɗina.
Ya ilahi!!!!
Ya salam!!!!!!!"Inna lillahi wa'inna illaihi raji'un" wallahi ba dan ni da na riga na san Yaya Ayman ba, da babu wanda zai iya gane shi, da wallahi cewa za'ayi ba shi bane, yayi baki, ya rame kamar mai cuta Allah ka raba mu da ita......yana tangal tangal....ya kusa faɗi na taro shi da hannu na biyu, hawaye na suka sauka saman fuskar sa yayin da ya ɗaga dara daran idanuwan sa ya kalle ni da kyau, sai ya saki murmushi mai kayatarwa, ya sanya siraran hannayen sa ya share min hawayen dake fuska ta, ya ce,"Anan me yasa kika ɗau tsayin lokaci baki zo ba?....Kullin da ke nake kwana nake tashi a rai, a ko da yaushe zuciya ta na bani kwarin gwiwar zuwan ki, Bana bacci sai dare ya raba, ako wani sa'i guda ina ambaton sunan Allah da ya kawo mun Anam ɗina na sani you are the one, Anam ke kaɗai ce zaki cece ni daga hannun azzaluman mutanen nan.
Na ɗaga idanuwa na ina kallon Gimbiyan data fito tana harara ta,ta umarci da a raba mu, garin buɗewa ne za a fito dani, sai ga commander da sauran sojojin suka fara bada wuta suna harbi, nan da nan suka harbe duka direbobin motaoci ukun, kuma aka sake mutanen da ke ciki, bayan ni kuma na sauko na kama gimbiya, dukan ta na fara yi sai da hancin ta ya soma jini.
YOU ARE READING
AL'ADARMU ✔
Ficción GeneralAL'ADARMU No description, Just get your self ready, seat properly and enjoy reading this amazing heart touching story AL'ADARMU