AL'ADARMU🏇
Page 35
©FADILA IBRAHIMAbhi ya ce,"Yes na jima ai, shekaru uku da suka wuce,.....ya faɗa yana kokarin fitowa daga cikin mota ya kulle kofar yana cewa,"Fito mana Anam.
Babban sashin da aka tsara shi a harabar parker motoci, ba shi muka nufa ba, sai naga mun billa ta wani gate cen da nisa, muka shiga wannan kam babban sashi ne mai fili haɗe da kewaye ga flawoyi, da karamin round about ginin gidan sama ne, ya tsaru iya kar tsaruwa, yafi na farkon girma da tsari.
Wani kyakkyawan yaro ne ya fito a kalla ba zai wuce shekara huɗu ba, yana kama dani sai dai kammanin Abhi sun fi bayyana a fuskar yaron ya nufo ni da gudu yana cewa, *Aunt Anam*
Da mamaki na chaɓe yaron, sama ina chilla shi duk da ban san ko ɗan waye ba, na kalli Abhi ɓangare guda shima yana kallo na chike da murmushi a fuskar sa.
ABHI Ya ce,"It's a surprise Anam, lets go inside"
Na gyaɗa kai ina karasa shiga cikin babban corridor da zai kai ni main parlorn gidan....Ya ilahi,"Gida kamar aljannan duniya wani gini ne kaman palace, dogayen labulaye dark blue na cikin kuma white, gidan nan ya tsaru makurar tsaruwa ga wasu cushion ko a ƙasar waje albarka, kafafuwa na suka luntsuma saman lallausan rug mai tsada kamar na gidan sarauta.
Muryar Umma ce ta fito sanye cikin lifaya mai tsada da kyau, jikin ta sai tashin kamshin turare ya keyi, kamar kuma ba Umma mai ɗan wake ba, hasken ta na zabiya yana nan amma ta kara glowing, tayi kyau hutu ya nuna a cikin ta, daga bisani kuma Ammi ta fito tana cewa, Anam kice gwara da Allah yasa na zo Nigeria da yanzu ina turkey da anyi lovely moment bana nan"
Da mamaki na ke kallon fuskar kowannen su, Shin me ake kokarin sanar dani ne all this while ban sani ba?....Na kara kallon yaron dake hannu na, sai na ga kammanin Umma kuma a fuskar shi....na ce,"Abhi shin hasashen da zuciya ta take min gaskiya ne kuwa?
"Me zuciyar taki take hasasho maki Anam? Ya bukaci tambaya
"Shin ka auri Umma ne bayan tafiya ta? Na tambaya ina kara kallon Umma da Ammi suna ta kashe ni da murmushi....naji Abhi yana cewa,"Well!! well!!! at long last yau zakiji komai, zauna ANAM, Na samu waje na zauna na kagu da naji koma miye.
Abhi ya ce,Zan baki labari right from faɗuwar ki lokacin da kika suma a gidan su Umma...gidan Baba huraira you get that right"
Na gyaɗa kai ina cewa ai Abhi daga wannan faɗuwar buɗe idanuwana nayi na ganni a ƙasar Turkiyyah ko ba haka bane? na tambaya
"Yes haka ne, shiyasa nake so na dawo miki da tunanin ki baya.************
*Wallahi na dai ga tafiyar su, amma daga nan ban sake sanin in da kai na yake ba*"Kin suma a wajan baki san in da Hankalin ki yake ba, Ayman da Khausar ba tafiya suka yi ba, sun sha kwana ne kawai, sai suka yi reverse suka dawo suka ɗauke ki"
Na gyaɗa kai ina jin wani sabon labaru kuma.
Anam, Duk da cewa ni na san komai, amma Tun daga kan Baban gida, Grandpa, da sauran zuri'ar gidan daura kowa abin ya ɗaure masa kai jin sabon labarin da Ayman ya zo da shi.
Ranar da Ayman ya sanar ma kowa cewa kuna soyayyah, Feedback ɗin ko ince reaction ɗinki shi ya tabbatar mana da cewa yes kuna tsananin son junan ku, mu ba yara bane, a cewar Grandpa ɗinki bayan ke da Ayman kun bar filin meeting ɗin kun tafi gida.....Grandpa ya kirawo Khausar ya zaunar da ita ya kuma sheda mata yadda Anam take ta kokarin ɓoye mata soyayyar da suke yi da Ayman, don saboda kada alaqar dake tsakanin ku ta yanke.
Khausar was so heartbroken, da ta gane ashe son maso wani takeyi, and she cannot become so heartless ta auri masoyin ta daga baya kuma ta rasa friendship ɗin ta da ƴar uwar ta.....So is either ta hakura ke ki aure shi, ko ya aure ku duka biyu.
YOU ARE READING
AL'ADARMU ✔
General FictionAL'ADARMU No description, Just get your self ready, seat properly and enjoy reading this amazing heart touching story AL'ADARMU