Kashi na Ɗaya
Duk da duhun da ke cikin ɗakin bai hana ta ganin hawa da saukar numfashinsa ba, ta yi masa ƙuri kamar mai shirin hango mafitar minsharin da ke sauka a kunnuwanta kamar wani kukan rago da ke jiran avyi layya da shi.
Mtsw! Ta ja wani dogon tsaki tana mai juya baya, ƙarin takaicinta shi da ya sanya ta a halin da take ciki bai ma san tana yi ba. Miƙa hannu ta yi bayan ta juyo gare shi a karo na biyu tana mai shirin taɓo shi, amma sanin da ta yi ɓata mata rai kawai zai yi ya sa ta juya cikin wani tuƙuƙin baƙin ciki, hasken da wayarta ta yi ne ya sa ta ga carbinta a gefe yashe, ta kai hannu ta ɗauka ta shiga ambaton Allah, ba ta ce kai tsaye ga irin zikirin da take ba, komai ya zo harshenta kawai shi take ambato, a haka har bacci ya yi awon gaba da ita.
Kamar kullum, alfijir na ketowa ta tashi cikin aminta da Allah a matsayin Ubangiji, bayan ta gabatar da sunnoni da farillai ne kuma ta fara kiciniyar shirya musu abin kari kafin ya dawo daga masallaci. Hakan ne sunnar gidan, abincin kari ba ya wuce musu ƙarfe bakwai na safe, idan kuma kwanakin aiki ne su fita bakwai da rabi, idsn kuma ƙarshen mako ne su koma bacci.
Yau ma kamar koyaushe kicin ɗin ta shiga, ba tare da sanin me za ta girka ba. Hakan ɗabi'arta ce, ba dai ta tsara abu kafin ta yi ba, abu ɗaya ne da ta taɓa tsarawa kuma ya zo mata da tangarɗa.
Ganin biredi a sama ya sanya ta gasa biredi sannan ta cika shi da sandwich. Kafin ta kammala 'yan aikace-aikacen ya dawo, ya leƙo inda ta ke suka gaisa kafin ya juya zuwa ɗakinsu.
Yana ba da baya ta ji wani tuƙuƙi ya tokare mata a ƙirji, in da son samu ne ta ji shi gam a jikinta, ba wai kawai ya bar ta da rahaman jin saukar numfashinsa a kan fatarta ba. Tunawa da ta yi so ba samu ba ne ya sanya ta mai da hankali a girkinta, tana kammalawa ta shirya a tire ta kai musu ɗaki. Haka ɗabi'arsa take, da yawan lokuta ba zai fito falo su ci abinci ba, ya fi son cin abinci a ƙuryar ɗaki . Tun da ta ga bai fito ba ta san yau irin ranekun ne, dan haka ba ta yi ko tunani na biyu ba. "Abinci a ƙuryar ɗaka," ta faɗa a ranta cikin takaici, "in har a ce wani abun kirki ke gudana."
Ko da ta isa ɗakin yana kashingiɗe yana sauraren radiyo, hankalinsa kacokan na ga abin da yake ji amma kuma hakan bai hana masa amsa sallamarta ba. Ya yunƙura ya tashi daga kwanciyar da yake zuwa ga zaune yana mai jingina da allon gadon kwanciyarsu cikin gyarawa yanda za ta sanya farantin abincin da kyau.
Kallon sa ta yi bayan ta ajiye tiren, inda aka yi dace shi ma ita ɗin yake kallo, hakan ya sanya idanunsu sarƙewa cikin juna tana mai ƙoƙarin aika masa da saƙon da duk wani sassa na jikinta ke ƙoƙarin aika masa. Gaba ɗaya jikinta macewa ya yi da ta rasa ko fahimta ce bai yi ba ko kuma kawai ganin dama ce ya sanya shi mai da hankali a damtsen hannuta tare da faɗin, "Esha, ƙiba kawai kike mulkawa fa abinki." A muryarshi akwai alamun dariya da nishaɗi.
Yaƙe ta yi cikin ƙarfin hali ta ce da shi, “Alhamdulilla! Ai da yake kana ciyar da ni da kyau ne Sabbeni."
Ya ɗan ƙyalƙyale da dariya ba tare da gane saƙon da ke cikin amsar da ta ba shi ba mai gugar zana, sannan ya fara mai da hankalinsa kan abincin da ke gabansu, takaici ya ƙara ƙume ta.
Ita ta taso a gidan da tsarinsu ba a magana yayin cin abinci, tsarin da ta ɗakko zuwa gidan aurenta, amma cikin shekaru takwas ba ta iya tabbatar da shi na wata biyu ba, gaba ɗaya lokacin da Faruƙu mijinta ke da shi wajen faɗa mata duk wani abu to lokacin da ya ke cin girkinta ne. Esha kaza, Esha kaza! Haka yake kiran sunanta, Esha. A da can idan yana kiran ta da hakan ba ta sanin lokacin da take darawa, ita kaɗai ma sai kawai ta ji tana murmusawa, giyar so da ƙauna na ɗawainiya da ƙwaƙwalwarta. Amma a yanzu duk ta daina jin zaƙin hakan, lami, salam!
Yau ma kamar kullum, ya fara daga labarin sabon shugaban ma'aikatansu da aka kawo ya dire da labarin tubashiyarsa mai taya shi zaɓen macen ƙara aure. “Esha an ce za mu iya haihuwa, lokaci ne kawai be yi ba, amma kuma duk an bi an dame ni da ƙara aure!" Ya ce cike da takaici. Ba ta yi mamaki ba, dan har gaban idonta an sha goranta mata haihuwa, danginsa, musamman ƙannensa mata da tun farko ba ita ce zaɓin aurensu ba gare shi.