CCB

80 18 13
                                    

KASHI NA ASHIRIN DA ƊAYA

Haka suka ƙarasa gidan Hajiya Lawisa kowanne da abin da zuciyarshi ke raɗa masa. Tare suka shiga ciki gidan, wandal A'isha ta yi ta ƙoƙariin ganin ta kaucewa hakan, 

to amma bisa al'ada haka suka sabarwa juna, shiga ko'ina tare idan sun je unguwa. Hakan ya sanya ba su yi wata hira da kowace ke son su zanta a kai ba.

A nan gidan suka sallaci Magariba, bayan sun idar Hajiya Lawisa ta kawo musu funkaso da miyar hanta. Nan suka zaƙe suka kwashi gara, dan haka ciki a cike suka bar gidan.

A hanyar komawarsu gida ba yabo ba fallasa, hirar da suka yi da Hajiya Lawisa wadda da yawa a kan yadda ake tafiyar da kamfanoni ne da kuma yanda shirin gwamnatin tarayya na aika wakilai masu binciken kamfanoni dan ganin ingancinsu. Hakan ya sa suka ci gaba da hirar, kowanne na faɗin ra'ayinshi. Duk da sa'i bayan lokaci A'isha na ganin hasken da wayarshi ke yi alamun kira na shigowa amma ba sauti.

Tare suka fito daga motar, yana riƙe mata tsarabar da ta samo daga gidan Hajiya Lawisa, hakan al'adarshi ce, shi ke riƙe leda komai ƙanƙantarta. Surayya na tsaye amma hankalinsa bai kai gare ta ba, hakan ne ma ya sa bai san tana tsaye ba, amma A'isha ta lura gaba ɗaya muradinshi bai wuci ya ajiye kayan ya isa ga matarsa ba, wataƙila ko dan gudun kar ta yi fushi, wataƙila kuma zumuɗi ne kawai yake mata. Ai kuwa suna shiga ya ajiye mata jakar kayanta da ke hannunsa ya mata sallama ya fice. Kallon da ta bi shi da shi sai kawai ya ba ta dariya da kuma tausayi lokaci guda, namiji  ke nan, in dai wajen nuna zaƙaƙa-ta-fari ne to ba ya shi, zai sa ki ji duk duniya ke kaɗai ce mace da ta isa kallo gare shi. Amma hakan duka na ɗan wani taƙaitaccen lokaci ne, da ya gama wannan ɗokin da zumuɗin zai hango wata.

Sallar isyha'i ta yi kafin ta zauna tana kallo tana cin jiƙaƙƙiyar ayarta, sannan ta ɗauko wayarta ta kunna yanar gizo. Sai a lokacin ta amsa wa Bigi maganar da ya yi mata.

-Da dai za ka girma Bigi irin jikinka da an huta.

Dariya ya aiko mata kasancewar yana kusa, sannan suka yi musayen gaisuwa, ya ce ta gai da Faruƙunta. 

-Yana Abuja.

Ta tura mishi da amsa. 

-Ayya, to Allah ya dawo da shi lafiya. 

-Wai ba ka san Abujar ba?

-Capital territory ko?

A'isha ta ƙyalƙyale da dariya sosai kafin ta tura masa da amsa.

- Ɗakin amarya de😂

-Toh, uwargida fa?

-Lagos, Eko.

-Chai, mata ba kwa ji wallahi.

- A bakinku muka ji ai.

Haka dai suka ci gaba da hirarsu wanda gaba ɗaya a kan rayuwa ne, kafin daga ƙarshe su yi sallama saboda dare. A'isha  ta yi addu'ar bacci ta kwanta, a ranta sam ta manta da batun Faruƙu da ke kwance ɗakin amaryarsa.

***

Rayuwarsu ta ci gaba da tafiya ba yabo ba fallasa, tun ana ƙirga kwanakin Surayya a gidan Faruƙu har aka haura shekara ɗaya. Duk zaman nan gardama ba ta taɓa shiga tsakanin A'isha da ita ba, kowa zaman kansa yake, ba su shiga al'amuran juna ba balle a samu saɓani. Irin zaman 'yan marina da Bahaushe yake cewa.

A duk lokacin da yake gidanta tana ƙoƙarin kyautata masa, duk da minti ukunta ta manta rabon da ta same shi, in ba ƙarya ta yi ba za ta iya cewa a shekara ɗaya ba za ta ce ta samu ya kai sau shida ba, amma kuma ya ta iya? Tunda dai an ce shi aure yaƙin mata ne, ƙarshe dai ko ta kashe ko a kashe ta.

CIWON CIKIN BAREWA Where stories live. Discover now