CCB

87 17 5
                                    

BABI NA GOMA SHA BAKWAI

Sai da ya yi mintuna kusan biyu bai iya amsa mata ba, yana jin idanunta a fuskarsa, ya daure ya mai da hankali a tuƙin da yake yi. Can ya nisa ya kalle ta, har a lokacin kuwa shi take kallo, idanunta kan fuskarshi, tausayinta ya ƙara lulluɓe shi, a ransa yana ji ya san bai kyauta mata ba, amma kuma wani sashen na ce da shi to wa ya janyo?

"Lafiya lau take." Ya samu kansa da faɗa yana mai sauke ajiyar zuciya.

Ganin kamar ba ya son maganar sai kawai hakan ya ba ta dariya, ta girgiza kanta kawai sannan ta kau da kanta daga dubanshi. Ta juya tana kallon hanyar da suke shigewa ta cikin gilashin tagar motar. Can ta numfasa ta fara ba shi labarin tafiyarsu, a nan ya saki jiki suka dinga hira da dariya, a haka har su ka isa gida.

Sai a lokacin ne zuciyar A'isha ta buga, tunanin me za ta tarar a cikin gidanta. “Gidanki ko gidanku?" Wani sashe na zuciyarta ya kwaɓe ta. Sai kawai ta ji ta haɗi wani busasshen yawu. Cikin ƙarfin hali ta sa ƙafa ta fito daga cikin motar. Ko da sa ƙafarta harabar gidan sai gaba ɗaya take ganin kamar ba gidanta ba, dan sauye-sauyen da ta fara iskewa a wajen.

Akwai sabon fenti da aka yi wa gidan, wannan ba ta yi wani mamakin sa ba, hakan na faruwa. Amma wasu furanni da ta gani an jera su sun yi wa wajen ƙawanya, icen dogon yaron da a da shi ne kusan saiwa kaɗai a wajen yanzu duk babu shi, sannan kuma babu tukwanenta da ta yi dashen saiwar alobera da take amfani da shi wajen haɗan man wanke fuskarta.

Kallonsa ta yi cike da mamaki tana mai kallon ɗan kwikwiyon da ta gani a ƙulle a gefe yana ta 'yan tsalle-tsalle, ta samu ta danne tsoron da ke zuciyarta sannan ta ce da shi.

"Ba na son kare fa, ina matuƙar tsoron su." Ta tuna masa kalamanta gareshi tun kafin aurensu da ya taɓa bijiro mata da zancen ajiye karen Turawa.

A shekaru goma sha biyu da su ka yi tare bai taɓa gigin kawowa ba sai yanzu, cikin sati biyu da babu ita a gidan, har ya fara mantawa da so da rashin sonta, da nutsuwa da firgicinta. Ta tuna maganar da ya yi mata a filin jirgi ta batun zamansa adali, sai kawai murmushi na takaici ya suɓuce mata.

Ganin yana kaucewa dubanta ya sa ta wuce shi ta nufi sashinta, nan ma wani turus ta yi, ganin Surayya da yi ta fito tana “oyoyo darling!"

Dukkansu suka ja suka tsaya, ƙarfin hali A'isha ta yi ta ƙirƙiro murmushi ta ce.

"Amaryarmu barka da gida, fatan mun same ku lafiya?" Ta ce tana ɗan taɓo ta. Ita kuma ba ta ɓata lokacin janye jikinta ba tana mai watsa mata kallon da sam A'isha ba ta yi mamakinsa ba, nan ta ja ta yi danga har Faruƙu ya iso.

"Darling ya haka, ba ka mata bayani ba ne?" Surayya ta ce cikin shagwaɓa tana mai kwantowa jikinshi. Ga mamakin A'isha, maimakon ya ture ta yanda ya kan yi mata a duk lokacin da ta nemi raɓo shi a bazata sai kawai taya  ya tarota yana mata shafar mage.

Baki ta saki tana kallon su, kamar wata wadda ta fara kallon majigi karo na farko a rayuwarta. Yadda yake shafa Surayya da yadda ita ta kwanta a jikinsa, kai ka ce abin da yai A'isha ma bai tsiro a wajen ba. A'isha ta san ana faɗin asiri na sa namiji ya sauya, amma za ta iya rantsuwa babu aikin asiri a cikin abin da idanunta suke gane mata, zallar rashin ta-ido ce da kuma son muzguna mata.

Ganin abin na su ba mai ƙarewa ba ne ya sa ta ɗan yi gyaran murya. Sai a lokacin ya juyo ya kalle ta, ita kuwa Surayya har a lokacin fuskarta na kwance jikin ƙirjinsa.

"A'isha, Surayya ta fi buƙatar nan shi ne aka yi musaya, ke kika koma can."  Ya ce yana mai nuna ginin da a da take tunanin shi ne na amarya.

Zuciya na ƙuna ta kalle shi ta kalli ginin, duk da sam bai taɓa ambata mata cewa a ciki zai ajiye Surayya ba, hasashenta ne kawai ya ba ta hakan.

CIWON CIKIN BAREWA Where stories live. Discover now