Kashi Na Biyar
Sosai Faruk ya ba ta lokaci, so yake ya ga ko za ta faɗa masa meke damun ta, dan ya leƙa duk wani lungu da saƙo na alaƙarsu bai ga inda ya kuskure mata ba. Hakan bai hana shi zaman gida kamar yadda ya saba ba, za su fita tare zuwa ziyaran iyayensu a duk Juma'a kamar yadda suka saba, in suna cikin mutane ta yi ta nan-nan da shi da sun keɓe za ta murtuke fuska kamar ta hango ɗan saƙon mutuwarta, ko wata wadda aka jefa cikin kurkuku.
Akwai lokacin da ya taho da tarin ƙishin ruwa, ya dinga jan ta da lallaɓa ta dan neman sulhu, amma ta yi ƙemadagas da shi, a ƙarshe ma sai albarkar tsaki ya samu, hakan sosai ya ƙona masa rai, dan haka shi ma ya ɗaura aniyar yin biris da ita.
Tun suna ƙirga kwanaki har ya koma watanni. A nan har azumi ya gabato, bai faɗa mata ya biya Umara ba, jirginsu ya tashi ranar sha bakwai ga watan. Duk shirin da yake A'isha ba ta kula ba, ta dai san akwai ranar da ta ga fasfo ɗinsu kan gado ya ajiye, ta dinga surfa masifa tana faɗi.
"Ka adana abu a fito da shi sai ka ce a kan mutum yake, sannan in ba a gani ba a ishe ka da tambaya!"
Ganin zancen ya ƙi ci ya ƙi cinyewa sai maimaita magana guda take ya sa ya miƙe daga gadon da yake kishingiɗe ya dauki fasfo dinsa, ba tare da ya ce da ita ci-kanki ba ya fice.
Ba ta kawo komai ba sai da ta ga saƙon karta kwanan da ya aiko mata, "mun wuce zuwa Umara a yafe mana."
Ji ta yi kamar ta ɗaura hannu a kai ta kurma ihu, amma wa za ta yi wa? Gani kawai take babu babban azzalumi sama da Faruƙu, dan ta rasa dalilinsa na ɗauke mata.
Ta shiga haɗa kata zuciyarta na ci gaba da mata suya, duk wani abin buƙatarta sai da ta ɗauka, sannan ta kulle gidan ta nufi gidansu. Ta yi mamaki da ta ji sun san da zuwanta, amma da ƙaninta Ibrahim ya shigo ya tuntsere da dariya sai ta sha jinin jikinta, ta san kusancin da ke tsakaninsu bai sa ta taɓa fadi masa rayuwar da su ke ba.
"Da ma ya ce kila ba za ki iya zaman kaɗaici ba za ki zo, amma kina cika bakin za ki iya, ina jarumtar take!" Ya faɗa yana ci gaba da mata dariya.
Ba ta kula shi ba, ta shige ɗakinsu na 'yammatanci zuciyarta na hawaye, watau yana sane da abin da yake yi har ma yana tunanin za ta tafi, to da ma kora da hali yake mata ko me?
Rashin amsar tambayar da ke mata yawo ne ya sanya ta tashi wajen gabatar da alwala zuciyarta cike da mamakin Faruƙu, ina son da yake tutiyar yana mata? Da ma ita ma za ta ga wani sashi na mijinta da ta kan ji mata na faɗi? Haushi da baƙin ciki kawai ya sanya ta jin jiri, ta yi zaman dirshan a tsakar tayel ɗin ɗakin tana ambaton Allah, sam ba ta jin sanyin tayel ɗin a jikinta.
***
Kwanci tashi asarar mai rai, duk kwanan duniya Faruƙu sai ya kira, ita kuma sai ta ƙi ɗauka, haka zai aika mata saƙo ta manhajar WhatsApp yana tambayar lafiyarta. Rashin halin ko-in-kula da take da saƙonninsa bai sa ya daina ba, ko da salla ta matso kuwa ya aika mata na cefanen salla. Kayan salla kuwa sai kawai gani ta yi telanta ya kawo mata duk da ba ta san ya siya ba balle ta ce ga wanda ta ke so. Maimakon hakan ya burge ta sai ma ƙara ɓata mata rai da ya yi.
A bakin Ibrahim ta ji dawowarsa, saboda gyaran gidan da ya sa shi ya yi musu, yana faɗa mata kuwa a fusace ta ce, "ni fa ban zo dan na koma ba, na dawo ke nan!"
Maganar ta girgiza Ibrahim har sai da ya nemi bakin gado ya zauna.
"Mene ne ke faruwa haka A'isha?" Ya tambaye ta cike da damuwa.
Aikuwa kamar ya burge bakin fanfo haka ta dinga zuba, ba ta bar komai ba shi kuma ya saurare ta yana mai fahimtar dalilinta.
"Kin tabbatar da ba abin da ke distracting ɗinsa?"