KASHI NA ASHIRIN DA BIYAR
Ba za ta ce ga yanda ƙafafunta su ka ƙarasar da ita cikin gidan ba, tun da ta ga maza manya da ƙanana fuska a turɓune a harabar gidan su gabanta ke mata lugude ga kuma ayar "kullu man alaiha fan" da ke amsa kuwa a kunenta.
Tana shiga ta iske mata a tsaitsaye, ganin uwargidan babanta na kuka ya sanya ta sakin fitsarin da ta ke ƙoƙarin riƙewa, ta san dai in baba ne ba yanda za ayi a kawo shi gidan bayan ga gidan uwargida Wanda ke haɗe da gidan gandunsu.
Dafe bango ta yi ganin tana shirin faɗi, nan ta ga an taro ta.
"Ba ta ɗago ta kalla ba don dai tabbas hannun da ya riƙo ta mutum ɗaya ta mallaki irinsa.
" ka da ki masa kuka mamana, insha Allah ya dace "
Muryarta ta ji, hakan ya sanya ta juyowa da sauri.
" Maa-maamaa"ta ce tana fadawa jikinta cikin sadakar da ta rasa mahaifinta.
Fitowar Baba daga dakin sa yana sharfe gumi ne ya sanya ta tunanin ko dai Sagir ne, tana so ta tambaya amma wa za ta tambaya ne ta rasa.
Ƙullutun da ya tsaya mata a ƙirji na ƙara girma, idanunta na ganin dishi-dishi ya sanya ta yin zaman ƴan bori a wajen, hakan ya jawo hankalin matan wajen gareta, ba su ɓata lokaci ba kuwa sai zagaye ta su ka yi masu firfita na yi masu bata hakuri na yi, duk ba shi ta ke son ji ba, kamar kuwa makotansu sun karanta zuciyarta su ka fara
"Allah sarki, dama ina ta tunanin ta, kun san shaƙuwarsu na daban ne, Allah ya jikan Ibrahim"
Tiryan Tiryan kalamansu suka shiga kunnen ta, ƙwaƙwalwarta ta fassara mata zancen amma ban da hakan ba ta gane komi ba.
"Aisha ba kuka yake bukata ba, don Allah" ta ji kalaman anty Fatima, babbar yayar su gaba ɗaya.
"Wane? Wanene? Ku faɗa min ba wanda ban gani ba toh wanene ya rasu" ta ce cike da ruɗu , ji take ma ƙarya ne babu wanda ya rasu.
Maimakon Antyn ta amsa mata, hannunta ta rike su ka shiga ɗakin baba, Hadiza ce ta gani zaune gaban gawa a shimfide kan tabarma. Sai kuma wasu samari da ta sansu amma Sam ba za ta iya tuna alakarsu da gidan ba, zaune su ke suna karanta suratul mulk. Karasawa su ka yi, a kwance yake nannade cikin farin ƙyalle, fuskarsa ce kawai a bayyane.
Sake juyawa ta yi don ta ga wainda ke zaune a dakin, sai a lokacin ta ga Abdulgaffar cikin masu karatun.
Takawa ta yi har inda Abdulgaffar yake ta ɗan taɓa ya waigo, idanun sa jawur alamun ya na kan kuka
"Abdul ina Ibrahim?"
So ta ke ya ƙaryata abin da idanunta ke gane mata, ya ce mata ba Ibrahim dinta bane a kwance.
Kamota anty Fatima ta yi. Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun kawai ta ke fadi har Aisha ta fara maimaitawa, cikin ikon Allah sai wani irin natsuwa ya shige ta. A haka har ta ƙarasa kusa da gawar ta gana da shi ta masa addu'a duk da zuciyarta na raɗa mata dogon suma ne zai tashi kafin Ƙarfe goman da aka ce za a yi Janazarsa.
Daren ya fi ko wanne sauri garesu, gari na wayewa kuma Ƙarfe goman ta buga, aka fara hadahadar fita da shi don sallatarsa
"nawa zan ba ku, ku bar min shi in ta kallonsa" kawai A'isha ke faɗi sai dai duk wanda ta tukara tuna mata addu'ar da ya kamata ta masa ake watau
"Allahum-maghfir lahu warhamhu, wa 'aafihi, wa'fu 'anhu, wa 'akrim nuzulahu, wa wassi' mudkhalahu, waghsilhu bilmaa'i wath-thalji wa-lbaradi, wa naqqihi minal-khataayaa kamaa naqqaytath-thawbal-'abyadha minad-danas"
Haka ta dan samu tana yi cikin hardewa da rashin natsuwa, jan kafa ta yi har filin da su ka sallace shi aka tafi da shi gidansa na gaskiya.
KASHI NA ASHIRIN DA SHIDA