KASHI NA SHA BIYU
Bai katse shi ba har sai da ya kai aya. Amma yanayin mamaki da al'ajabi duk ya cika fuskarshi. Mamakin A'isha ne fal a cikinsa, ita da ya ke wa kallon mai hankali ashe dai sai a hankali.
"Ni ai imani ma ya cika ni, har ta iya kallon idonka ta faɗi haka." Alhaji Salmanu ya faɗa cike da nuna mamaki.
"Taya ni figa kai ma Alhaji, ni f agaba ɗaya ma ta sire min, ka san shekarun baya ba ta iya fitowa ba amma duk wani cin kashi na kwasa, ko dan ta ga ina son ta ne."
"A to, ka faɗi ai, mace sai dai ta ci ta zaga, an ce ka ƙara aure kana ƙi, in ba kai da gaske ba ka kusan jin ka a filin Jakar Magori" yace yana dariya mai cike da shaƙiyanci.
"Aure kuma Alhaji!" ya ce cikin wani irin yanayi mai cike da damuwa da nuna rashin tabbas.
"To ko dai da gaske raggon ne?" Alhaji ya ce yana kallon sa. So yake ya tunzura shi ya amince da zancen auren, shirun da Faruk yayi kuwa ya tabbatar masa da an ɗauki hanyar hakan.
Haka ya ci gaba da ingiza shi har dai Faruƙu ya nuna tsoronsa a zaɓin matar aure.
"To in ban da abinka Faruƙu, ga Surayya nan. Ka dai san irin son da take maka, me zai hana ka zo kawai a yi tuwona maina."
Suka yi shiru na wani ɗan lokaci, kowa da abin da yake saƙawa. Shi Faruƙu hango yiwuwar auren yake da kuma yadda mutane za su ɗauka kasancewar Surayya kamar ƙanwa take a wajenshi, 'yar gidan Goggonsa ce.
"Ka ga ko ba komi Alhaji zai yi matuƙar farin cikin zumuncin nan da za ka assasa." Alhaji salmanu ya katse shirun da suka yi.
"Alhaji in da gaske laifin nawa ne fa? Kar na kasa ta je ta yaɗa ni a dangi."
" 'Yar'uwarka ba za ta taɓa tona maka asiri ba, ita dai rasa kunyar can ka yi fatan ba ta mai da ka kanun labarai ba. Besides, sam ba haka ba ne, kawai jaraba ce irin ta 'ya'yan yau, da kallace-kallacen banza da kuma shan kayayyakin da ke tunzura sha'awarsu, amma mene ne a ciki da ba za ka iya ba!"
Alhaji Salmanu ya gama tsara shi tsaf, hakan ya sa shi jin sanyi a ransa. Suka ci gaba da tattauna zancen, Alhaji Salmanu na ƙawata masa hikimar da ke cikin hakan, da nuna masa hakan ne kawai zai ƙaryata A'isha a duk inda ta kai zancenshi.
Lokacin da Faruƙu ya koma gida A'isha ta daɗe da kwanciya bacci, ba ta ji ko ƙarar motarshi ba, ba kuma ta ji alamun shigowarshi ɗakinsu ba.
KASHI NA GOMA SHA UKU
Gaba ɗaya mamakin A'isha ya ƙare ga yadda ya tattara ta ya watsar, tun abin na mata ciwo har ya koma ba ta dariya kafin ya sauya zuwa ga mamaki. Zamansu ya zama kamar gidan haya, tun tana ƙirga kwanaki tare da dakon zuwansa gare ta har ta daina ƙirgawa. A hankali sai ta lura da zamanshi a waje bayan Isha'i a wasu kwanaki dan har ya kan kai ƙarfe goma a waje, sannan idan ya dawo zai ɗauki waya yana latsawa fuskarsa kamar gonar auduga, saboda annurin da ya kan kasance a duk lokacin da ya ke riƙe da wayar.
Ganin abin ba ƙararre ba ne ya sa ta fara zargin sa, duk da a giginta ba ta taɓa hasaso aure yake nema ba, ta fi kallon abin a ya samu wata da ya ke rage damuwarsa da ita. Kamar yadda mafi yawan maza suke a rayuwa, dole suna kula wata macen da take ɗebe kewarsu a hira. Kamar yadda Hajiya Lawisa ta taɓa cewa da ita, "namiji ba ya taɓa iya rayuwa da mace guda ɗaya."
Tunanin haka da ta yi ya sanya ta shirya duba wayarshi. Ba ta sha wuya ba haƙarta ta cim ma ruwa, ya shiga wanka ya bar wayar tana caji. Kai tsaye WhatsApp dinsa ta fara shiga, kuma saƙon farko ya ba ta amsar tambayarta.
"Nur!" Ta faɗi a hankali kamar yadda ta ga sunan a rubuce. Murmushi kawai ta yi, tunawa da ta yi ana wa wasu alkunya da hakan ba wai shi ya laƙa mata hakan ba, ganin ita ma in ya tafi da ita a shauƙin soyayya yakan ce da ita "Ayish".