BABI NA KARSHE

96 19 6
                                    

Kashi Na Tara

***

Tafin da A'isha ta ji ne ya dawo da ita daga duniyar tunani da take ta faman saƙawa. Sam ba ta ji buɗewar ƙofar bayi ba, balle har a ce ta ji tsayuwar Faruƙu a kanta.

"Tunanin me kike yi ne?" Ya tamabye ta cike da kulawa, a zuciyarta ji take ina ma a ce kulawarsa gare ta a kan duk wani abu da ya shafe su ne.

Hmmm! ta ɗan yi ajiyar numfashi kafin ta ba shi amsa. "Ba komi, rayuwar aurenmu ce kawai nake tunawa." Ta furta hakan tana mai langwaɓe kai cikin tausayin kai.

"Aisha kar ki damu, haihuwan nan in sha Allah za mu yi har mu cika gida." Ya ce yana mai rungumo ta.

"Ta yaya za mu haihu?" Ta tambaye shi byana da ta zame jikinta daga nashi sannan ta kafe shi da idanunta. "A ruwa a ke kurɓa ne hala?"

Ya yi 'yar ƙwafa kafin ya ce da ita, "tarawa duk dare ba shi ke ba da haihuwa ba, ba ki ganin yan ciranin nan ciki kawai suke zuwa su ɗura ma matansu su koma." Ya kai hannu ya riƙo hannunta ya matsa su. Ta ƙara zame su ba tare da ta bari ta kalle shi ba kafin ta ce.

"In ba a yi dan haihuwa ba, halittarmu fa? Ka taɓa tunanin in ni mai tarin buƙata ce ko kuwa? Ka taɓa tuna  cewa shi ne kawai abin da ba a isa a ba ni a gidanmu ba shi yasa aka ba ka ni? Har sai yaushe? Har sai yaushe ne Faruƙu!"

Idanunta suka ciko da ƙwalla, ƙwallar takaici da tsananin ɓacin rai, ƙwallar da ba ta da mai share mata. Ta yi saurin saukar da kanta ƙas, ba za ta yarda ya ga rauninta ba haka.

"Ita mace har sha'awa gare ta na karan kanta! Ai halittarta na tafiya ne da sha'awar mijinta, in ma za ki cire ma kanki jarabar nan ki cire, ba abinci  ba ne da za a ci a ƙara, sannan ba shi cikin wajiban rayuwa. Na dai faɗa miki ki yaƙi zuciyarki daga banzan jarabar da kika dasa mata." Ya ce yana mai ɗaga murya. Ya ja tsaki tare da kyaɓe baki kamar wanda ya ga kashi, sannan ya sa ƙafa ya fice ya bar mata ɗakin.

Shiru ta yi a zaune, gaba kura baya sayaki, dan ko giyar wake ta sha ba za ta nemi saki a dalilin hakan ba, ko dan Allah ya isa da iyayenta suka ɗaura a kan hakan. Haka ta yi zaune kamar wadda ruwa ya cinye, ta ƙulla wannan ta saƙa wancan. Wata zuciyar ta ce to ko azumi za ta ɗaura ɗamara, ta yi ta yi ba kama ƙafar yawo. Amma kuma sai ta tuna sam ita fa ba mai juriyar azumi ba ce tun usulinta, idan ta ce za ta yi haka ƙarshe ta ƙara ja wa kanta wata lalurar, goma da ashirin!  Abin zai mata yawa, wai shege da hauka. To ko akwai wata ƙwayar magani ne da ake sha ta kashe wannan wutar buƙatar? Wani tunanin ya ƙara faɗo mata. Ta yi tsam tana tunani ko akwai ɗin, ko ta taɓa ji ko da a hira ne ana batu irin hakan. Amma tsayin mintuna ba wani abu da zuciyarta ta tuna mata. Ƙarshe ta faɗi sharaf da baya kan gadon da take zaune gefensa. A hankali ta ba wa idanunta damar fara zubar da hawayen da take ta aikin riritawa. Ciwon cikin barewa, wani ɓoyayyen sauti ya yi mata raɗa a kunnuwan zuciyarta. Hawayen da suke zuba kan fuskarta suka ci gaba da kwaranya, ba ta ko da mu da share su ba.

Kashi Na Goma

Safiyar Litinin ta zo mata wata iri, dan ko jiran ta Faruƙu bai yi ba kawai ya ja motar sa ya yi gaba. Hakan bai dame ta ba, saboda tun daren jiya da suka yi musayar magana ta rasa ƙawa zucinta, jin zuciyarta take kamar wani holoƙo, wani waje da aka rarake shi, ba komai a ciki face amsar amon zuciyarta da take bugawa fat, fat, fat. Bayan ta gama shiryawa ta fito bakin titi ta tare Adaidaita Sahu, wanda silar hakan da tsaye-tsaye da cunkoso ya sanya har ta isa wajen aiki a makare.

Gaba ɗaya ji ta yi ina ma dai ba ta fito aikin ba, dan duk wanda ya gan ta sai ya mata sannu da jiki kasancewar babu abin da suke gani a gare ta face irin fuskar da ta yi fama da jinya, irin rashin lafiyar nan da wuni ɗaya tak kan zaftare kumarin mutum.

CIWON CIKIN BAREWA حيث تعيش القصص. اكتشف الآن