KASHI NA SHA HUDU
Gaba ɗaya haka hutun ƙarshen makon ya zo wa A'isha, ba wani armashi, ranar Litinin ma haka ta shirya dan zuwa aiki, da safiyar ranar ta dafa musu sinasir da farfesun busasshen kifi.
Tare suka ci abincin, duk da ba uhm ba uhm-uhm a tsakaninsu, kamar wasu bebaye. Shi wayarsa kawai ya ke dannawa, fuskarsa sai ƙyalli take, yana yi yana murmushi sa'i bayan lokaci, abincin da ke gabansa kuma yana ci ne kawai bisa sabo ba dan hankalinsa na kai ba. A'isha tana zaune gabansa amma ita ma ba abincin da take ci ba ne a ranta, a ranta ta fi zargin anya ma ya san irin kalar abincin da ta ajiye a gabansa? Zuciyarta kawai ta shigi karanto mata irin hirar da suke tattaunawa tsakaninsu ta wayar salularsu, wani tuƙuƙin ɓacin rai ya cike mata cikinta, ƙarshe da ta ji ba za ta iya jurewa ba sai kawai ta ture abincin da ke gabanta ta miƙe.
Ya ɗago kai ya kalle ta kafin ya mai da hankali ya ci gaba da cin abincinsa, hannaynsa na ci gaba da shafa wayarsa. Yana ƙoƙarin tambayar ta har ta ƙoshi ne saƙon Surayya da ya shigo salularsa ya katse masa tunanin hakan. Ya karanta saƙon cikin zuciyarsa.
"Yanzu ba za ka faɗi mata ba wai?"
Nan ya tuna da maganar da suka yi. Sun yi magana shi da Surayya a yammacin jiya da ya je gidansu taɗi, bikinsu saura sati uku kacal, amma matarsa ba ta sani ba.
"Ba wai ba zan faɗa mata ba ne Nur, kawai de yanda zan mata maganar ne na rasa."
Ya mayar mata da amsa.
Tun bayan maganarsu da Alhaji Salmanu bai ƙyale shi ba har sai da ya tabbatar da sun iske magabatan Surayya da batun neman aurenta. Baffanta ya ce tun da abin na gida ne kuma Faruƙu ba saurayi ba ne ba sai an ɓata lokaci ba, nan take suka tsai da magana aka sanya aure wata biyu.
Sai da ya ba da komai ya fara gabatar da kansa ga Surayya a matsayin wanda ya nemi aurenta kuma an ba shi.
Surayya kuwa da ma abin nema ne ya samu, da ma tsohon tabo ne take kwance da shi kuma aka yi mata faminsa. Sosai ta kanainaye shi da salo-salon soyayyarta, har bai san lokacin da ya tsunduma ba, ga shi har ana ƙirga saura sati uku bai iya faɗa wa A'isha ba.
Wayarsa ta yi gunji, saƙon Surayya ya shigo.
"Har sai yaushe?"
"Yanzu in sha Allah."
Ya tura mata da amsa. A daidai lokacin A'isha ta fito sanye da hijabi ruwan madara da ta ɗaura a kan atamfarta.
"Har kin fito ne? Ki jira na sauke ki." Ya ce mata yana ƙoƙarin miƙewa.
Ba ta musa ba, ta jira ya ƙarasa shiri cikin shigar kaftani.
Tafe suke, motar shiru kamar babu mutane a ciki har suka iso ma'aikatarsu. Kafin ta fita ya juyo ya ce da ita.
"A'isha mun kusa samun ƙaruwa fa."
Ya ce yana mai kau da idanunsa ba tare da ya bari sun haɗa idanu ba.
"Ma sha Allah! Mota za mu sake ko mun ma sake ɗin?" Ta ce tana mai kafe shi da idanunta, yanayin fuskarta mai wuyar fassarawa.
"No." Ya ba ta amsa. "Duk ba nan ba, matar mutum ce, aure zan ƙara."
A'isha ta yi shiru ba ta tanka masa ba, ba kuma ta ɗauke idanunta daga kansa ba. Kawai ta kafe shi da idanu, a zuciyarta akwai tuƙuƙi da takaici, da yanayi da ba ta san ya za ta fassara shi ba. Ta sani zai ƙara aure, a ranta ma har tana ji ta yi masalaha da hakan da zuciyarta. Amma sam ba ta lissafa yana da zarrar da zai iya buɗa baki ya faɗa mata da kansa ba. Tana so ta buɗe bakinta ta ce da shi wani abu, ba ta san me za ta ce ba, amma dai ko ma mene ta ji ta furta ta san za ta samu sauƙin abin da take ji. Amma harshenta kamar an sa kwaɗo an kulle shi. Komai ya yi mata nauyi, komai ya yi mata duhu, komai. Kamar ƙabari, kamar mutuwa, kamar....