Chapter 1 (the beginning of my destiny)

110 6 0
                                    

*RA'AYIN ZUCI...*
_(The opinion of the heart ♥ )_

بسم الله الرحمن الرحيم

*Dedication to my late mother  Maryam Abdullahi Zango who died 15years ago. Ma'anarta a rayuwata yanada tarin yawan da baki bai isa ya kwatanta girmansa ba, she lived with me and my sisters until her death in 2008. Ubangiji ya jiƙansu da rahama tareda sauran musulmi baki ɗaya.*

*warning ⚠  this is my book. the copyright is mine alone ni kaɗai nake da haƙƙin mallakar abina. Pleaseb don't change it for me in any way without my permission, especially youtubers wllhi this time za'aga fishina idan akayi hakan, idan...👂yaji....*

 chapter :1
#the beginning of my Destiny#
Juyawar da kaina keyi yasa na fara ƙoƙarin Jan ƙafafuna waƴanda ke barazanar sagewa a lokacin dana tsinkayi furucin Yusuf Attahiru A tsakiyar kaina. firgici gamida tsoro Mai tsanani ne sukai wa gaɓoɓina dirar mikiya, cikin gajeran lokaci naji Zuciyata tana ƙoƙarin tsinkewa.
Da ƙyar nake iya jan numfashi ta tsakanin ƙofofin hancin da ubangiji ya wadata halittar jikina dashi, amma sai naji abin ya faskara, cikin ƙarfin halin da yay min saura na fara ƙoƙari gaiyato jarumtar da tai min ƙaura tun tsaiwata a bakin ƙofar. Nadama gamida tarin dana sani ne suka dabaibayeni, cikin gajeran lokaci suka kashe tasirin duk wata jijiyar jini dake kai saƙo cikin curin ƙwaƙwalwar dake ɓoye a tsakanim ƙoƙon kaina.

"ya ilahi"

Na furta a cikin wani gajiyayyen sauti wanda yay dai-dai da saukowar ruwan hawayen dake maƙale a tsakiyar idanuna, a haka nabar Asibitin ina kukan zuci wanda nakeji a jikina cewar banida ranar dainawa. "mai yasa na gurɓata rayuwata da wannan ƙazantar a shekarun daya kamata ace naci ribar rayuwata?" wani ɓangare na zuciyata ya jefa min wannan tambayar wadda naji saukarta a cikin ƙirjina tamkar dirar harshashi.
Ƙwallar dake kwaranya a saman kuncina na saka hannu na shafe, ina jin yanda zuciyar dake ɓoye a tsakanin ƙirjina ta dunƙule a guri guda tamkar ubangiji bai ƙaddara mata motsawa ba,"Ashe dama haka sakamakon halacci kan rikiɗe ya koma ƙiyayya?" na firta hakan a tsakanin busassun laɓɓana, ina jin ciwo mai matiƙar zafi da raɗaɗi na ƙara yin yaɗo a cikin tsokar jikina, jin yanayin nake tamkar almara don ban taɓa ƙaddarawa kaina Cewa ra'ayin zuciyar mutun kan tilasta shi yaƙi yin halacci ga abokin gaminsa ba, sai yau da jifan dutsen Yusuf Attahiru ya daki kunnuwa na. Nayi zaton zai sauya a ya tayani karɓar ƙaddarar data sameni, wadda ke ƙoƙarin dai-daita da tsayin kafaɗuna.

A she sam ba haka lamarin zai kasance kamar yanda na jima ina fatan kasancewarsa ba. Ashe nayi kuskure da na yarda dashi a lokacin da bai kamata na miƙa masa ƴarda ta ba. Haƙiƙa wani dana sanin baya riskar mutum a lokacin da ya dace, har sai wankin Hula ya kai ka ga dare.

To a gareni ma hakane ya kasance lokacin da tsumin gyaɗa ya juye ya zame mini Bommi me tsananin wari da hamami, wanda da mayen warinsa ya fara walagigi da rayuwata tamkar juyin katantanwa!
Shikenan nayi bankwana da farin cikin rayuwata wanda ya zama silar lalacewar komai tun daga mafari. Fashewa nayi da kuka mai matiƙar zafi hannuna dafe da da ƙirjina, yayinda kunnuwana sukaci gaba da dawomin da kalaman da Yusuf ke firtawa akan Aisha Sulaiman ga abokinsa Doctor Umar. ina jin yanda ƙunci da baƙin ciki ke huda duk wata kafar dake kai saƙon da ubangiji ya halitta a tsakanin zuciya da gangar jiki. Lumshe idanuna nayi waƴanda suka jiƙe da ruwan hawaye, cikin sarewa na fita daga cikin Asibitin gabaɗaya ina bin miƙaƙƙen titin daya mamaye ilahirin gurin da fadinsa.

A wannan lokacin ruwan hawayen dake kwaranya a fuskata yayi ƙarancin da babu wadatar da zai tsawaita zuba, na jima a tsaye sannan na saka hannu na tare ɗan-adaidaita sahun dake shirin giftani.
A sagalce nake ɗaga sawayena na isa gareshi na ce,"Hayin ɗan-mani zaka kaini."

RA'AYIN ZUCI... THE OPINION OF THE HEART Where stories live. Discover now