Episode 5

14 3 0
                                    

*RA'AYIN ZUCI...*

CHAPTER: 5
#

The unexpected response#


Ina kwance ban motsa ba har ya gama bude qofar dakin ya shigo, jikina a mace na dauke ganina daga barin kallonsa,ya jima a tsaye sannan ya tako a hankali ya fara qoqarin rage kayan dake jikinsa.

Ganin haka yasa na miqe a hankali na nufi qofar fita daga dakin cikin.

"Bilkisu!" Ya kirani cikin sanyida taushin harshe

Tsayawa nayi chak na kasa motsi jin yanda ya ambaci sunana kai tsaye. ban juyo ba sai da na tabbatar da na kori mamakin da ya wanzu akan fuskata sannan, Murmushin takaici nayi sannan na ce,"na'am!"

Tsareni yay da idanu kimanin gushewar wasu mintuna sannan ya ce,"wannan sabuwar dabi'a da kika tsiro da ita banajin zata kawo maslaha a tsakanin mu, idan kinada matsala dani zefi kyau ki fuskanceni a madadin ki tsaya kina boye bacin ranki ta hanyar gujemin."

Wani abune ya tasomin daga cikina zuwa wuyana, nan take naji wani tuquqin baqin ciki da bacin rai suna mamayar zuciya da gangar jikina. Murmushin takaici na qara wadata fuskata dashi a lokacin dana tuna haurawar da mukai dashi a daran jiya. don haka na danne bacin raina cikin qarfin hali dana zuciya na nitsa kwayar idanuna cikin tasa na ce,"hadin Aurenku da Aisha da fari na karbeshi a matsayin umarnin da Hajiya ta baka. amma daga baya sena fahimci akwai kyakkyawar alaqa a tsakaninku, yanayin dana ganku a ciki ya gama fallasa min gaskiyar abinda ke boye a bayan zukatanku." nayi maganar idanuna suna cikowa da ruwan hawaye

Numfasawa nayi tareda kai hannu na share qwallar data fara zubowa ta tsakanin fatar idanuna, sannan naci gba da cewa,"abinda na gani kwance a tsakiyar idanunka lokacin da ka fito daga mota yasa na fahimci wasa kake da intelligence dina, sannan kayi min qaryar cewa ba zaka hada son da kake min da wata diya mace a duniya ba. Hmmm amma sai gashi tun bamuje ko ina a zamantakewa ba naga irin tausayawar da kake min kwance cikin idanunka a lokacin da kake kallon tsakiyar idanun Aisha Sulaiman!

Yusuf, tell me how can I share the same shade with you?" nayi maganar ina sakin kuka dana jima ina dannewa a qasan ruhina

Jikinsa ne yay sanyi lokaci guda yaji nadamar abinda ya aikata tana mamayarsa, cikin rashin guzari ya tako gabana ya tsaya akan sawayensa, cikin wani irin sanyin jiki wanda ban taba ruskarsa a ciki ba ya kai hannayensa ya riqe kafaduna. in a weak voice ya ce,"kada ki Dora zuciyarki akan Zargi Bilkisu, wllh abinda nakeji gameda ke a zuciyata babu wata diya mace data isa ta ruski matsayinki a raina har gaban abadah." yayi maganar yan qoqarin kamo hannuna ya Dora a saitin zuciyarsa, wadda ke bugawa daki bayan daki

Janye hannuna nayi da sauri har lokacin ban dena zubar da hawaye ba na ce,"wllh idan na rantse bazanyi kaffara ba cewa irin son da kakemin wllh irinsa na gani kwance a tsakiyar idanunka lokacin da kake kallonta. don Allah Yusuf kada kayi amfani da raunina ka cutar da yarda ta akanka. Nasan kana da dalilin qara aure tunda ban baka abinda kafi buqata a rayuwarka ba, idan har zan maka adalci to bai kamata in hanaka qarin aure sabida son zuciyata ba."

Bai ce min komai ba ya janyoni jikinsa ya rungumeni qam yana shafa fatar bayana alamar rarrashi, a wannan lokacin kuka nake sosai ina jin zafin kishinsa yana qara huda min zuciya.

Ranqwafawa yayi tareda Dora bakinsa a saitin kunnena ya ce,"kin min abubuwa dayawa Bilkisu, you are a darling not only for me, ke abar so ce ga kowa sabida tarin alkhairanki." Ya fadi hakan yana qara Matsoni cikin jikinsa. A haka wannan ranar ta gushe yusuf yana kasheni da dadin bakinsa irin nasu na maza.

RA'AYIN ZUCI... THE OPINION OF THE HEART Where stories live. Discover now